Daidaiton Jinsi da Damawa da Kowa (GESI)

Title
Gabatarwa

Al'ummun duniya sun ƙunshi rukunonin mutane daban-daban, waɗanda dukkanninsu na da buƙatu daban-daban, kadarori, damarmaki, da ƙalubale. Hanyar tabbatar da cewa an fahimci wannan al'umma mai jama'a mabambanta sannan an ba su kulawa shi ne ta hanar sanyo batutuwa Daidaiton Jinsi da Damawa da Kowa (GESI) a cikin shirye-shiryen P/CVE. Majalisar Ɗinkin Duniya na ci gaba da jaddadawa game da amfanin GESI a yayin shirye-shiryenta na cigaba; Manufofin Cigaba Masu Ɗorewa, wanda kai tsaye yake taɓo lamuran daidaiton jinsi, ƙarfafa mata, da damawa da kowa a matsayin abu mai muhimmanci kuma wanda babban manufarsa ita ce rage talauci da samar da duniya da ke ciki da ƙarin lafiya, aminci, tsabta, ilimi mai nagarta, da adalci da sauran abubuwa na gari.

A ƙasa za ku samu muhiamman bayanai game da GESI da yadda za ku sanya shi a cikin shirinku na P/CVE.

Title
Mene ne Daidaiton Jinsi da Damawa da Kowa?

MENE NE DAIDAITON JINSI?

"[D]aidaiton jinsi ya haɗa da aiki tare da ma yara da manya, mata yara da manya domin samar da sauye-sauye game da halaye da ɗabi'u, matsayi da ayyuka a gida, a wurin aiki, da kuma a cikin al'umma. Daidaiton jinsi ya wuce batun jerin dokoki a cikin littattafai kawai; ya shafi ba da 'yanci da inganta rayuwa baki ɗaya domin samun daidaito ba tare da tauye maza ko mata ba.” Tushe

MENE NE DAMAWA DA KOWA?

"Damawa da kowa na nufin inganta matsayin ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi domin su sanya hannu a cikin al'amuran al'umma da kuma matakin inganta ƙarfi, dama, da mutuncin waɗanda suke baya a ɓangaren tushensu domin ba su damar a shiga a dama da su a cikin al'umma.” Tushe

A ra'ayin Bankin Duniya, al'ummar da ke damawa da kowa dole ne su samu hukumomi, tsarin jagoranci, da matakan da ke ƙarfafa wa al'ummomi domin ya kasance za su iya tuhumar gwamnatinsu. Sannan yana buƙatar halartar dukkannin rukunonin mutane a cikin al'ummar, ciki har da rukunonin mutanen da al'ada ta ware su - kamar mata, matasa, tsofaffi, 'yan maɗigo, 'yan luraɗi, mata-maza, masu sauyin jinsi, da marasa jinsi (LGBTI), nakasassu, ƙabilu marasa rinjaye, da 'yan gida - a matakan yanke hukunci. Tushe 

MUHIMMAN HUKUNCI DOMIN HADA RA'AYIN GESI A CIKIN AYYUKAN P/CVE

Fahimtar sauye-sauyen GESI, musamman jinsi, na da muhimmanci domin fahimtar abubuwan da ke haifar da ɗabi'u da suka shafi tsattsauran ra'ayi tare da samar da ingantattun matakan magancewa. A ƙasa an kawo waɗansu muhimman abubuwan lura na GESI domin a yi la'akari da su yayin tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen P/CVE:

1
“.. kada a raya cewa mace ta kasance mafi haɗari ko rashin haɗari [sama da namiji], ko kuma wanda zaman lafiya zai yi tasiri a kanta, ko tattaunawa, ko kuma ta fi ba da goyon baya da rashin ta da hankali sama da namiji.”

Tushe

Maza da mata duk sun kasance daga cikin masu hannu a cikin ko waɗanda rikici ya shafa, sannan ya kamata shirye-shiryen P/CVE su yi la'akari da wannan.

Yawanci, akan kalli maza ne a matsayin masu ta da zaune tsaye mata kuma a matsayin marasa marasa laifi da ke cutuwa daga rikici da hatsaniya. Saidai kuma, an gudanar da bincike da yawa a shekarun baya waɗanda suka tabbatar da cewa wannan bugun 'yan kaɗanya bai kasance koyaushe gaskiya ba, a maimakon haka, dole ne a kalli maza da mata a matsayin masu hannu a ciki da kuma masu cutuwa daga shi.

2

Matsayin jinsi da al'adun zamantakewa da suka shafi abubuwan da yara mata/manya mata za su iya/ba za su iya aikatawa ba na iya taƙaita damar da suke da shi na halartar ayyukan shiri.

A cikin al'ummu da dama a faɗin duniya, ƙa'idojin al'ada da na addini na iya nuna matsayin mata manya da yara a cikin al'umma, da kuma nau'ukan hulɗayya da aka aminta da su a tsakanin maza da mata. Ya kamata a yi la'akari da waɗannan ƙa'idoji tare da nazartar yadda za a yi aiki tare da mata mahalarta game da ayyukan shiri. A misali, ayyukan da suka rataya a kan mata yara/manya a gida na iya hana su halartar gudanar da ayyukan shiri. Yawanci an fi ba wa ayyukan gida muhimmanci wanda hakan ke sa mata su rasa lokacin halartar gudanar da ayyukan shiri a wajen gida.

3

Ƙa'idojin zamantakewa da suka shafi mazantaka na iya yin tasiri a kan idan/kan yadda maza yara/manya ke ɗaukar da/ko ke halartar gudanar da ayyukan shiri.

Kamar yadda ƙa'idojin zamantakewa da na al'ada game da mata ke iya zama ƙalubale a fuskar aiki tare da mahalaita, haka ma ƙa'idojin da suka shafi mazantaka za su iya yi. A cikin al'ummun da ke ƙarƙashin jagorancin maza, ana kallon maza a matsayin ɓangaren iyalai da suka kanainaye komai. Su ne ke ɗaukar nauyin gida kuma su ke da alhakin ba da kariya ga mutuncin iyalansu. Saboda haka, kusan ƙalubalen iri guda ne yayin da aka nufaci aiki tare da mahalarta maza. Zai iya kasancewa ba su da lokaci sakamakon suna can wurin taimaka wa iyalansu ko suna gudanar da waɗansu ayyukan da suka shafi maza.

4
“... sakamakon tsohon tarihi da suke da shi da yadda aka yi riƙo da su, an tafi kan cewa ƙoƙarin ba da kariya da mata ke yi ko ƙungiyoyin mata suna da muhimmanci na musamman yayin ƙarfafa wa mutane guiwa a matakin al'umma.”

Tushe

Mata za su iya kasancewa manyan masu samar da sauyi da samar da zaman lafiya a cikin al'ummominsu sannan ya kamata a tuntuɓe su yayin tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen P/CVE.

Yayin da ya kasance sau da dama an fi raya cewa mata sun fi son zaman lafiya sama da maza, ba koyaushe ne hakan ke kasancewa gaskiya ba. Mata ma suna da rawar da suke takawa a matsayin masu samar da zaman lafiya sannan sau da dama suna da ƙarfi a cikin al'umma sannan za su iya samar da tasiri mai kyau a cikin al'ummominsu. A matsayinsu na matan aure, uwaye, 'yan uwa mata, masu ba da kulawa, jagororin al'umma, da sauransu, sau da dama mata na kan matsayin da za su iya gane alamun matsalar cusa tsttsauran ra'ayi a cikin iyalansu da sal'ummarsu, sannan abu mai muhimmanci, suna iya ɗaukar mataki. Sannan mana ta iya aiki a matsayin abun koyi ga waɗanda suke reno tare da gyara musu salon rayuwa da cusa musu haƙuri da zamantakewa na ƙwarai.

Kamar haka kuma, ƙungiyoyin mata na iya kasancewa mahukunta masu tasiri ga P/CVE. Bayan kasancewar waɗannan ƙungiyoyi suna da ilimi game da abubuwan da ke faruwa ga al'umma, suna kuma da hulɗayya mai kyau tsakaninsu da al'ummominsu sannan sukan taimaka wajen biyan buƙatun al'umma.

5
“Jinsi bai kasance saniyar ware a cikins auran abubuwan da suka shafi zamantakewa ba. Ya kamata a dubi al'amarin jinsi a cikin shirin buƙatun PVE da idon basira sannan tare da sauran al'amura kamar shekara, ƙwari/naƙasu, rukuni, muhalli, da abin da ya shafi aure ko rashin aure.”

Tushe

Jinsi Ya Fi Hankalin Mata Kawai

A ra'ayin UNDP da Cibiyar Faɗakarwa, ta Ƙasa-da-Ƙasa, "Mafi yawan taƙaddamar jinsi a shirin PVE sun mayar da hankali ne a kan matsayin mata da halartarsu cikin PVE." Sai dai kuma, "Zai fi dacewa a ɗauki jinsi a matsayin abin nazari wanda ya haɗa da dukkannin mutane: mata manya, yara mata, maza manya, yara maza, da waɗanda ba sa cikin wannan rukuni ko kuma suka karƙashin duka rukunonin biyu. A yi la'akari da yadda mata manya, maza manya, yara maza, yara mata, da sauran waɗanda ba sa ƙarƙashin rukunonin nan ke fuskantar rayuwa ta hanyoyi mabambanta wanda hakan ya danganta da, a misali, shekarunsu, tushensu, iliminsu na rayuwa, nakasa, ko matakin karatu.”

Title
Farawa: Yadda ake Haɗa GESI cikin Ayyukanku

Idan kuna mamakin yadda za ku fara haɗa ra'ayoyin GESI a cikin aikinku, fara da daidaitattun Jinsi da Haɗin Kan Jama'a na yaudara, wanda ya haɗa da bayanai don taimaka muku fahimtar bukatun GESI don aikinku da matakan farko da za ku ɗauka. Don ƙarin ƙayyadadden bayani game da yadda ake haɗa ra'ayoyin GESI cikin aikinku, da fatan za a tuntuɓi kowane nau'in tsarin aikin – Samun Dama, Tsara, Aiwatar, Duba & Auna, and Koyi. An jera ƙarin albarkatun GESI a ƙasa.

Title
doc
DAIDAITAR JINSINI DA DARUSSAYIN HADA JAMA'A