Me ya sa Koyo da Daidaitawa ke da Amfani?

Kamar yadda aka kammala a Modul Ɗin Samu, za ku iya fara shirinku ta hanyar tattara bayanai (misali, ta hanyar nazarin tsattsauran ra'ayin rikici ko nazarin haɗurra) domin su jagoranci shirinku da aiwatarwarku. Yayin da wannan ya kasance matakin farko da yake wajibi, yana kuma da muhimmanci a ci gaba da wannan koyo na duk tsawon wa'adin aiwatar da shirin sannan a yi kwaikwayo daga wani wuri idan ya zama dole domin tabbatar da cewa shirin ya kasance mai inganci da dacewa. Wannan gaskiya ne dangane da dukkannin ayyukan da ke kan cigaba, amma ya ma fi zamowa gaskiya game da shirye-shiryen da ke aiki kan tsattsauran ra'ayin rikici (VE). Yin kwaikwayo dole ne domin kula da al'amuran da suka shafi sauye-sauyen VE da rikici da kuma sarƙaƙiyar da yake da shi.

Al'amura masu sarƙaƙiya game da shirye-shiryen P/CVE sun kasu kashi biyu: sarƙaƙiyar al'amari da sarƙaƙiyar muhalli.

Sarƙaƙiyar al'amari 

Sarƙaƙiyar al'amari na nufin cewa al'amura sun shafi wani lamari guda ne yadda ba za a iya amfani da sakamakon a wani bagire na daban cikin sauƙi ba. Sannan yana nufin cewa al'amura sun karkasu da yawa; ɓngarorin ayyuka na haɗuwa da juna ta sigogin da ba a zato, wanda hakan ke sa ya kasance abu mai wahala a yi hasashen wani al'amari na iya yin tasiri a kan sakamako - wanda hakan ke nuna cewa akwai buƙatar sanya ido koyaushe.

Waɗanne al'amura ne ke haifar da sarƙaƙiyar tsattsauran ra'ayin rikici da kuma buƙatar da ke da akwai na shirye-shiryen P/CVE da su yi amfani da koyo da kwaikwayo?

  • Fitattu a cikin al'amuran VE na saurin sauya dabarunsu da salailan gudanar da lamuransu. Dole ne a ci gaba da gudanar da shiri amma haka zai yiwu ne kawai idan an samu tsarin sanya ido da nazarin sauye-sauyen VE.
  • Yayin da VE ke wanzuwa a wuraren da rikici ya shafa, to ana iya samun sauye-sauye da ba a tsammanta ba. Yin la'akari da sauye-sauye ga muhalli zai kasance abu ne mai amfani ga ƙananan ƙungiyoyi.
  • Yayin nazartar yadda al'amuran da ke faruwa a matakin ƙasa ko matakin hukuma ke da alƙa da na matakin ƙaramar hukuma, a wurin da za a iya gudanar da shirye-shirye da dama, abu ne mai wahala a fahimci yadda tsarin VE ɗin zai riƙa sauyawa. 
  • Ra'ayoyin gwamnati ma na iya sauyawa cikin gaggawa, sannan dole ne a bibiyi al'amuran dangantakar waɗannan ra'ayoyi da ayyukan VE kuma dole a fahimce su. 
  • Har yanzu P/CVE na matsayin sabon al'amari ne wanda kullum sababbin al'amura ke ɓullowa game da shi - musamman bayanai game da ayyukan da suka tabbata masu tasiri a muhallai mabambanta.

Daidaita daga: Tushe

Sarƙaƙiyar muhalli

Sarƙaƙiyar muhalli na iya yin tasiri a kan shiri ko da al'amarain a karan kansa ba mai sarƙaƙiya ba ne. Ko gudanar da aiki a kan "sauƙaƙan" matsaloli ma na buƙatar kwaikwayo daga waɗansu idan abin ya shafi ƙasashen da rikice-rikice ya shafa ko a lokutan da mutane ke buƙatar taimakon gaggawa.

Title
Ta Yaya Koyo da Kwaikwayo za su Iya Yin Tasiri Kan Shirye-Shiryen P/CVE? 

Koyo

Koyo na iya ɗaukar nau'o'i da yawa kuma kan biya bukatu iri daban-daban. Koyo ya haɗa da himma da ƙoƙarin ku wajen tattara bayanai da yin nazarin abubuwan da ake fuskanta, da ayyukan da ake aiwatarwa, da kuma yanayin da suke gudana, don samar da darussan da za ku iya amfani da su a cikin shirye-shiryen ku (“ Daidaitawa” yanki na Koyo).

Wannan daftarin na nuna mahimmancin karin ilimi domin inganta Daidaito a yayin da ake tsara shirye-shiryen ci gaba. Haka kuma yana bayyana nau'ikan koyo iri biyu da za ku iya aiwatarwa:

Koyo Sannu-Sannu

Gano ayyuka da ke da alaƙa da juna guda ɗaya ko sama da haka (a misali, mujallar da ke ƙarƙashin jagoranci matasa wanda ke taɓo al'amuran da suka shafi matasa da ke yaƙi da tsattsauran ra'ayin rikici a cikin al'ummarku) tare kuma da koyo a lokacin aiwatar da shiri domin samun cigaba da gano darrusan da aka koya. Abin da aka koya zai kai ga an samu sauye-sauye sannan an yi kwaikwayon waɗansu shirye-shirye yayin tsara ayyukan. A misali, shirin horaswa game da mujallar da ke ƙarƙashin kulawar matasa na iya bayyana cewa rediyo na iya kaiwa ga matasan da ake so ya kai gare su sama da sauran hanyoyi, wanda a bisa wannan, shirin na iya yanke hukuncin sanya wannan a cikin tsare-tsarensa.

Koyo na bai ɗaya

Ana aiwatar da shiri guda ko jerin shirye-shirye masu alaƙa da juna a lokaci guda (a misali, mujallar da ke ƙarƙashin kulawar matasa tare da wani aiki na daban domin samar da kulab-kulab na 'yan ƙasa a makarantu domin damawa da al'umma ga ta fuskokin da ba su shafi rikici ba) tare da gudanar da al'amura domin auna nasara da gano darrusan da aka koya. Ta hanyar bin matakai biyu a lokaci guda tare da nazartar sakamakon duka biyun, za ku iya fahimtar matakin da ya fi aiki yadda ya kamata sannan ku samar da sauye-sauyen da suka dace.

Dabarun Aiwatarwa

YI AMFANI DA NAU'IN KOYO NA SANNU-SANNU DA NA BAI ƊAYA

Kada ku kalli waɗannan nau'ukan koyo a matsayin masu zaman kansu ko masu bambanci da juna - suna bayani ne game da dabarun da za ku iya yin amfani da su domin bunƙasa hanyar koyonku. A aikace, za ku iya gudanar da ayyuka waɗanda suka shafi nau'in koyo na sannu-sannu da na bai ɗaya duk a lokaci guda.

DAIDAITAWA

Daidaitawa na nufin abin da kuke yi da bayanai da ƙididdigan da kuka tattara da kuma ilimin da kuka ƙaru da shi; yana kuma nufin ayyukan da za ku aiwatar sanadin abubuwan da kuka koya. A cewa Hukumar Sin Auna Mataki na nufin: Tsari Mai Armashi na Sanya Ido ga Shirye-Shiryen Taimako, yawanci dalilai uku ne ke sa shirye-shiryen cigaba su gudana yadda ya kamata. Mun bitar waɗannan dalilai domin sanyawa a shirye-shiryen P/CVE.

1
Details
Ƙungiyoyi na samun sababbin bayanai

A dun tsawon lokacin aiwatar da shiri, ƙungiyoyi na ci gaba da samun sababbin bayanai (waɗanda suka haɗa tun daga sakamakon aunawar da aka yi wa VE zuwa ga ra'ayoyin mambobin ƙungiya) wanda hakan ke sa a ƙara fahimtar muhallin da matsalolin. Sau da dama dangantakar da aka gina kan aminci na da matuƙar muhimmanci domin samun sababbin bayanai, musamman bayanan da suka shafi batutuwa masu nauyi kamar su VE. Ba dole ne abokan hulɗa da sauran manyan mahukunta su ba da ra'ayoyinsu na gaskiya ko bayanai ba har sai an amince sosai da mamban ƙungiyar. Wannan ne ya sa sau da dama bayanan da ake samu a lokacin tsara shirin ba cikakku ba ne.

2
Details
Sauye-sauyen waje da sauyi na muhalli

Yayin da ya kasance ba za a iya lissafo dukkannin sauye-sauye na waje da za su iya sanya ƙungiya da yi sauya salo ba, waɗannan sauye-sauye na iya haɗawa da samar da sabuwar hukuma da ta mayar da hankali kan P/CVE, sabuwar dokar yaƙi da ta'addanci na cikin gida ko na ƙasashen waje, sauyin gwamnati, lamuran da suka shafi tsaro ko ta'addanci ko waɗansu sauye-sauye ga muhallin da ke tasiri a kan matsalar, masu cin gajiyar shirin ko mahukunta, ko kuma ɗaukacin al'ummar.

3
Details
Ƙalubale da nasarori

An samar da tsarinku ne bisa ilimin da ake da shi game da bayanan da kuke da shi a wancan lokaci dangane da hanyar da ta fi dacewa ta cimma manufar P/CVE ɗinku. Fuskantar tangarɗa, kamar a ce mutane daga cikin al'umma sun ƙi shiga cikin shirin da ya mayar da hankali kan kare tsattsauran ra'ayin rikici, ba dole ne ya kasance abu marar kyau ba - hakan na iya samar da haske game da yadda ya kamata a tsara gudanar da ayyuka ko buƙatar samun amincewa wanda ke ƙara damar da ake da ita na samun sakamako mai kyau.

Dangane da wannan daftarin Sarrafa Daidaito, akwai nau'ikan Daidaitawa na mussanman guda biyu:

Daidaita dabaru

Daidaita dabaru na nufin samar da sauye-sauye ga ayyuka ta la'akari da sakamakon sanya ido da aka yi ko tsokaci da aka samu. Yawanci wannan nau'in daidaitawa yana mayar da hankali ne a kan bunƙasa shiri da nasarar aiwatarwa ko kuma ya mayar da hankali kan matakan janyo al'ummomi masu cin gajiyar shiri cikin tsararrun ayyukan.

Daidaita Matakai

Daidaita matakai na nufin shin gyare-gyare, da suka shafi koyo ko tsokaci da aka samar game da dacewar matakan da ake bi na aiwatar da shirin da tsararrun ayyuka. A misali, wannan na iya kasancewa ilimi da kan haifar da sauye-sauye game da sakamakon shirin, ƙarawa ko cire wani aiki, ko sauya rukunin mutanen da aka mayar da hankali kansu.

SALON GUDANARWA NA DAIDAITAWA

Salon gudanarwa na adaftib faffaɗan tsarin aiki ne da ya shafi koyo da ɗaukar hannu yayin gudanar da ayyukan cigaba. Ya haɗa da sanya ido, koyo, da tattara tsokaci yayin da kuke aiwatar da shiri. Bugu da ƙari, ya haɗa da samar da sauye-sauye da gyare-gyare ga shiri ta la'akari da ilimin da aka samu. USAID ta ba da ma'anar salon gudanarwa na adaftib a matsayin "salon da ake amfani da shi a matakin ƙasa-da-ƙasa domin hanke hukunci da samar da sauye-sauye sakamakon sabon bayani da sauye-sauye a bagire." A dalilin haka, salon gudanarwa na adaftib bai shafi sauya manufofi ba a yayin aiwatar da shiri; ya shafi sauya hanyar da ake amfani da ita domin cimma manufofin ta la'akari da sauye-sauyen da aka samu.

DUBA WANNAN A ƊAKIN KARATUNMU

Daga baya a cikin wannan tsarin za mu duba dalla-dalla game da tsarin USAID da sauran ƙungiyoyi don aiwatar da koyo da daidaitawa da tsarin gudanarwa na daidaitawa.