Nazarin Bincike

Title
Tallafawa Domin Aiwatar da Aikin P/CVE da Matasa ke Jagoranta: Mujallar Matasan Sharekna

Ƙungiyar Joussour de Citoyenneté (Joussour) ƙungiyar fararen hula ne da ke Tunusiya (CSO) wanda ke gudanar da ayyuka tun a shekarar 2014 domin tallafa wa matasa da al'umma a El Kef. A shekarar 2019, Jussour ta fara buga Mujallar Matasan Sharekna, wanda ya ya kasance aikin watanni shida da ke da manufar janyo matasa da mambobin al'umma da ke yankuna biyu a da ke yammacin Tunusiya (El Kef da Jendouba) domin faɗakarwa game da cigaba a cikin al'ummominsu tare da taimakawa wajen magance VE. Domin cimma wannan manufa, Joussour ta tallafa wa ƙaddamar da mujallar da ta mayar da hankali kan matasa sannan take ƙarƙashin jagorancin matasa domin inganta halartar matasa da haɗin kansu. Sannan aikin na da manufar bunƙasa ƙwarewar sauran CSOs a waɗannan yankuna tare da samar da haɗin guiwa mai ƙarfi a tsakaninsu.

Siffofin ayyukan Mujallar Matasan Sharekna da dama na iya kasance masu amfani wajen tsarawa, shiryawa, da gudanar da shirin P/CVE:

  • Bitar yadda Joussour ta yi aiki tare da mahukunta daga cikin al'umma na dun tsawon zangon gudanar da shirin.
  • Bitar yadda Joussour ta yi aiki tare da matasa tare da tabbatar da cewa matasan sun tagaza yayin tsarawa da aiwatar da shiri.
  • Bitar tsare-tsaren Joussour da shirye-shirye domin ɗorewarwannan shiri.
Title
Yin Aiki Tare da Mahukunta a Cikin Al'umma

Game da shirin Mujallar Matasa ta Sharekna, Joussour ta nemi haɗin guiwar mahukunta daban-daban tun daga farkon fara gano buƙatunsu da kuma nazarin mafita da za a iya samu.

MATAKIN SAMU

A Fabarairun shekarar 2019, Joussour ta halarci taron ƙara wa juna sani tare da ƙungiyoyin fararen hula (CSOs) da suka fito daga ƙasashe shida na yankin Maghreb da Sahel a inda suka yi musanyen ilimummuka game da dabaru da kayan aikin gudanar da P/CVE, ciki har da amfani da kafafen sadarwa da kuma haɗa kai da matasa. Lokacin da tawagar Joussour ta dawo El Kef, sai suka shirya taron gudanar da aiki tare da CSOs da suka fito daga yankinsu domin su gabatar musu da abin da suka koya a lokacin taron ƙara wa juna sani da suka gabatar, sannan suka nemi shawarwari domin sanin buƙatun al'umma da ke da alaƙa da tsattsauran ra'ayin rikici a yankin, tare kuma da haɗa kai domin gudanar da shirin Sharekna.

MATSAKIN TSARAWA

A wannan mataki, Joussour ta tsara yadda za ta gayyaci mahukunta daban-daban domin aiwatar da shirin. Sun gano abubuwa biyu masu muhimmanci wajen aiwatar da hakan: (1) samar da Kwamitin Masu ba da Shawara da ta ƙunshi abokan haɗin guiwa guda biyar daga cikin fararen hula da shuwagabanni domin tallafawa tare da jagorancin aikin matasa; da kuma (2) gayyatar waɗansu ƙananan ƙungiyoyi (misali, ƙungiyoyin yankuna da na shiyoyi, ƙungiyoyin kafafen sadarwa, da sauransu) daga yankuna biyu da abin ya shafa domin gabatar da shirin tare da jagorancin aiwatar da shirin.

 

MATAKIN AIWATARWA

Lokacin da Joussour ta samu kuɗi domin aiwatar da shirinta, sai ta gudanar da taron tattaunawa tare da abokan haɗin guiwarta wato ƙungiyoyi guda biyar da suka haɗa guiwa da ita (CSOs na matakin ƙaramar hukuma, Dandalin Matasa, da kuma Gidan Al'adu da ke El Kef sai kuma Mahukuntan Jendouba) domin samar da yarjejeniyar haɗin guiwa, zaɓen mambobi daga kowane ƙungiya domin kasancewa a cikin kwamitin masu ba da shawara, sannan da kammala tsarin aiwatarwa da a baya aka farasamarwa.

MATAKIN KOYO

Yayin da fitowar farko ta mujallar ta samu, Joussour ta nemi tsokaci daga mahukunta a cikin al'umma game da jaridar da kuma matakan tabbatar da ɗorewarta. A duk tsawon lokacin aiwatar da shirin, sannan musamman a zangon Bayan Bitar Aiki, Joussour ta gayyaci mutanenta domin tattaunawa game da darrusan da aka koya da kuma yadda za a ɗau hannu daga ayyukansu da tsare-tsarensu domin ci gaba da gudanar da mujallar.

Title
Damawa da Matasa a Lokacin Aiwatarwa da Koyo

Ƙari a kan gano matasa a matsayin manyan masu cin gajiyar shirinta, Joussour ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa shirin ya dama da matasa kai tsare a matsayinsu masu ba da gudummawa ga shirin da kuma al'ummominsu.

  • Joussour ta fahimci cewa, idan ana so matasa su jagoranci bunƙasar mujallar, to dole sai sun samu ilimi da kayan aikin da ake buƙata. Saboda haka, ɗaya daga cikin muhimman ɓangarorin tsara shiri shi ne inganta ƙwarewar matasa ta hanyar ba da horaswa da ci gaba da jagoranci. Inda masu alhakin aiwatar da hakan su ne ƙwararru a ɓangaren sadarwa, tawagar Joussour, da kuma Kwamitin Shawarwari. A lokacin Bitar Bayan Aiki, matasan da suka halarta sun tattauna ta fuskokin da suka ji gajiyar horaswar da kuma ta yadda wannan ilimi ya ƙarfafa musu guiwar zamantowa wakilan samar da sauyi mai kyau a cikin al'ummominsu.
  • Joussour ta yi amfani da shawarwarin matasa yayin tsara ayyukan shirin. A lokacin taron ƙara wa juna sani na buɗewa, Joussour ta tattara bayanai game da ra'ayoyi da buƙatun matasa, sannan waɗannan bayanai sun yi amfani wajen tsara shirin ba da horaswa ga matasan. A misali, lokacin da Joussour ta fahimci cewa matasa sun ba da muhimmanci ga ilimin da za a iya aiwatarwa, sai suka bi tsarin jera ayyuka ta yadda za a gudanar da ziyarar bincike da tattara bayanai ne a lokacin shirin ba da horaswa ga matasan, a maimakon lokacin da aka kammala ba da horaswar.
Title
Shiri Domin Ɗorewa

Joussour ta tsara yadda shirin zai ɗore ta fuskoki da dama a lokacin shiryawa da aiwatar da shirin:

  • A Matakin Samu, Joussour ta fara tattaunawa da hukumomi a matakin ƙaramar hukuma waɗanda ka iya tallafa wa shirin bayan an cinye tallafin farko da aka bayar.
  • A lokacin Tsarawa, Joussour ta sanya abubuwa da dama a cikin shirin waɗanda za su taimaka wajen ɗorewarsa:
    • dabarunta na aiki tare da abokan haɗin guiwa daban-daban da mahukunta masu faɗa-a-ji, ciki har da hanyar bi ta hannun kwamitin masu ba da shawara
    • mayar da hankali da ya yi a kan inganta ƙwarewa da aiki tare da ƙwararru a fannin sadarwa domin tsara horaswa, jagoranci, da bayanai waɗanda Joussour zai yi amfani da su wajen ba da horaswa da tallafa wa ƙarin matasa
    • Bitar Bayan Aiki wanda ya samar da haɗin kai tsakanin matasan, Kwamitin Masu ba da Shawara, mai horaswa, da tawagar Joussour domin yin nazari a game da abubuwan da suka koya sannan su samar da tsarin da zai taimaka wa shirin domin ya ɗorewa

Ƙoƙarin Joussour na ganin cewa shirin ya ɗorewa ya haifar da ɗa mai ido. Lokacin da kuɗin shigar da suke da shi ya ƙare, Joussour ta haɗo kan matasa, abokan haɗin guiwa, da mai ba da horaswa domin su ci gaba da aiki tare, kuma su gayyaci ƙarin matasa domin tsara mujalladi na biyu na mujallar wanda zai fito a farkon 2020.