Matakin Ainawa

Wannan ɓangare zan yi bayanin matakin aunawa na VE da rikici sannan zai yi sharhi a kan kayan aiki daban-daban da ake da su a ynazu waɗanda za su iya taimaka wa a aunawarku. Bayan haka, wannan sashe zai samar da ƙarin kayan aiki game da yadda za ku iya aiwatar da wannan a muhallinku. A lura cewa kayan aikin da aka nuna - Takardar Jagoranci Game da Tsattsauran Ra'ayin Rikici na USAID daga 2009 - sun mayar da hankali ne a kan "abubuwan da ke haddasawa" a maimakon "sauye-sauye da suka shafi tsattsauran ra'ayin rikici. A yanzu, masu ba da tallafi da masu gudanarwa suna kallon muhimmancin nazartar sauye-sauyen VE bayan abubuwan da ke haddasawa. Za a iya amfani da kayan aikin auna rikici da aka yi bayaninsu a ƙasa domin auna auna sauye-sauyen VE ma.   

MENENE WANNAN KUNDIN?

Wannan bayanan jagoranci shi babban muhimmin tsarin aiki ne na da dama daga cikin shirye-shiryen P/CVE na USAID. Duk da cewa babu bayanan rayuwar masu tsattsauran ra'ayi, sannan hanyoyin cusa wa mutane tsattsauran ra'ayi ba guda ba ne, wannan bayanan jagoranci da tsarinsa na abubuwan da ke ingizawa/janyowa hanya ce ta ƙwanƙwance dalilan da ke sa mutane su shiga cikin VEO.

TA WACE HANYA WANNAN YA SHAFI AIKINKU?

Wannan tsarin aiki na taimka muku wajen fahimtar abubuwan da ko ƙarfafa wa mutane guiwa domin su shiga cikin VEO da kuma yadda waɗannan abubuwa za su iya sauyawa a cikin rukunonin mutane masu rauni mabambanta. Sai dai kuma, tsarin ba ya mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi rauni a cikin al'umma ko abubuwan da ke taimakawa wajen inganta damar da mutum ke da shi na kauce wa abubuwan da ka iya cusa masa tsattsauran ra'ayin rikici.  

YAUSHE KUKE SON YIN AIKI DA SHI?

Ya kamata a gudanar da wannan nazari kafin ku tsara shirinku. Fahimtar abubuwan da ke ingizawa zuwa VE zai taimaka muku wajen yin tunani game da abubuwan da ka iya dacewa da al'umma ko rukunin mutanen da shirinku ke ƙoƙarin amfanarwa. Bayan haka wannan tsarin aunawa na da matuƙar amfnai a ɓangaren tsara shirin taimako, haɗawa, da sake haɗawa, da kuma shirye-shiryen gyaran hali domin fahimtar dalilin da ya sa mutane ke barin ƙungiyoyin VE da kuma taimakon da wataƙila suke buƙata domin aikata hakan.  


Title
Ƙwanƙwance abubuwan da ke ingiza mutane domin su riƙi tsattsauran ra'ayin rikici: Takardar Jagorancin USAID Game da Abubuwan da Ingiza Mutane Zuwa Shiga VE
Title
BAYANIN KAYAN AIKIN

Jadawalin da ke ƙasa ya samar da samfurin tsarin abubuwan da ke ingizwa/janyowa waɗanda aka ɗauko daga Bayanan Jagoranci ga Abubuwan da ke Janyo Tsattsauran Ra'ayin Rikici na USAID. Jadawalin na nuna yanayi da ke ba wa VE wurin zama, abubuwan da ke ingizawa (wanda ke sa mutane su shiga cikin VEO) da kuma abubuwan da ke janyowa (yanaye-yanayen ƙungiyar da suka kasance masu jan hankalin mutane).

MUHALLI MAI KYAU
pushpull
 
Title
doc
Takardar Aiki ta Kimanta Lamurran da ke kawo VE
photo
Details

Takardar aiki ta 1 ta Kimannta Lamurran da ke kawo VE

Ga nan tsarin aiki da zai taimaka muku wajen aiwatar da aiki domin ƙwanƙwance abubuwan da ke kawo VE a muhallinku. Ku daure ku duba bayanan da aka ba da shawarar amfani da su domin samun ƙarin bayanai game da wannan tsarin aiki da yadda za a yi aiki da shi.

Yayin da tsarin abubuwan da ke ingizawa/janyowa ya kasance sanannen tsarin aiki na fahimtar lamarin cusa tsattsauran ra'ayi, hanyoyin janyo rikici da suka shafi cusa ra'ayi sun kasance masu ruɗani sannan suna buƙatar sama da hanyar ƙwanƙancewa guda ɗaya. Ƙarin misalan tsarin aikin da ke nazartar al'amarin cusa ra'ayi sun haɗa da:

Title
Binciken Kayan Aikin Auna Rikici

Cusa tsattsauran ra'ayi ba abu ne da ya kasance mai bin tafarki iri guda ba, musamman kasancewar mutane da ƙungiyoyi na tasirantuwa daga sauye-sauyen da ke faruwa a muhallinsu. Domin cikace ƙwanƙwance sauye-sauye da abubuwan da ke kawo VE, yana da muhimmanci a yi tunani game da sauye-sauyen rikici a matakin bai-ɗaya. Sannan yana da amfani a gano abubuwan da ke kawo juriya da ƙarfafa mutane domin ƙin ruɗuwa da kiraye-kiryen VE. Akwai kayan aiki daban-daban da za ku iya amfnai da su domin gudanar da bincike game da rikici, sannan za a iya ɗaukar hannu daga gare su domin nazartar sauye-sauyen VE. 

Title
doc
KUNDIN BINCIKEN RIKICI TARE DA TSARIN YADDA ZA KU IYA AMFANI DA SHI
Photo
Details

Kundin nazarin Rabe-rabe da MAHAƊAI

Waɗannan kundin zai taimaka wajen Nazarin yanayin Rabe-rabe da MAHAƊAI da ke gurɓata zamantakewa, ko ƙarfafa zamantakewa a tsakanin ƙungiyoyi da ke cikin al'umma. Wannan shine tushen ƙa’idojin Ba-Cutarwa kuma za a iya amfani da shi akai-akai yayin gudanar da ayyuka tare da tabbatar da cewa aiyyukan ku na la’akari lamuran da ke haddasa rikici.  

 

image
Details

Tsarin Tsarin Nazarin Rikici na USAID (CAF 2.0)

Wannan kundin na taimakawa wajen tattara bayanan MAHAƊAI, da tsara su, da kuma tantance yanayin da nazarci ire-iren rikici da kuma gano tasirinsu nan gaba. 

image
Details

Tsarin Binciken Rikici na GPPACDokoki da Matakan Aiki

Wannan nazari game da rikici na da kayan bayanai masu muhimmanci da za su iya taimaka wa masu aiwatarwa, waɗanda an lissafo su a ƙasa:  

  • Gano Mahukunta Aikin gano mahukunta na mayar da hankali ne wajen jero mahukunta daban-daban da suke cikin rikici ko rikici ya shafe su tare kuma da nazartar dangantakarsu da rikicin da kuma junansu. 
  • Nazarin Mahukunta da Ƙungiyar Sau da dama akan yi amfani da waɗannan bayanai domin sasantawa tsakanin ɓangarori daban-daban na rikici ko idan ana ƙoƙarin fahimtar dangantakar mahukunci da rikicin. 
  • Bishiyar Li'irabin Rikici Bishiryar li'irabin rikici na kama da bishiyar li'irabin matsala kasancewar ya mayar da hankali wajen bayanin babbar matsala, binciko musabbabin matsalar, da kuma gano tasirorinsu. 
  • Binciken rikici ta hanyar nazari Wannan mataki ya haɗ da gano mahukunta da bishiyar li'irabin rikici ta hanyar gano cewa abubuwan da ke janyo rikici da tasirorinsa ba su kasance masu bin turba guda ba sannan sau da dama sukan danganta ga masu aikata su. 
Title
Bincike da tattara bayanar

Dabarun tattara bayanai daban-daban na iya taimaka muku wajen auna abubuwan da ke jawo VE da rikici, ciki har da dabarun da ake aunawa adadinsu (ziyara) da waɗanda ake iya auna ingancinsu (mayar da hankali kan tattaunawa a cikin rukuni). Kowace hanya na da alfanunta da rauninta. Sau da dama haɗa hanyoyi guda biyu (hanyar gambiza) na sa a yi gwaji mai kyau. Dacewar hanyar da aka yi amfani da ita na iya tasirantura da muhalli da kayan aikin ƙungiyarku, da iya bincike, da sanin batun, da kula lokacin gudanarwa. Ana ba da shawarar koyaushe a janyo ƙwararrun manazarta da suka samu horaswa game da waɗannan dabaru, sannan suka fahimfi tasirin bincike a kan tarbiyyar mutane, sannan suka kasance a baya sun gudanar da bincike a wuraren da ke fama da rikici.

Kayan aikin Gidauniyar Sin: Bincike da Yaƙar Tsattsauran Ra'ayin Rikici Bayanan Jagoranci ga Mai Gudanarwa na samar da bayani game da dabarun da suka shafi adadi da inganci a cikin Jadawali na 1 da ke ƙasa. Za a iya samun liƙau ɗin samun ƙarin kayan aiki da bayanan jagoranci game da gudanar da bincike kan VE a Ɗakin Bincike.

Jadawali na 1: Dabarar Adadi Saɓanin na Inganci

Bincike/Na Adadi  Dabarun Duba Inganci 
Tsararriyar hanyar tattara bayanai daga masu ba da amsa wanda jami'an da aka ba wa horaswa suke yi cikin ingantaccen salo rubutacce  Hira, rukunin waɗanda za a bincika, lura, da rubutattun bayanai 
A auna amsoshi domin gudana lissafi A dogara a kan manazarta domin bibiya da samar da buɗaɗɗen ƙarshe 
Na da manufar yin ikirarin da zai haɗa da mutane da dama Mayar da hankali kan mutane kaɗan amma da yin abin yadda ya kamata
Ba mu damar kallon abubuwa daban-daban game da ayyukan masu tsattsauran ra'ayin rikici, da ɗabi'unsu, da halayensu. Haskaka matakai da hanyoyin cusa tsattsauran ra'ayi

 

Title
doc
NAZARIN GUDUMOWAR MATASA
Photo
Details

Haɗa kai da matasa_ƙungiyoyin matasa domin ƙwanƙwance ƙarfi da rauni

Motsa jiki na farko yana mai da hankali kan nazarin abubuwan da ke shafar matasa waɗanda za su iya ba da gudummawa ga tsattsauran ra'ayi ko wasu halayen rashin zaman lafiya da haɗari.

image
Details

Tsara ayyukan al’ummarku

Motsa jiki na biyu yana jan hankalin matasa don nazarin al'ummominsu ta hanyar samar da bayanan yadda al'ummomin ke tsara rayuwar matasa.

Title
Ganowa da rage son zuciya
Kowa yana da fahimta iri daban wanda ka iya yin tasiri kan kasancewarsu a turbar adalci, saboda haka a koyaushe ku riƙa tunanin ko son kai na iya yin tasiri a kan bincike. Wannan na iya kasancewa keɓantaccen son kai da kuke da shi ko kuma son kai na mai amsawa wanda zai yi tasiri a kan amsoshin da za su bayar na tambayoyinku.

Ga nan tambayoyi kaɗan da ya dace ku yi la'akari da su kafin da kuma lokacin gudanar da bincikenku domin yin nazari game da son kai da za a iya samu wanda zai iya yin tasiri a kan sakamakon gwajinku:

Rage son kanmu
  • Me ke ƙarfafa aiwatar da wannan bincike? Me ya sa kuke gudanar da wannan bincike, sannan me ake son ta samar?
  • Ta yaya tushenmu ke yin tasiri a kan binciken gaskiya? Mene ne manyan hasashe, sannan shin an gwada su?
  • Mene ne zai iya kuɓuce mana ko mu yi masa fahimtar baibai sakamakon tushenmu? Shin akwai waɗansu ra'ayoyi na daban?
  • Waɗanne ne matakan ƙwanƙwancewa da ake buƙata (ƙasa, al'umma, mutane, da sauransu)
  • Ta yaya za mu iya rage illar da za a iya samu game da hanyar da muke bi domin aunawa?
Gano son kai da masu ba da amsarmu ka iya cuɗanyuwa da shi tare kuma da ingancin tushen bayani
  • Mene ne tushen bayananmu? Shin sun samu sauyi daga waɗansu tushen bayanai ko hanyar tattara bayanai?
  • Nau'ukan mahukunta ko rukunonin mahukunta nawa ne suke da hannu cikin bincikenmu? Ta yaya muke neman ra'ayoyi daban-daban?
  • Wane ne ka samar mana da bayanai? Mene ne ke jan ra'ayinsu domin su samar mana waɗannan bayanai?
  • Ta yaya suka samu wannan bayani (misali, shin sun kasance shaidun gani-da-ido ne ko jita-jita suka samu daga majiya ta kusa ko ta nesa)?
  • A wane wuri suke samar mana da wannan bayani? Shin wannan na iya yin tasiri a kan bayanin da suke samar mana da dalilin da ya sa suke samarwa?