Zaɓen Ayyukanku

Auna VE ɗinku da kuma Ra'in Sauyinku shi zai yi jagorancin zaɓen ayyukanku. Jadawalin da ke ƙasa ya kawo waɗansu daga cikin ɓangarorin aiki da za su taimaka wajen gano abubuwan da ke kawo VE. Wannan ne mafarin wurin da ya dace danganta ayyukanku da abubuwan da ke ingizawa da masu janyowa waɗanda kuka gano ta hanyar bincikenku na abubuwan da ke kawo VE.

Abu Abubuwan da ke Kawo VE Ayyukan P/CVE da za a Iya Nunawa
Muhalli Mai Kyau
  • Jihohi Masu Rauni 
  • Rashin ingancin tsaro da/ko cin hanci
  • Wuraren da ba a kulawa da su yadda ya dace ko ake matsa musu 
  • Ƙirƙirar ajendojin da suka shafi addini 
  • Rarrabe-rarraben kawuna na ciki da wajen addini 
  • Ɗaukar nauyin da jiha ke yi wa ƙungiyoyin da ke ta da rikici 
  • Horaswa ga jami'an tsaro ko jami'an gwamnati 
  • Tattaunawa tsakanin addini mabambanta da/ko tsakanin mabiya addini
Ingizawa
  • Dalilan Zamantakewa da Tattalin Arziki da ke Ingizawa, nuna wariya a cikin al'umma, nuna bambanci, takaici da tauye hakki
  • Lamuran da Suka Shafi Siyasa: tauye ‘yancin siyasa da damarmakin rayuwa, muzgunawar gwamnati da tauye ‘yancin ɗan’adam, harƙallolin ƙasar waje, mamayewar siyasa da/ko ta sojoji, rashin tuhumar waɗansu game da cin hanci da rashin hukunta masu hannu da shuni, rikicin cikin gida, gwamnati marar ƙima da muƙaman shari’a da ba su da mariƙa ko waɗanda ake aiki da su ta hanyoyin da ba su dace ba, tsoratarwa ko tilastawar VEOs, fahimtar cewa tsarin dokokin ƙasa-da-ƙasa ba shi da adalci sannan yana nuna ƙiyayya ga rukunin ƙabila ko addininsu
  • Al'adu da ke Tunzuwara: jin cewa addini ko ƙabilar mutum na fuskantar muzgunawa ko barazana da suka shafi al'adu da tadoji da kuma ƙima da mutuncin kai da na al'umma
  • Shirye-shiryen damawa da matasa da ƙarfafa musu
  • Damarmakin tattalin arziki ga matasa
  • Ilimi
  • Shigar da mata cikin al'amarin P/CVE
  • Inganta harkokin gwamnati/magance matsalolin gwamnati
  • Damawa da shuwagabannin addini a cikin harkar CVE
  • Faɗakarwar game da 'yancin 'yan Adam da shari'a
  • Cigaban al'umma da haƙurinta
  • Sa hannun mahukunta a cikin al'umma
  • Samar da dokoki a cikin al'umma
Janyowa
  • Jin cewa mutum na tare da al'umma
  • Kafa hujja da bayyana ɗabi'u masu kai wa ga rikici
  • Wanzuwar ƙungiyoyin VE da ke da wasu ra'ayoyi da manufofin masu jan hankali
  • Wanzuwar majalisu ko wuraren assasa tsattsauran ra'ayi
  • Cuɗanyar mutane da ƙungiyoyi masu tsauri
  • Samar da ayyuka (a matsayin matakin fuskantar buruka da buƙatu da ba a cimma ba)
  • Samun kayayyaki, kwaɗayi ko yaɗuwar badaƙalar tattalin arziki
  • Sanyo 'yan uwa tare da sauran masu faɗa-a-ji
  • Taimako da ya shafi ƙwaƙwalwa da zamantakewa da kuma farfaɗowa daga halin ruɗani 
  • Maganganu ko saƙonni masu ƙalubalanta ko ba da zaɓi
  • Gusar da tsattsauran ra'ayi  
  • Wani zaɓi na daban da kulle masu tsattsauran ra'ayi/FTFs  
  • Gyara FTFs  
  • Dawo da FTFs Cikin Al'umma
  • Sa Hannun ɗaiɗaikun mutane

 

Yayin da kuke zaɓar ayyukanku, yi la'akari: 

WACE DAMA ƘUNGIYARKU TAKE DA SHI NA AIWATAR DA AYYUKAN DA KUKA ZAƁA?  

Shin a yanzu haka kuna aiki ne a kan al'amari mai buƙatar ƙwarewa ko a wuri mai buƙatar ƙawarewa? Idan haka ne, shin za ku iya faɗaɗawa ko sauya ayyukanku domin fuskantar abubuwa ko mutanen da kuka gano? Idan ba haka ba ne, shin za ku iya faɗaɗa muhallin shirinku? Me za ku yi amfani da shi domin yin hakan? Damarmaki da iyakokin ƙungiyarku na iya nuna muhallin shirin da za ku iya gudanarwa. 

TA YAYA ZA KU IYA GAYYATO WAƊANSU MUTANE DOMIN FAƊAƊA TASIRIN AYYUKANKU? 

Ku yi tinani kan muhimman mahukunta da za ku gayyato da kuma yadda ya fi dacewa ku gina haɗin guiwa da sauran mutane, ƙungiyoyi, da neman haɗin kai domin faɗaɗawa ko samar da ƙarin ayyuka.    

TA YAYA ZA KU TABBATAR DA CEWA AYYUKANKU BA ZA SU HAIFAR DA ILLA BA?  

A duba Sashen Haɗi game da Ilimin Fahimtar Rikici domin samun tambayoyin da za a yi, takardar aikin da za a yi amfani da ita, game da yadda ya fi dacewa da ku gudanar da ayyukanku domin su kauce wa masu rabawa a cikin al'umma, sannan domin su samu damar ƙarfafa masu haɗawa.

Title
doc
NAZARIN TSARIN AYYUKA
photo
Details

Takardar nazarin tsarin ayyuka

Wannan takardar nazarin zai taimaka maku wajen tsara ayyukan ku.

Title
Tabbatar da Cewa ba ku Janyo Wata Illa ba

Da zarar kun kammala nazartar masu rabawa da masu haɗawarku, za ku iya yin amfani da tsarin aikin da ke ƙasa domin taimaka muku wajen danganta nazarinku da kuma tsarinku na ayyukan shiri.

Bayan kun ba da ƙarfi kan masu rabawa da masu haɗawa (ku duba aikin da ke ƙasa), za ku iya la'akari da zaɓuɓɓuka da damarmaki.

  • Ta yaya za a iya sauya waɗannan masu rabawa ko masu haɗawa? Ma'ana, waɗanne dabaru ne za su iya taimawa wajen rage/daƙushe waɗannan masu rabawa da kuma dabarun da za su ƙara/tallafa wa waɗannan masu haɗawa?
  • Me ƙungiyarku za ta iya yi domin a samu sakamako mai kyau? Me kuke aikatawa wanda yake da, ko zai iya haifar da matsala? Me ya sa matsalar ke aukuwa? Me za ku iya sauyawa domin yin tasiri a kan sakamakon? Fahimtar ayyuka da ɗabi'u na iya taimaka muku wajen tsara dabarun aiwatarwarku (an tattauna a ƙarƙashin Modul Ɗin Aiwatarwa).
  • Waɗanne zaɓuɓɓuka da damarmaki ne ke da alaƙa da manunan da kuka samar a Mataki na 2 a yayin auna Masu Rabawa da Masu Haɗawa a Modul Ɗin Samu?
  • Ta yaya za ku iya sa ido ga sauye-sauyen da shirinku ya haifar? Wannan zai taimaka wa dabarunku na sanya ido da aunawa (an tattauna a Modul ɗin Sanya Ido da Aunawa).
  • Idan ba a samu sauyi ba, shin kuna da wani zaɓi na daban? Shin kuna da hanyar fahimtar dalilin da ya sa sauyi bai samar da tasirin da kuke tsammani ba? Wannan zai taimaka wa tsarinku na koyo (an tattauna a ƙarƙashin Modul Ɗin Koyo).
Title
doc
NAZARIN TANTANCE RABE-RABE DA MAHAƊAI
photo
Details

Takardar nazarin tantance Rabe-rabe da MAHAƊAI

Wannan takardar zai taimaka a yayin gudanar da nazarin.