Kafin ku fara aikinku, ku yi la'akari da tambayoyin da ke ƙasa:

1
Details
A TUNANINA ME TSATTSAURAN RA'AYIN RIKICI KE NUFI?

Wannan sashe zai yi bayani game da keɓantattun ƙalubale da suka shafi ba da ma'anar VE sannan zai yi ƙarin haske game da amfanin ƙwanƙwance VE a matakin fahimtarku. 

2
Details
WAƊANNE HAƊURRA KE DA AKWAI SANNAN TA YAYA ZA MU IYA AMFANI DA ILIMIN FAHIMTAR RIKICI?

Wannan sashe zai yi bayani a kan "ilimin fahimtar rikici" da kuma dalilin da ya sa amfani da ilimin fahimtar rikici a dukkannin matakan P/CVE yayin gudanar da shiri ke da amfani.

Title
3

SHIN MANUFARMU ITA CE HANA AUKUWA KO MAGANCE TSATTSAURAN RA'AYIN RIKICI?

USAID da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka sun bayyana yunƙurin hana aukuwa ko mangance tsattsauran ra'ayin rikici (P/CVE) a matsayin: "yunƙurin tagaza wani abu domin fuskantar ƙoƙarin masu tsattsauran ra'ayin rikici na cusa ra'ayin, ɗaukar mambobi, da jawo mabiya domin shiga rikici, tare kuma da shawo kan waɗansu al'amura da ke taimaka wa wajen samun sababbin masu tsattsauran ra'ayi da kuma cusa ra'ayin rikici. Wannan ya haɗa da lalata dabarun da masu tsattsauran ra'ayin rikici ke amfani da shi wajen jawo hankalin sababbin mambobi da kuma gina sababbin ra'ayoyi da suka ci karo da su a cikin al'ummar da abin ya shafa domin rage haɗarin da ke tattare da cusa tsattsauran ra'ayi a mutane tare da cusa wa mutane ra'ayin rikici.” 

DUBA WANNAN A ƊAKIN KARATUNMU  
Magance Tsattsauran Ra'ayin Rikici (PVE) da kuma Fuskantar Tsattsauran Ra'ayin Rikici (CVE)

Bambanci tsakanin CVE da PVE na iya shafar yadda masu ba da tallafi ko ƙwararrun masu tsara hanyoyin ci gaba ke raba aikinsu. Duk da cewa sau da dama akan yi amfani da CVE da PVE a madadin juna, yanyoyin biyu suna da ɗan bambanci da juna musamman yayin da aka bar matakin rubutu kawai aka koma matakin aiwatarwa. Taswirar da ke ƙasa, wanda ke nuni da tsarin P/CVE a fahimtar masu ba da tallafi daban-daban, na ɗauke da muhimman bayanan da ke nuna ta yadda waɗannan hanyoyi za su iya kasancewa sun bambanta. Nau'ukan mutanen da kuka so ku sanya a cikin shirinku zai yi tasiri a kan tsarin shirin naku. Yanayi, sakamako, da haɗurran da ke da alaƙa da waɗannan matakan sa hannu za suka kasance masu bambanci matuƙa.

 

Sannan akwai muhimmin bambanci tsakanin tunkarar ta'addanci (CT) da tunkarar tsattsauran ra'ayin rikici (CVE). Duba taswirar da ke ƙasa.

 

TUNKARAR TA'ADDANCI (CT)

Huɓɓasa domin taƙaitawa, dannewa, da bibiyar al'amarin 'yan ta'adda da ayyukan ta'addanci.

Da kuma (VS)

Vs

TUNKARAR TSATTSAURAN RA'AYIN RIKICI (CVE)

Huɓɓasa domin hana ƙungiyoyin ta'addanci da ke wanzuwa samun sababbin shiga da kuma karɓuwa tare da faɗakar da al'ummar wurin da rikicin masu tsattsauran ra'ayi ke wanzuwa tare da neman taimako.

Kun shirya? To Mu Fara!

Zaɓi Rukuni domin farawa.