Sassa biyu da ke buye za su yi bitar manunai da hanyoyin tantancewa. Manunai masu inganci za su samar da ma'aunan inganci da adadi game da matakan aiwatar da shiri da kuma tasirinsa. Hanyar tantancewa na nufin matakan samu bayanan da suka dace da manunin.
Mene ne manunai?
Manunai su ne ma'aunan adadi ko inganci na nau'uka ko matakan sauyi. A shirye-shiryen PVE a inda sauyi ya kasance abu mai sarƙaƙiya, sannan ya shafi halayya, ɗabi'u, da alaƙa, yana da matuƙar amfani a saita tare da bibiyar sauye-sauyen inganci da za a iya samu.
Me ya sa za a yi amfani da su ?
Manunai na da amfani wajen nuna mana nau'ukan bayanai da za a tattara, sannan za su ba mu bayani game da lokaci, matakai, da dabarun tattara waɗannan bayanai. Amma abin lura shi ne, sai an ƙwanƙwance bayanan ne tukuna za mu iya fahimtar sauyin da ya samu. Ƙwanƙwancewa mai kyau ya haɗa da binciken ƙwaƙƙwafi na bayanai. Wannan na nufin tantance sahihancin bayanai daga waɗansu majiya a ƙalla guda biyu tare da amfani da matakai daban-daban kamar gwada sauye-sauyen adadi ta hanyar bayanan da aka tattara daga tattaunawar rukunin mutanen da ake bincika da kuma tsokacin manyan masu samar da bayanai.
*Bayanin da ke sama ya fito ne daga UNDP/Faɗakarwar Ƙasa da Ƙasa
Manunan adadi da na inganci
Wannan bayani da ya fito daga Cibiyar Aminci ta Amurka ya bayyana waɗansu manyan ɓangarori da shirye-shiryen P/CVE ka iya samar da sauye-sauye ga: halayya, ɗabi'u, da dangantaka.
Ɗabi'u |
Na iya auna:
Wanda ya same shi:
Rauni:
|
Ɗabi'u da ayyuka |
Na iya auna:
Wanda ya same shi:
|
Dangantaka da kafafen sada zumunta |
Na iya auna:
Wanda ya same shi:
Rauni:
|
Wannan albarkatu daga Cibiyar Aminci ta Amurka ta gano wasu mahimman yankuna waɗanda ayyukan P/CVE yakamata su auna canje-canje a: halaye, halaye, da alaƙa.
Akwai manyan nau'ukan manunai guda biyu: manunen sanya ido ga muhalli ke taimakawa wajen auna muhimman sauye-sauye da ke aukuwa a muhallin shiri (ciki har da abubuwan da za su kasance sun wuce ƙarfin ikonku); da manunan sanya ido ga aiki waɗanda ke taimakawa wajen auna cigaban da ake samu da suka shafi samun nasarar sakamakon da ake buƙata da/ko sakamakon shirin. A ƙasa an kawo misalan dukkannin nau'ukan maunai:
Manunan sanya ido a muhalli |
A sanya ido a muhimman sauye-sauye da suka auku a muhallin da ake gudanar da shiri. Waɗannan sauye-sauye na iya shafar sauye-sauyen PVE wanda ke iya yin tasiri a kan shirin ko ya samar da sababbin damarmaki. Misalai:
|
Manunan sanya ido ga aiki |
Suna auna cigaban da aka samu game da aiki ta la'akari da manufofi da maƙasudan da aka zayyana a matakin sakamako, da kuma sakamako da cigaba a matakin tasiri. Misala:
|
*Da dama daga cikin misalan manunai da ke sama sun fito ne daga Ofishin CT. Domin samun ƙarin misalan manunai, ku duba wannan Rumbun Manunai daga Cibiyar Faɗakarwa ta Ƙasa-da-Ƙasa/UNDP, da kuma Bayyanannun Misalan Manunai na CVE daga Ofishin CT.