Al'amuran da ke Kawo Haɗi

Yayin da kuka kai ƙarshen ToC ɗinku sannan kuka fara tsara shirye-shiryenku, akwai al'amura daban-daban da ke kawo haɗi da ya kamata ku yi la'akari da su.  

Nazarin Jinsi da Jawowa Jiki

Bincike ya nuna cewa abubuwan da ke haifar da haɗarin VE (da juriya) na da bambanci tsakanin maza da mata. Saboda haka, muna ba da shawarar a yi nazarin jinsi domin samun damar tsara shiri ga mutane daban-daban da ke da raunin da za a iya cusa musu ra'ayin VE. Matsayin jinsi a cikin al'ummominku zai yi tasiri a kan yadda za ku tsara shirinku ga dukkannin mata da maza, da yara mata da yara maza da ke da rauni. Domin samun ƙarin bayani, a daure a duba Ɓangaren Daidaiton Jinsi da Damawa da Kowa da Samar da Haɗi.

Title
doc
NAZARIN GAMAYAR DAIDAITON JINSI
photo
Details

Takardar gudanar da nazarin Gamayar Daidaiton Jinsi

Wannan takardar gudanar da nazari zai taimaka majen yin la'akari da jinsi a yayin da ake tsara aiyyuka da aiwatarwa.

Title
Sanya Cigaba Mai Kyau na Matasa (PYD) a cikin Tsarin Aiki

Sannan za a iya amfani da Tsarin Shirin Matasa na PYD a matakin tsarawa domin gano ayyukan P/CVE da ke samar da nau'ukan PYD daban-daban. Ƙungiyarku na iya samar da tsari na kowane ɗaya daga cikin manufofin da ke da alaƙa da matasa da kuma rukunin al'ummar da kuka gano domin shirinku. Ku je zuwa Sashen Haɗi Game da Damawa da Matasa domin samun bayanai game da ra'o'in PYD da kuma misalan matakan PYD.   

Title
doc
PYD NAZARIN AIKIN MATASA
photo
Details

Takadar Gudanar da Nazarin Ayyukan Matasa

Wannan takadar gudanar da nazari zai taimaka wajen tsara aiyyukan ku. Ya samo tushe daga ingantatun ayyukan matasa na ci gaba da ke da tasiri da haɗaɗiiyar adabin zamantakewar al’umma. 

Title
Haɗin-gwiwa da Masu Ruwa da Tsaki wajen tsara ayyuka

Haɗin gwiwa da Masu Ruwa da Tsaki na da matuƙar muhimmanci a yayin da ake yin nazari da tsara ayyukan ci gaban al’umma. Haɗin gwiwa da Masu Ruwa da Tsaki na taimaka wa al’umma su mallaki ayyukan, kuma a samu muhimman gudunmowar al’umma domin cimma nasarar da dorewar ayyuka. Haka kuma, fifita buƙatun al’ummar da ake yi wa hidima a yayin da ake tsara ayyukansu na tabbatar da kyawawan sakamako. Sashen da ke bayanin hulda da Masu ruwa da Tsaki, na ƙunshe da ƙarin bayanai game da ƙa'idodin haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki, jagora kan gudanar da nazarin ayyukan da kuma bayanin yadda wannan haɗin gwiwa ke da kyakyawan tasiri kan aiki na P/CVE.