Gabatarwa

Wannan sashen na bayanin yadda za ku gudanar da tantancewa, gami da fahimtar maƙasudai da tambayoyin da za a gabatar. 

Title
Maƙasudai

Me ya sa auna tsattsauran ra'ayin rikici (VE) ke da amfani ga ƙungiyarku?

  • Don taimakawa hana VE ta hanyar haɓaka fahimtar abubuwan da ke ba da gudummawa ga tsattsauran ra'ayi  
  • Don sanar da ƙirar ayyukan da aka yi niyya don hanawa ko magance VE

ME WANNAN MODUL ZAI TAIMAKA MUKU KU CIMMA?

  • Ku gano muhimman matakai da tambayoyi na aunawar 
  • A samar da haɗaka tsakanin auna VE da shirin VE 
  • A fahimci yanayin tasirin wariya da ilimin da ake da shi game da abubuwan da suka auku a baya game da sauye-sauyen VE da abubuwan da ke haddasawa da kuma abubuwan da suka shafi juriya 

TA YAYA ZA MU IYA RAGE SON KAI TARE DA FAHIMTAR ƁANGARORIN SAUNIN TUNANI GAME DA ƘWANƘWANCE VE?

  • A gano abin da ke ƙarfafa mana guiwa domin mu aiwatar da wannan aunawa 
  • A bayyana matakan ƙwanƙwancewa da ake buƙata (ƙasa, al'umma, mutum, da sauransu) 
  • Gano yadda tushenmu ke yin tasiri a kan ƙwanƙwancewar da muke yi ta hanyar tambayar kanmu cewa: mene ne muhamman hasashenmu, sannan shin an auna su? 
  • A gano idan tushenmu na sa mu fahimci wani abu baibai. Shin waɗannan ra'ayoyi ne da ya kamata a yi la'akari da su?  
  • Ku gano idan za ku iya rage illar da za a iya samu game da hanyar da muke bi domin aunawa 
Title
Tambayoyin Jagoranci Domin Auna VE Ɗinku
GABATARWA GAME DA AUNAWA

Da zarar kun ba da ma'anar tsattsauran ra'ayin rikici (VE) a muhallinku, a ƙasa ga nan waɗansu tambayoyin da za ku iya fara gwajinku da su. Wannan modul ɗin ya mayar da hankali ne kan taimaka wa tawagar da ke tsara shirinku wajen fahimtar sauye-sauye da abubuwan da ke janyo tsattsauran ra'ayin rikici da fitina, tare da dangantakar da ke tsakaninsu, domin taimaku wajen tsara shirinku.  Sauye-sauyen VE na tasirantuwa daga alaƙar da ke tsakanin ƙananan matsaloli da juriya, da kuma ja-gaba da ke shirya mutane da kayan aiki domin ƙoƙrin cimma manufofin da suka shafi zamantakewa, siyasa, ko tattalin arziki ta amfani da nau'in rikicin da aka yi amfani da ra'ayi wajen nuna yana kan daidai. Abubuwan da ke janyo VE sun kasance abubuwa ne da ka iya taimaka wa VE (da aka sani da "abubuwan da ke turawa”) da kuma waɗanda ke yin tasiri a kan cusa tsattsauran ra'ayi ko janyo ɗaiɗaikun mutane (wanda aka sani da "abubuwan da ke jawowa”).  Gano rauni da abubuwan da ke haddasa bin tafarkin ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin riciki (VEO) na taimakawa wajen gano haɗurra tare da gano waɗanne tsare-tsare da manyan abubuwa ne za su iya yin tasiri a kan sauye-sauyen VE.

Wannan modul ɗin ba zai mayar da hankali ba kan auna tushe na sa ido da aunawa, wanda za a iya samu a cikin  modul ɗin Sa Ido da Aunawa.

Gano mutanen da ke da rauni
  • Waɗanne mutane ne suka kasance mafiya raunin a cusa musu tsattsauran ra'ayi da/ko a ja su zuwa cikin masu tsattsauran ra'ayi a wurin da kuke gudanar da shirinku?
  • Shin akwai abubuwan da ke yin tasiri a kan janyo mutane cikin ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin rikici (VEO) (misali, sheka, jinsi, zama a wani wuri, matakin karatu, matsayin zamantakewa da tattalin arziki, ƙabila da addini)?
Fahimtar Abubuwan da ke Ƙarfafa Guiwa
  • Waɗanne abubuwa ne ke haddasa husuma da kasancewa tushen rashin zaman lafiya (abubuwan da ke turawa) da za su iya yin tasiri kan raunin VE?
  • Waɗane abubuwa da ke jawowa za su ƙarfafa guiwar ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi domin shiga cikin riciki (sakamakon abubuwan sun tunzura su)?
    • Ta wace fuska waɗannan abubuwa ke bambanta a tsakanin maza da mata, (yara maza da yara mata)?
    • Ta yaya jinsi ke yin tasiri a kan hanyar cusa wa mutane tsattsauran ra'ayi?
  • Waɗanne ne daga cikin waɗannan abubuwa suka fi dacewa da muhallin aiwatar da shirinku?
  • Waɗanne sauye-sauyen alaƙa da na ƙungiya ne ke taimaka wa VE?
  • Waɗanne muhimman abubuwa ne da suka shafi gwamnatoci da abubuwan da ake gudanarwa da dokoki waɗanda za su iya yin tasiri a kan raunin faɗawa cikin VE?
Fahimtar ayyuka da jawo mutane zuwa cikin VEO
  • A waɗanne wurare ne mutane ke faɗawa cikin wane nau'in VEO? Yaya tsarin VEO ɗin yake sannan ta yaya suke gudanar da al'amuransu (tsarawa, samar da kuɗaɗen shiga, sadarwa, da sauransu)?
  • Me aka fahimta game da wuri da yanayin janyo mutane cikin tafiyar wanda yanzu haka yake faruwa?
  • Su wane ne jiga-jigai a cikin tafiyar waɗanda ke janyo mutane da cusa musu tsattsauran ra'ayi?
  • Waɗanne ne alamomi ko siffofin zahiri ko waɗanda aka tsammanta na VEO da ke da tasiri a muhallin aiwatar da shirinku da kuma ke iya taimakawa wajen jawo mutane?
Fahimtar sauye-sauye da suka shafi VE
  • Shin illar VE na raguwa ne ko ƙaruwa a muhallin da abin ya shafa, sannan shin illar na sauyawa ta fuskar yanayi, muhalli, da dabarun da ake amfani da su?
  • Waɗanne muhimman abubuwa ne na cikin gida da na waje za su iya yin tasiri a kan raunin faɗawa cikin VE a muhallin da ake gudanar da nazarin?
  • Waɗanne sauran sauye-sauye ne ake samu a waɗansu muhallai - waɗanda ke da nasaba da rikici, daidaiton jinsi, damawa da dukkannin ɓangarorin mutane, da sauransu - ne za su iya yin tasiri a kan raunin bin tafiyar VE?  Ta yaya VEO suke ko za su iya amfani da wadannan sauye-sauye a muhallin da suke gudanar da ayyuka domin cimma manufofinsu?
Muhallin CVE da abubuwan da ke kawo rauni
  • Shin akwai dokoki da matakan gwamnati da game da CVE?
  • Shin gwamnatin ƙasa za ta haɗa kai da shirinmu game da wannan al'amari?
  • Shin shuwagabannin gwamnatin ƙaramar hukuma/yanki za su so haɗa kai da shirinmu game da wannan al'amari? Shin suna kallon tsattsauran ra'ayi a matsayin matsala, sannan shin suna kallon cewa farar hula na da rawar takawa wajen shawo kan al'amarin?
  • Shin ƙungiya kamar tamu za ta fuskanci matsalolin tsaro yayin aiki kai tsaye da ya shafi matsalolin tsattsauran ra'ayin rikici?
  • Waɗanne abubuwa ne (mutani, ƙungiyoyi, al'adu, tsarin imani, da sauransu.) za su iya amfani wajen hanawa, ragewa, da kassara VE a cikin waɗansu al'ummu?
  • Su wane ne muhimman masu tasiri (mai kyau ko marar kyau) game da sha'anin yaƙa da magance tsattsauran ra'ayin rikici a bagiren da ake gudanar da shiri?
  • Waɗanne darrusan da aka ɗauka daga CVE da ya gabata da wanda ke ci a yanzu ne za su iya taimakawa wajen tsara CVE a nan gaba?

DABARUN AIWATARWA

Sau da dama aiwatarwa da aunawa na ɗaukar haɗurra iri guda ne da na aiwatar da shiri. Saboda haka, yayin tunani game da aunawa, yana da muhimmanci a:

  • Yi nazari game da haɗurrar da za su iya shafarku sannan ku lura da rikici da ka iya faruwa domin kada ku jefa kanku ko masu halarta cikin matsala. Ku samu ƙarin bayani a Sashen Haɗi game da Ilimin Fahimtar Rikici.
  • Ku gano hasashenku domin ku kasance masu faɗin gaskiya yayin gabatar da ƙwanƙwancewarku.

VE da rikici na da nau'ukan tasirori mabambanta a kan mutane Saboda haka, yana da kyau a yi nazari game da matakan damawa da mahukunta domin aikinku ya ƙunshi ra'ayoyi da sa hannun mutane mabambanta. Kafin aunawa, ku yi tunani game da:

  • Ta yadda za a dama da matasa yadda ya kamata. A lokuta da dama, matasa ne rukunin da shirye-shiyen P/CVE ke hanƙoro. Kasancewar suna kowane mataki na aiwatar da shirin abu ne mai muhimmanci, amma yana cike da ƙalubale. Tsarin aikin Cigaba Mai Kyau na Matasa (PYD) na samar da muhimman shawarwari game da matakai da aiwatarwa. Ku samu ƙarin bayani game da PYD a Sashen Haɗi game da Damawa da Matasa.
  • Ta yadda za a sanya nau'ukan fahimtar da aka yi wa jinsi. Tsarin aiwatar da bincike da aka kawo a cikin wannan modul ɗin zai taimaka muku wajen rarraba ƙwanƙwancewar da kuke yi ta lura da rukunonin mutane daban-daban, ciki har da maza da mata. Sashen Haɗi game da Damawa da Dukkannin Jinsi da Ɓangarorin Al'umma ma ya samar da matakai masu muhimmanci da dabarun aiwatarwa game da yadda za a iya samun haɗin guiwar rukunonin mutane daban-daba.