Sa Hannun Mahukunta

Tsarin VE abu ne mai ruɗani ɗauke da rukunoni daban-daban da ke da matsayi mabambanta game da shirin P/CVE. Matakin da kowane rukuni ya ɗauka na iya yin tasiri kai tsaye kan waɗansu mutane da rukunonin mutane, sannan sababbun al'amura na iya ɓullowa idan babu tsari tsakanin mahukuntan P/CVE daban-daban. Inganta haɗin kai da haɗin guiwa a tsakanin masu ruwa da tsaki ya zama wajibi a dukkannin matakan gudanar da shirin. Manyan mahukunta sun haɗa da duk wani mahukunci da ya mayar da hankali kan al'amarin, sannan na iya kasancewa jami'in gwamnati ko farar hula ko ya fito ne daga hukuma mai zaman kanta, da sauransu. Ga ƙungiyoyin da suke tsara shirin P/CVE, taimako da halartar al'ummar wurin da suka shirya gudanar da shirin - ciki har da mutane a cikin al'ummar da shuwagabanni - na da muhimmanci. Bugu da ƙari, za ku iya faɗaɗa manufofinku na P/CVE ta hanyar samun tallafi da sa hannun masu faɗa a ji da gwamnatoci domin yaƙar tsattsauran ra'ayin rikici sannan tare da bin hanyar rataya nauyi a kan gwamnati. A wannan ɓangaren mun mayar da hankali a kan matakan aiki tare da mahukunta da kuma abubuwan da ƙungiyarku za ta iya amfani da su domin shirye-shiryen P/CVE ɗinku.

Title
Mene ne Aiki Tare da Mahukunta?

Mahukunci na nufin dun wani mutum ko rukunin mutane ko ƙungiya waɗanda suke cikin al'umma sannan kai tsaye ko a kaikaice suka yi tasiri a kan ayyuka ko shiri da za a aiwatar. Mahukunta na iya yin tasiri mai kyau ko marar kyau a kan sakamakon aikin/shirin. Misalan masu ruwa da tsaki sun haɗa da: al'ummu ko ɗaiɗaikun mutane; gwamnatocin ƙasa da na ƙananan hukumomi; jiga-jigai a cikin fararen hula; ƙungiyoyi masu zaman kansu a matakin ƙaramar hukuma, yanki, ƙasa, ko ƙasa da ƙasa; da mutane 'yan ƙasa, shuwagabannin addinai, malamai, hukumomi masu zaman kansu, hukumomin UN, 'yan ƙasashen waje da ke ba da tallafi, da rukunonin al'umma da ke da ra'ayi na musamman.

DUBA WANNAN A ƊAKIN KARATUNMU

MAHUKUNTA DA ZA A IYA AIKI TARE DA SU YAYIN GUDANAR DA SHIRIN P/CVE KO FASAHA

 

Fararen Hula Gwamnati Sashin Masu zaman kansu
  • Ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs)
  • Kwamitoci (ciki har da na matasa da na mata)
  • Ƙungiyoyin bunƙasa al'umma da taimako
  • Ɓangaren ilimi
  • Shuwagabannin al'umma da shuwagabannin addinai
  • Ƙungiyoyin al'umma (CBOs)
  • Ƙungiyoyin addinai (FBOs)
  • Kafafen sadarwar al'umma
  • Hukumomin gwamnati na ƙaramar hukuma, yankuna, da na ƙasa
  • Gwamnati mai nuna ƙabilanci
  • Doka da ba da tsaro
  • Hukumomi da shirye-shiryen da ƙasa ke tallafawa
  • Kafafen sadarwar da ke ƙarƙashin jagorancin gwamnati/al'umma
  • Hukumomin da ke gudanar da ayyuka
  • Cibiyoyin da ba na gwamnati ba da masu zaman kansu
  • Kananan- da matsakaita-masu kasuwanci na gida ko masana'antu,
  • Kamfanoni da dama da manyan kamfanoni na kasa baki daya,
  • Gine-gine masu zaman kansu
  • Kafofin yada labarai masu zaman kansu da masu zaman kansu
  • Kungiyoyin kwadago
  • Kungiyoyin wasanni

 

 

Title
Ƙa'idojin Aiki da Mahukunta

Ƙa'idojin aiki tare da aka kawo a ƙasa sun kasance dole ga nasarar duk wani aikin haɗin guiwa tare da mahukunta.

DUBA WANNAN A ƊAKIN KARATUNMU

Principles of engagement graphic

  • DAIDAITO: Ta la'akari da al'amarin da ke da akwai, ku yi ƙoƙarin tabbatar da cewa akwai daidaiton jinsi, ƙabila, yankuna, addinai, da sauransu a tsakanin mahukuntan. Sannan a girmama gudummuwa da matsayin mahukuntan baki ɗaya, sannan ya kamta dukkanninsu su kasance za su iya samun bayanai sannan a ba su damarmaki iri guda na bayyana damuwowinsu da ra'ayoyinsu.
  • SASSAUCI: Kasancewar kowane mahukunci abin tuhuma ne ga al'ummarsa, yana da kyau ku kasance masu sauƙi wajen bi da al'amura tare da la'akari da kowace damuwa ko ra'ayi - amma a cikin farfajiyar binciken ta ɓangaren manufa da maƙasudai.
  • SHIGAR DA KOWA: Ku yi ƙoƙarin aiki tare da dukkannin mutanen da wani al'amari ya shafa da mahukuntan da za su iya yin tasiri a kan wani al'amari. Ya kamata masu aiwatar da shiri su mayar da hankali sosai kan mahukuntan da ba su nuna ra'ayin shiga a dama da su a cikin shirin ba amma suna da muhimmanci wajen ci gabansa. Ku yi ƙoƙarin ganowa ko wani daga cikin mahukuntan yana buƙatar ƙarfafawa domin samun damar shiga a dama da su a cikin shirin, tare da tabbatar da cewa an ba su tallafin da ya dac.
  • KOYO: Mayar da hankali a kan koyo a duk tsawon lokacin gudanar da ayyukan mataki ne da zai tabbatar da ingancin shiri. Ya kamata mahukunta (ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi) su samu damar samun ƙwarewa a fannin gudanar fasaha da gudanar da ayyukan ƙungiya a dukkannin matakan aiwatar da shirin.
  • MALLAKA: Domin ganin cewa mahukunta sun mayar da hankali sosai ga shirin, akwai buƙatar a sanya su a dukkannin matakan aiwatar da shirin. Haɗin guiwa wajen ƙirƙira na ba wa mahukunta damar tarayya a haƙƙin mallaka tare da taron dangi wajen aiwatar da lamuransu.
  • BAYYANA GASKIYA: Ku yi ƙoƙarin ganin kun sanar da mahukunta duk halin da ake ciki game da kowane al'amari na shirin, ciki har da musanyen ilimummuka, harkokin haɗin kai, ba da rahoto, da sauransu. Sannan abu ne mai matuƙar amfani a tattauna tare da yaɗa bayanai yadda ya kamata zuwa ga ɗaukacin al'umma.
Title
doc
Yaya hanyar damawa da mai ruwa da tsaki take kama?