Nazarin bincike

Title
Inganta Matsayi da Auna Tasirin Sadarwar Sauyin Ɗabi'a game da P/CVE

Ƙungiyar Chifae (Chifae) ƙaramar ƙungiya ce (CSO) da take Tangier, Moroko. Chifai ta aiwatar da shirin watanni bakwai wanda ya mayar da hankali kan faɗakar da matasa game da tsattsauran ra'ayin rikici. Shirin ya ba da horaswa ga ma'aikata 15 da ke ɓangaren hulɗayya da ilimi. An ba da horaswar ne game da dabarun sanarwa domin su gudanar da shirin faɗakarwa na sati biyu a wuraren wasanni domin koyar da haƙuri da samar da inganta haɗin kai a Beni Makkada da ke Tangier.

Bayan taron ƙara wa juna sani na kwanaki biyar, ma'aikatan Chifae huɗu zuwa biyar (tare da tawagar taimako FHI 360) sun samar da da kundin jagoranci domin shirin faɗakarwar Chifae. Wannan kundin jagoranci ya haɗa da tsarin M&E domin gano ko shirin faɗakarwar ya samar da wani tasiri a kan ilimim matasa, halayyarsu, da ɗabi'unsu. Chifae ta tsara bunƙasa shirin yadda zai karaɗe illahirin garin Tangier. Saboda da haka, auna sakamakon faɗakarwar a Beni Makkada ya kasance wajibi domin samun shaidar da za ta goyi bayan tsare-tsaren shirin Chifae a nan gaba.

Chifae ta fara gudanar da shirin faɗakarwa a Beni Makkada a ranar 18 ga watan Yuni na shekarar 2019. Kirarin shirin faɗakarwar wato #MuhalliDominKowa, na nufin al'ummar da ke girmama ra'ayin juna.

Shirin faɗakarwar ya ƙunshi ɓangarorin da ke ƙasa:

  • Shafin Facebook na harkokin Chifae wanda ma'aikatan Chifae ke gudanarwa. Chifae ta ba da amsoshi ga rubuce-rubuce da dama da aka tura ta shafin Facebook ɗin.
  • Tallar shafin harkokin a kan fitaccen kafar intanet labarai da kuma jaridar da ake wallafawa sati-sati (jarida tilo bugun Tangier).
  • Sanya taken shirin yadda za a iya gani filayen ƙwallo guda 15 a Beni Makkada.
  • Rarraba kayan atisayen ƙwallo guda 400 da ke ɗauke da rubutn taken shirin zuwa ga 'yan wasannin CSOs a Beni Makkada.
  • Manyan allunan sanarwa a wurare daban-daban guda huɗu a cikin babban filin wasanni na Tangier da kuma Beni Makkada.
  • Shirin gidan rediwo na tsawon sakanni 30 da ake sanyawa sau huɗu kullum a na tsawon makwanni biyu a gidan rediyo na cikin gari.

Dabara da hasashe-hasashen M&E

Chifae ta tsara bincike (wanda aka fassara zuwa Darija na Moroko) domin domin tattara bayanai da suka shafi ra'ayoyin matasa game da farawa da kammala shirin, da halaye da ɗabi'un matasan a cikin al'ummominsu. Chifae Na son fahimtar ra'ayin matasa game da haƙuri da juna da sauran ɗabi'u masu kyau.

Chifae ta yi tsari mai sauƙi ga binciken domin ya ba wa masu sa kai damar tattara bayanai ta hanyar tattaunawar gaba-da-gaba. Da farko Chifae ta tsarin tambayoyi ga jerin mutane guda tun daga farko har ƙarshe domin samun damar auna tasirin da faɗakarwar ke iya samarwa. Wannan mataki zai ba wa Chifae damar fahimtar yadda masu ba da amsa za su iya sauya halaye da ɗabi'un da suke da shi kafin fara faɗakarwar zuwa bayan kammalawa. Sai dai kash...! Masu sa kai ba su samu damar yin tambayoyi ga msu ba da amsar da suka tambaya a farko ba yanzu da aka kammala shirin faɗakarwar. Saboda haaka, tattara bayanai ya ƙunshi matasan da suka halarci shirin faɗakarwar Chifae kawai.

Adadin mutanen da shirin ya ƙunsa matasa 100 ne, ciki har da matasa masoyan wasanni/ƙwallon ƙafa (tare da daidaiton jinsi duk da al'adun gargajiya da ke sanya takunkumi ga jinsi daban-daban a cikin al'umma) Chifae ta tsara yadda kowanne daga cikin 'yan sa kai zai iya karɓar amsoshin tambayau 20 a ya yi yawa, domin jimillar bincike 100+.

Ɗaya daga cikin manyan hasashe shi ne cewa dukkannin matasa da ke ba da amsa sun kalli (ko sun ji) bayanai game da shirin faɗakarwar Chifae. An haɗa da tambayoyin tantancewar farko domin al'amarin. Chifae ta yanke shawarar mayar da hankali kan manyan filayen wasannin ƙallon ƙafa da kuma filayen ƙwallon maƙwabta da na al'umma kafin fara shirin faɗakarwar da kuma bayan kammala shirin faɗakarwar.

Chifae ta nemi haɗin kan matasa 'yan sa kai daga cikin al'umma ta la'akari da ilimin da suke da shi game da al'ummar, inda aka ba su horaswa domin su gudanar da binciken. Horaswar ta shafi yin bayani gam da shirin, dalilin binciken, da dabarun gudanarwa, da kuma abubuwan da suka shafi tabbatar da Rashin Yin Illa.

Title
Taƙaita sakamako
Ilimi Ɗabi'u Ɗabi'u
  • Kashi 52% na matasan da suka ba da amsa na da ra'ayin cewa saƙon shirin fadakarwar (kira zuwa ga zaman lafiya da haƙuri da juna domin magance rikici a manyan filayen ƙwallon ƙafa) ya kasance a bayyane ba tare da ruɗani ba.
  • Kusan biyu bisa uku (63%) na dukkannin masu ba da amsa sun aminta da saƙon shirin faɗakarwar, inda suka nuna matuƙar amincewarsu da da saƙon da ke magana game da haƙuri da ra'ayoyin juna.
  • Kimanin rabi (47%) na dukkannin matasa da suka ba da amsa sun nuna cewa suna kallon masu goyon bayan waɗansu ƙungiyoyi da idon fahimta sosai bayan an kammala shirin faɗakarwar.
  • Kusan ƙarin kaso 30% na matasa (daga 44% zuwa 72%) sun samu gamsuwar zuci game da matasan da suka fito daga waɗansu al'umma a ƙarshen shirin faɗakarwar.
  • Ƙarin kaso 34% na matasa masu ba da amsa sun bayyana cewa suna da kamanceceniya sama da yadda suke da bambance-bambance tsakaninsu da matasan da e goyon bayan waɗansu ƙungiyoyi na daban bayan sun yi cuɗanya da shirin faɗakarwar na #Fada2_Liljami3.
  • Kafin lokacin shirin faɗakarwar, ɗya bisa ukun matasa sun ba da amsar cewa za su iya bunƙasa amincewa da juna ta hanyar nuna soyayya da gaskiya yayin wasanni, yayin da kashi 14% ne kaɗai suka tafi kan cewa ƙoƙarin sadarwa da faɗakarwa na iya zama abubuwan da za su taimaka wajen samar da aminta da juna.
  • A lokacin kammala shirin faɗakarwar, ƙarin kaso daga cikin matasa (36%) sun bayyana sadarwa da tattaunawa a matsayin hanyar samar da aminci tsakanin mutane, wato kusan daidai da kason masu goyon bayan girmama ra'ayoyin juna yayin wasanni (39%).

DARRUSAN DA AKA KOYA DAGA MATAKAN CHIFAE NA M&E:

Chifae ta samu nasarar tabbatar da cewa matasa a Beni Makkada sun aminta sosai da saƙon game da girmama ra'ayoyin juna, wanda ke nuni da sauyin halayen matasan da suka halarci shirin faɗakarwa na Chifae sannan an nuna cewa matasa za su girmama sadarwa da sauran matasa a matsayin ɗaiɗaikun mutane da ke wajen tsarin gasar wasanni. Wannan ilimi ya taimaki Chifae wajen tsara cigaba da shirin faɗakarwar zuwa ga wuraren da suka fi na da yawa tare da bunƙasawa domin faɗakarwa dangane da waɗansu batutuwa na daban.

Chifae ta auna tasirin shirin faɗakarwar sannan ta auna ƙwarin ƙwarewar ma'aikata game da samar da sauyi a ɓangaren zamantakewa da ɗabi'a yadda ya kamata ta hanyar shirin faɗakarwa. Sannan M&E ya ba wa Chifae damar gano ƙarin abubuwan da ake buƙata domin bunƙasa shirye-shiryen faɗakarwarsu da kuma ingancin shirin na gaba ɗaya.

Sannan auna shirin faɗakarwar ya taimaka wa Chifae wajen gano muhamman giɓi game da aiwatar da lamuransu. A misali, Chifae ta tsara yadda za ta sake mayar da hankali game da al'amuran jinsi domin samun damar damawa da mata a cikin al'amuransu. Wannan darasi ya samu ne yayin da aunawar ya gano cewa mata 'yan kaɗan ne kawai aka yi bincike tare da su sakamakon takunkumin al'ada.