Sa Hannun Mahukunta

Game da ƙananan ƙungiyoyi da ke tsara shirin P/CVE, taimako da sa hannun manyan mahukunta a matakin ƙaramar hukuma (ciki har da mambobin cikin al'umma da shuwagabannin al'umma) abu ne mai muhimmanci.  Bugu da ƙari, ƙananan ƙungiyoyi na iya faɗaɗa manufofinsu na P/CVE ta hanyar samun tallafi da sa hannun masu faɗa a ji da gwamnatoci domin yaƙar tsattsauran ra'ayin rikici sannan tare da bin hanyar rataya nauyi a kan gwamnati. Shirinku na iya aiki tare da masu ruwa da tsaki a matakin ƙaramar hukuma ta hanyar "haɗakar ƙirƙirar" ayyukan shiri tare, da gudanar da zaurukan tsokaci da koyo, da ƙarfafa sanya hannun jari (bayyananne ko ta hanyar ƙarfafawa) tare da masu ruwa da tsaki a matakin ƙaramar hukuma.

Yayin da kuke aiki tare da mahukunta a lokacin aiwatar da shirinku, ku duba Sashen Haɗi game da Aiki Tare da Mahukunta.

Title
Yaya tsarin damawa da mahukunta daban-daban yake?

Dole ne a tsara al'amarin aiki tare da mahukunta dangane da kowane shiri. Game da shirye-shiryen P/CVE, sauye-sauyen da ake samu a matakin ƙaramar hukuma da muhalli na taka muhimmiyar rawa wajen gyara tsarin shirin, da kuma shuwagabanni a matakin ƙramar hukumomi da za a nemi haɗin kansu. Tambayoyin jagoranci da ke ƙasa da samfurori da aka samar za su taimaka muku wajen samar da tsari mai nagarta na neman haɗin kan mahukunta.  

Wa? Waɗanne mahukunta ne ya fi dacewa a ba da ƙarfi kansu sannan a nemi haɗin kansu a yayin ganowa da tantance mahukunta na farko? Shin an ci karo da waɗansu rukunonin mutane da ke fuskantar wariya a cikin mahukuntan? 
ME YA SA? Mene ne muradai da manufofin kowane mahukunci? Me ya ja ra'ayin mahukunta domin yin aiki tare da ku? Me ya sa ake aiki tare da mahukunta?
Me? Mene ne mizanin damawa da kowane mai faɗa a ji da ake yi a kowace gaɓa a matakan aiwatar da shirin? Waɗanne abubuwa ne ya dace a samu yarjejeniya wajen yanke hukunci game da su?
TA YAYA? Waɗanne dabaru za a yi amfani da su domin samun haɗin kan kowane mahukunci? Waɗanne matakai za a bi domin tabbatar da cewa an yi aiki tare da rukunonin al'umma da ke fuskantar wariya?
YAUSHE? Wane tsawon lokaci za a ɗauka sannan yaya adadin yawan lokutan da za a yi aiki tare da mahukunta?
NAUYE-NAUYEN DA SUKA RATAYA A KAI? Wace rawa wakilan mahukunta za su taka? Wane ne zai ɗauki nauyin aiki tare da mahukunta?
KAYAN AIKI? Nawa za a kashe dangane da aiki tare da mahukunta sannan da wane kasafin kuɗi za a yi amfani?

 

DABARAR AIWATARWA

SAMFURIN bayani SAUƘAƘAƘƘE GAME DA TSARIN AIKI TARE DA MAHUKUNTA

Ta hanyar yin amfani da wannan bayani, za ku iya lissafo mahukunta da za a iya aiki da su, ku gano dalilin da ya sa suke da ra'ayin ba da haɗin kai, ta wace hanya za ku ci gaba da aiki tare da su, wane ne zai gudanar da hakan, yaushe, sannan ta wace hanya za a samu kuɗi/tallafin gudanarwa.

Mahukunci (mutum guda ko rukuni) Ra'ayoyin Mahukunci/Manufofi Dabarun Aiki Tare Ayyukan da Suka Rataya Kan Mutane Yayin Aiki Tare Wa'adin Lokaci Ƙiyasin Kuɗin da za a Kashe (ciki har da kayan aiki)
           
           
           
           
           
           

 

SAMFURIN bayani CIKAKKE GAME DA TSARIN AIKI TARE DA MAHUKUNTA

Idan kuna da ƙarin lokaci, to ku yi tunani kan samar da tsarin aikin haɗin guiwa mai cikakken bayani, kamar yadda aka zayyana a ƙasa:

1

BAYANIN AIKI

Wannan sashe ya kawo bayanin shirin a taƙaice (maƙasudai, iyakoki, Ra'in Sauyi, da sauransu) ciki har da ƙalubale da za a iya fuskanta.

2

MAHUKUNTAN SHIRI

Ta la'akari da nazari/zaƙulo mahukunta, a gano muhimman rukunonin mahukunta waɗanda za su taka rawa yayin shirin. Ciki har da mutane ko rukunonin mutane da suka kasance:

  • Shirin da/ko ayyukan shirin sun yi tasiri a kansu kai tsaye da/ko a kaikaice
  • Sun gano yiwuwar samun "abubuwan da suke muradi" daga shirin
  • Za su iya yin tasiri a kan sakamakon shirin ko gudanar da shi

Yi bayani game da dalilin da ya sa kuka zaɓi yin aiki tare da waɗannan mahukunta. Mene ne dalilin da ya sa ku yin aiki da kowane mutum ko rukunin mutane?

3

TSARIN AIKI TARE DA MAHUKUNTA

  • Taƙaita dalili da maƙasudan tsarin aiki tare da mahukunta. Me ya sa kuke buƙatar wannan tsari, sannan ta yaya za ku riƙa amfani da shi?
  • Yi bayanin dalilin da ya sa aka zaɓi waɗansu mahukunta (ɗaiɗaikun mutane ko rukunonin mutane) domin su ba da gudummuwa ga wannan shirin. Mene ne dalilin wannan haɗin guiwa?
  • Yi bayani a taƙaice game da bayanan da za a bayyana wa mahukunta, sannan a cikin wane fasali da harsuna, sannan ta waɗanne kafofi za a samar musu da bayanan.
  • Lissafo duk waɗansu ayyuka/matakai/yanke hukunci da za a iya samu sakamakon haɗin guiwa, horaswa da ayyukan ƙarfafawa, faɗakarwa, da sauransu.
  • Yi bayanin dabarun da aka yi amfani da su wajen samar da haɗin guiwa da kowanne daga cikin rukunonin mahukuntan da aka bayyana.
  • Yi bayanin keɓantattun matakai da za a yi amfani da su domin aiki tare da rukunonin mutane daban-daban (ciki har da mata, addinai ko ƙabilu marasa rinjaye, matasa da sauran rukunonin al'umma da ke fuskantar wariya.
4

JADAWALIN LOKACI

  • Samar da wa'adin lokaci/tsare-tsare da ke zayyana taƙamaimai ranaku/adadi da wuraren da za a gudanar da ayyukan haɗin kai tare da mahukunta daban-daban, ciki har da tattaunawa da haɗin kai.
5

KAYAN AIKI DA NAUYIN DA YA RATAYA KAN MUTANE

  • Zayyana nauyin da ya rataya a kan kowane mahukunci yayin gudanar da ayyukan shiri.
  • Ƙayyade kasafin kuɗi da na sauran kayayyaki da za a yi amfani da su wajen aiwatar da waɗannan ayyuka.
  • Ƙayyade wanda zai gudanar tare da jagorantar tsarin haɗin kan mahukuntan.
6

SANYA IDANU DA AUNAWA

  • Yi bayani game da yadda za a sanya mahukunta a cikin tsarin sanya ido ga aiwatar da shiri.
  • Yi bayani game da mataki da lokacin da za a bayyana sakamakon ayyukan haɗin guiwar mahukunta ga rukunonin mahukunta (misali, jaridu, rahoton nazari, rahoton sanya ido da aunawa, tarurrukan tattaunawa, da sauransu).
  • Yi bayanin ta hanyar da masu aiwatarwa za su karɓi tsokaci daga mahukunta (ciki har da waɗanda shirin ya shafa kai tsare ko a kaikaice). Yi bayanin ta yadda za a magance ƙalubale.
Title
doc
NAZARIN TSARA GUDANAR DA AYYUKA CIKIN AL’UMMA
photo
Details

Takardar gudanar da zaben da tsara ayyuka cikin al’umma

Da zarar an zaɓi Masu Ruwa Da Tsaki da za ayi mu’amala da su, to wannan takardar ayyukan zai taimaka maku wajen tantance mahimman matakan da ƙungiyar ku za ta bi domin gano mafi mabuƙatan al’umma domin ayyukan ku.