Aiwatar da Shiri

Yadda ƙungiya ke ƙaddamarwa da aiwatar da kowane nau'in shiri ya danganta da kayan aikinta, ƙarfinta, matakan cikin gida, da kuma sau da dama ƙa'idojin mai ba da tallafi da ya zama dole ta bi. Sai dai kuma, ya kamata koyaushe aiwatarwa ya fara daga matakin tsawara, wanda a lokacin ne ƙungiya za ta tanadi kayan aikin da ake buƙata domin tabbatar da gudanuwar shirin cikin nasara tare da aiwatar da ayyuka yadda ya kamata. Shirin ya ƙunshi tattara muhimman takardun shiri, kamar su tsarin aiki da kasafin kuɗi, ko cike muhimman matakan gudanarwa, kamar su ɗaukar hayar ma'aikatan da suka dace da samar musu da ofisoshi.

DABARUN AIWATARWA

SHIN KUNA SO KU SAMU ƘARIN BAYANAI GAME DA YADDA AKE GUDANAR DA SHIRI DA AIWATAR DA SHI?

Ku duba NGOConnect, kafar intanet wanda ake gudanar da ita a ƙarƙashin kulawar shirin Ƙarfafa Fararen Hula a Faɗin Duniya na FHI 360 domin raba kayan aiki da ilimi a cikin al'ummar CSO. Kafar na ƙunshe da kayan aiki game da gudanar da shiri, gudanar da harkokin kuɗaɗe, shugabanci, ma'aikata, sanya ido da aunawa, cigaban kowa, da sauransu.

Matakan aiwatar da shirye-shiryen P/CVE suna da ƙa'idojin da ke kama da na shirye-shiryen da ke waɗansu ɓangarori na daban. Sai dai kuma, la'akari da yanayin wannan shirin, matakin shiri da na ƙaddamarwa zai iya kasancewa ya fi yawa tare da cin lokaci sama da sauran nau'ukan shirye-shirye. A misali, shirin P/CVE na iya buƙatar bincike kan haɗari sosai da ƙarin lokaci da ƙoƙri domin neman haɗin kan mahukunta da tsarin sadarwa, yayin da aka yi la'akari da ayyukan a cikin waɗansu al'ummu.

Yayin da kuke shirye-shiryen aiwatar da aikin P/CVE ɗinku, ku yi la'akari da matakan da ke biye:

  • Ku gudanar da nazarin ƙarfin ikon aiwatarwa (game da ƙungiyarku, rukuninku, da/ko abokan haɗin guiwarku) domin gano giɓi ko buƙatun da ya kamata a yi aiki a kansu yayin aiwatarwa. An kawo ƙarin bayani game da auna-kai na ƙarfin ikon aiwatarwa a shafin Ɗorewa.
  • Samar da tsarin aiki domin samun damar tsarawa da shirya ayyuka na duk tsawon shirin. Da zarar an samar da daftarin tsarin aikin, to za ku iya shirya zangon ingantawa domin gabatar da tsarin aikin tare da gabatar ƙudurin shirye-shirye ga abokan haɗin guiwa da/ko masu cin gajiyar lamarin domin jan ra'ayinsu.
  • Ku samar ko ku kammala nau'in farko na bayanan jagoranci, waɗanda da yawansu za a fara ne a matakan Samu da Tsarawa. Wannan kundi na iya ƙunsar abubuwan da ke ƙasa (a duba Sashen Haɗi domin samun ƙarin bayani):
  • A kammala tsara Sanya ido, Aunawa, da Koyo.
  • A kammala tsara yanayin gudanar da shiri domin tabbatar da shirya ayyuka da samar da sakamako daidai da tsarin aikin.

 

Title
Salon Gudanarwa na Adaftib

Bincike da kuma ilimin FHI 360 game da aiwatar da shiri sun nuna muhimmancin amfani da salon gudanarwa na adaftib, a maimakon hanyoyin gudanarwa wanda ƙungiyoyi suka fi amfani da su. Salon gudanarwar adaftib ya ƙunshi sanya ido, da tara tsokacin mutane a lokacin aiwatar da shiri. Abu mafi muhammanci kuma kuma shi ne, tsarin ya haɗa da samar da sauye-sauye ta la'akari da wannan koyo. Ɓangaren Modul Ɗin Koyo ya kawo ƙarin bayani game tsarom da salon gudanarwa na adaftib da na koyo da kuma ɗaukar hannu daga shirye-shiryen P/CVE.