Haɗurra da Hasashe

Haɗurra da hasashe abubuwa ne na waje waɗanda shirin ba shi da tasiri sosai a kansu, amma kuma za su iya yin tasiri a kan ayyuka da sakamakon shiri. Sau da dama abubuwan na da alaƙa da ayyuka, batutuwa, da/ko imanin al'umma. Gano haɗurra da hasashe na taimaka wa ƙungiya wajen shirya wa ƙalubale da ka iya tasowa yayin da ake ƙoƙarin cimma manufar shirin da kuma fahimtar ko tsarin shiri na iya amfanarwa. A misali, idan hasashe ya nuna cewa al'umma ba za ta so karɓar shiri ba, zai iya zama dole a sake tsara shirin ko kuma da farko a sake ƙara waɗansu ayyuka da za su sa al'umma su goyi bayan shirin.

logframe4