Gabatarwa

Wannan modul ɗin na samar da jagoranci game da yadda za ku tsara shirin P/CVE ɗinku. 

Title
Maƙasudai

TSARA SHIRI ZAI TAIMAKI ƘUNGIYARKU...

  • Danganta bincikenku na VE da tsarin shirey-shirye da ayyukanku na P/CVE
  • Ku tsara shirinku domin tallafa wa rukunonin al'umma da VE ya yi tasiri a kansu ko waɗanda suke da raunin faɗawa cikin VEO
  • A yi shirin fuskantar ƙalubale la'akari da ilimin fahimtar shirin P/CVE
  • Amfani da ilimin fahimtar rikici da taƙaddamar jinsi domin tabbatar da cewa ba ku yi illa ga al'ummarku da shirinku ba
  • A samar da dabarun aiki tare da mutane daban-daban domin tsara ayyukan shirinku

WANNAN MODUL ƊIN ZAI TAIMAKA MUKU WAJEN...

  • A samar da haɗaka tsakanin auna VE da shirin P/CVE
  • Fahimtar yadda za a samar da Ra'in Sauyi na P/CVE da maƙasudan shiri, wanda zai yi tasiri ga dabarun sa ido da aunawa
  • Kiyaye samar da yiwuwar aukuwar haɗari yayin tsara ayyukanku
  • Nazartar dabaru da dama na amfani da ra'ayi daban-daban a tsarin aikinku
Title
Tambayoyin da za su Taimaka Yayin Tsara P/CVE Ɗin Shirinku

Da zarar kun kammala binciken VE ɗinku, to ku yi la'akari da waɗannan tambayoyi domin fara tsara P/CVE ɗin shirinku:

  • Mene ne Ra'in Sauyi na shirinku: misali, me ya sa/ta yaya kuke tunanin waɗansu abubuwan da za a aikata za su samar da sauyin da ake buƙata a muhallinku? Ku duba bayanai a shafi na gaba game da yadda za ku tsara Ra'in Sauyi.
  • Yaya ƙarfin ƙungiyarku ya kasance na samar da wannan sauyi?
  • Ta wace hanya shirinku zai yi la'akari da kowane jinsi da rukunin al'umma? Ba za mu iya raya cewa abin da ya yi daidai ga maza (yara maza) zai yi daidai a mata (yara mata) ba. Ya kamata manufofin shiri da kuma dabarun cimma manufofin su kasance an gudanar da su bisa ingantaccen bincike game da abin da maza da mata za su iya aikatawa.
  • Ta yaya za ku tabbatar da cewa shirinku Ba Zai Haifar da Illa ba?