Mene ne wannan Bayanan Jagoranci?

Wannan kundin jagoranci na da manufar samar da kayayyaki da taimako ga ƙungiyoyin farar hula a faɗin duniya domin aiwatar da shiraruwansu da ke hani tare da magance tsattsauran ra'ayi da ke jawo rikici (P/CVE).

DON WA AKA YI SHI?

Wannan kundin jagoranci an tsara shi ne domin ƙananan ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da ke aiki a cikin al'umma, ko a wani yanki na ƙasa, ko a matakin ƙasa wanda aikin nasu ya shafi ƙoƙarin hani tare da magance tsattsauran ra'ayi da ke jawo rikici.

TA YAYA AKA TSARA SHI?

Bayanan da aka tattaro a cikin wannan kundin jagoranci sun kasance samfura ne na kundayen jagoranci da aka wallafa a baya waɗanda ke da manufar ba da jagoranci game da masu gudanar da P/CVE.

Wannan shi ne karon

farko gare ku?

Da ma Kun Raga da Kun Fara?

Barka da Dawowa!

Ku Zaɓi Rukuninku

YI RAJISTAR Zangon CVE Ɗin

A Zangon CVE akan kawo taƙaitattun saƙonnin da aka tura kafar Twitter bayan kowane sati wanda hakan na da manufar tattara sababbin rubuce-rubuce, ra'ayoyi, bincike, da kuma sababbin ilimummuka da ke da dangantaka da hani tare da magance tsattsauran ra'ayi da ke jawo rikici. Yi rajista a nan domin shiga tsarin Zangon CVE.