Hanyoyin Tantancewa/Tattara Bayanai

logframe3

Hanyar Tantancewa kayan aiki ne da aka yi amfani da su da kuma matakan da aka bi domin tattara bayanan da ake buƙata domin auna cigaba. Bayanan da aka tattara na iya shafar adadi ko inganci. Bayanan adadi sun fi kasancewa waɗanda za a iya musu ƙari sannan sau da dama ana karɓar su ne ta hanyar hira, rukunin nazari, da sauran dabarun tattara bayanan adadi. Ana amfani da bayanan adadi domin amsa tambayoyi kamar su, guda nawa, yaya mizanin yawan aukuwar sa, wane mizani, da adadin yaya, sannan yawance akan tattara ne ta hanyar bincike.

Dabarun tattara bayanai na iya kasancewa mai tsari na bai ɗaya, mai ɗan tsari kaɗan, ko marar tsari na bai ɗaya.

MUHIMMANCI DA KOMA BAYAN MUHIMMAN DABARUN TATTARA BAYANAI DA SUKA SHAFI P/CVE:

  Muhimmanci a muhallin PVE  Koma baya a muhallin PVE
Yin Sobe Dabara ce ta tattara bayanai da samun haske game da batu, sau da dama ta hanyar tambayau a kan takarda ko ta cikin na'ura.
  • Kasancewar mai ba da amsa na da damar ɓoye kansa zai sa a samu amsoshin gaskiya
  • Na iya tattara bayanai daga rukunin jama'a masu yawa
  • Sauƙin farashi
  • Saurin ba da amsoshi
  • Masu ba da amsa na da lokacin yin tunani game da amsoshinsu
  • Waɗanda ke da Intanet/wayar da ke iya kamawa ne kawai za su iya samu
  • Mahalarta ba za su iya neman ƙarin bayani ba idan ba su fahimci tambayar ba
  • Amsoshin da za a bayar na iya kasance kaɗan
  • Ba za a iya tambayoyin bibiya ba
Tattaunawa Cikin Tawagar Nazari Akan tambayi rukunin mahalarta, yawanci daga tushe iri guda (shekara, jinsi, ƙwarewa, da sauransu) game da ra'ayinsu dangane da wani batu da ya shafi shiri. Wani mutum na daban ne ke tsara tattaunawar rukunin nazari sannan yawanci rukunin kan ƙunshi mahalarta 6 zuwa 1.
  • Mayar da hankali kan wani batu taƙamaimai kamar matsalar al'umma
  • Tattaunawa na samar da ra'ayoyi mabambanta
  • Yana samar da damar musanyen ra'ayoyi tare da sauran mutanen da wataƙila suna da ra'ayoyi na daban (misali, shuwagabannin matasa na iya samun ilimi daga 'yan sanda ko kuma 'yan sanda su samu daga gare su)
  • Yana ba da damar a nazarci bayanai nan take
  • Son zuciyar mai gudanarwa: Mai gudanarwa na iya karkata ko ya nuna son zuciya, wanda hakan na sa a samu sakamako na daban
  • Son zuciya da ya shafi mu'amala: mahalarta na iya ba da amsoshin ƙarya domin ɗaukaka matsayinsu a idanun sauran mahalarta (misali, matasa na iya ba da amsoshi na daban idan suna tare da 'yan sanda a cikin ɗakin)
  • Tunani iri guda: mahalarta na iya aminta da waɗansu mutane da ke cikin rukunin domin kawai su taƙaita jayayya, alhali a haƙiƙanin gaskiya suna da ra'ayi na daban
  • Rashin sirrantawa: wataƙila mahalarta ba za su bayyana waɗansu bayanai na sirri ba (misali, wataƙila matasa ba za su samuwa nitsuwar zuci na bayyana hulɗayyarsu da ƙungiyar VE ba)
Tattaunawa da Manyan Masu ba da Bayanai Tattaunawa gaba-da-gaba na iya kasancewa mai bin tsari na bai ɗaya, mai ɗan bin tsari kaɗan, ko marar tsari na bai ɗaya. Waɗanda za a yi wa tambayoyi na iya kasancewa jami'an gwamnati, ma'aikatan NGO, wakilan ɓangarori masu zaman kansu, shuwagabannin addinai, malamai, da sauransu. 
  • Samun cikakken bayani game da wani batu daga wani masani
  • Yana ba da damar nazari sosai game da ilimummuka da aka samu ta hanyar amfani da waɗansu dabaru
  • Sakamako na iya zama bisa son rai: yana buƙatar jin ra'ayoyin mahalarta da dama da ke da ra'ayoyi mabambanta
  • Yana iya zama mai wahalar ganewa "masana”
  • Yana iya zaman mai wahalar tsarawa
  • Cin lokaci
Lura Nau'ukan lura guda biyu: 1) Lura daga waje hanya ce inda mai lura ba ya ta'ammuli kai tsaye da abin da yake sanya ido a kai. 2) Ana samun lura daga ciki ne idan mai sanya ido na hulɗ kai tsaye da abin da yake sanya wa ido (misali, shiga cikin mutane ko ƙungiya) da kuma mahalarta shirin da ake sanya ido a kansu.
  • Za a iya amfani da shi wajen gano dalilin da ya sa shiri ba ya samar da sakamakon da ya dace
  • Za a iya amfani da shi yayin da ya kasance yana da wahala a yi amfani da amintattun hanyoyin tattara bayanai, kamar idan mutane sun ƙi a musu tambayoyi.
  • Za a iya lura da abubuwan da ke haifar da VE, kamar huɗubobi da ke yayata rikici.
  • Samun cuɗanya da ƙungiyoyi na iya kasancewa abu mai wahala
  • Zai iya kasancewa abu mai haɗari a waɗansu muhallan VE
  • Yana ɗaukar tsawon lokaci kafin a samu bayanan da ake buƙata
  • Ya taƙaita ne ga wuraren da ba su da yawa
  • Dangane da lura daga ciki, za a iya ɗaukar tsawon lokaci kafin mahalarta su aminta da mai nazarin

* An cirato bayanan da ke jadawalin da ke sama ne daga: Cibiyar Faɗakarwa ta Ƙasa-da-Ƙasa/UNDP Yaƙar Tsatsauran Ra'ayin Rikici da Rage Haɗari: Bayanan Jagoranci ga Tsarawa da Auna Shiri (a duba shafi na 110 domin samun ƙarin bayani game da dabarun tattara bayanai da suka shafi nazarce-nazarce); IMPACT Europe: Kayan Aikin Gwaji domin ƙwararru da ke aikin da ya shafi yaƙi da tsattsauran ra'ayin rikici; da “Tsarin Sakamako: Amfani da Sanya Ido da Aunawa a Cikin Shirye-Shiryen da Suka Shafi Shawo Kan Rikice-Rikici” (shafi na 207-209) domin ganin muhimmanci da koma bayan waɗansu ƙarin hanyoyin tattara bayanai.