Gabatarwa

A wannan gaɓar shirinku, kun fahimci manyan abubuwa da ke kawo tsattsauran ra'ayin rikici a muhallinku (ku duba Modul Ɗin Samu Modul Ɗin Samu domin samun bayanai da jagoranci) sannan kun yanke shawara game da tsarin shirinku (ku duba Design Module domin samun bayanai da jagoranci). Yanzu a shirye kuke da ku fara aiwatar da shirinku. Domin samun agaji game da wannan mataki, ku yi tunani game da manufofi da tambayoyin jagoranci da ke ƙasa:

Title
Maƙasudai
  • Ku fahimci manyan abubuwan lura yayin aiwatar da shirin P/CVE.
  • Ku nemi bayanai game da bayyanannun kayan aiki da za su taimaka wajen yin amfani da waɗannan muhimman matakan aiwatar da shiri. 
Title
Tambayoyin Jagoranci

Waɗannan tambayoyin jagoranci za su taimaka muku wajen yin nazari game da yadda ya dace ku aiwatar da P/CVE ɗinku.  

  • Ta yaya kuke aiki tare da rukunonin mahukunta yayin aiwatar da shirinku? 
  • Ta yaya kuke damawa da matasa kai tsare yayin aiwatar da shirinku?  
  • Ta yaya za ku tabbatar da cewa shirinku ya yi la'akari da jinsi sannan ya janyo rukunonin mutane da ke fuskantar wariya jiki?  
  • Ta yaya za ku tabbatar da cewa shirinku ba wai kawai "bai cutar ba," har ya ƙalubalanta tare da da daƙile sauye-sauyen rikici?  
  • Ta yaya kuke ganewa, fahimta, tare da yin shiri game da haɗurra a yayin aiwatar da shiri?  
  • Wane shiri kuka yi da zai sa sakamako ya zama mai ɗorewa yayin aiwatarwa, da kuma neman tallafi domin sakamakon ya ɗore har bayan kammala shirin?