Magance Haɗari

MENE NE MATAKAN KULA DA HAƊARI?

Matakan kula da haɗurra tsari ne na lura da abubuwan da ka iya faruwa domin rage matsalar da za a iya samu ko asara tare da ƙara bin matakan samun damarmaki da nasarori. Manufar bin matakan kula da haɗurra shi ne "domin samar da hanya mafi dacewa ta gudanar da aiki bisa tabbacin cin nasara ta hanyar samu, fahimta, yanke hukunci, da ba da rahoto game da haɗurra. Matakan kula da haɗari ya kasance hanyar da ke ba da dama: komabayan samun matsala game da hukuncin da aka yanke wanda ka iya haifar da dakatarwar shiri. Ingantaccen matakin kula da haɗari na samar da yanayin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da shirin, sannan da nasarar shirin. Ku duba kayan aiki a ƙasa. 

MENENE HADARA A CIKIN SHIRIN AIKI?

Ƙungiyar Samar da Inganci ta Ƙasa-da-Ƙasa (ISO)  ta ba da ma'anar haɗari a matsayin “tasirin rashin tabbas a kan maƙasudai.” Tasirin na iya kasancewa wanda ake so (samar da alfanu/dama) ko wanda ba a so (zamowa barazana, lalatawa). Haka kuma, haɗari ya haɗa da kaucewa daga kan abin da ake tsammani. 

ME YA SA KULA DA HAƊARI KE DA MUHIMMANCI GA SHIRYE-SHIRYEN P/CVE?

Akwai haɗurra tattare da aiwatar da kowane shirin P/CVE. Saboda haka, ku yi tunani game da amfani da hanyar ganowa da ɗaukar mataki game da haɗurra na duk tsawon lokacin aiwatar da shiri. 

DUBA WANNAN A ƊAKIN KARATUNMU

SIFFOFI BIYU NA MUHALLIN P/CVE DA SUKA ZAMAR DA LURA DA HAƊARI ABU MAI AMFANI

Tsammanin tasiri mai kyau ko marar kyau na da yawa.

Idan ba a gano haɗurra da ka iya faruwa game da shirin P/CVE sannan aka shirya musu ba, to za a samu yiwuwar aukuwar illa ga mutane, al'umma, da ƙungiyar. A ɓangaren guda kuwa, idan muka gano sannan muka ɗauki mataki game da haɗurra domin taimakawa wajen bunƙasa aiki, inganci, mutane da al'ummu da suke cikin shirin P/CVE na iya zamowa mai jure wa faɗawa VE a cikin al'ummarsu.

Akwai yiwuwar aikuwar matsala yayin da kuke aiki game da P/CVE.

Yayin da kuke aiki a wuraren da rikici ya shafa ko a wuraren da ke cikin haɗarin faɗawa VE, to zai kasance kuna aiki ne game da lamuran da sau da dama ake musu mummunan fahimta, lamura masu ruɗani. Wannan na haifar da haɗurra da suka shafi mutuncin ƙungiyar da kuma tsaron ma'aikatanta. Bayan haka, kasancewar P/CVE sabon fage ne, ana kan gudanar da muhawarori sannan akwai harshen damo game da muhimman ma'anoni, abubuwan da ke haifar da VE, sannan da abubuwan da ke amfani ko rashin amfani yayin da ake aiwatar da shirin P/CVE.

Yayin da kuke ganowa da ƙoƙarin magance haɗari yayin gudanar da shirin P/CVE, to kuna rage yiwuwar samuwar sakamako marar kyau tare da inganta hanyoyin aiwatar da shirin yadda ya kamata tare da sakamako mai kyau na shirinku, a yayin da kuma kuke kare al'ummarku da masu cin gajiyar shirin da tawaga da kuma ƙungiya.

Yayin da ya kasance salon lura da haɗari ya na kowane shiri na iya bambanta da na wani shiri na daban, salailan yawanci sun haɗa da matakan da aka zayyano a jadawalin da ke ƙasa.

MATAKI NA 1

Gano haɗari

Sau da dama za ku gano "rukunonin haɗari" ne domin tabbatar da cewa kuna mayar da hankali kan ɓangarori ko matakan shirin daban-daban. Waɗannan rukunoni na iya haɗawa da: haɗurra da suka shafi gudanarrwa; haɗurra da suka shafi muhalli; haɗurra da suka shafi tsaro; haɗurra da suka shafi shugabanci; da haɗurra da suka shafi shiri.

MATAKI NA 2

Auna haɗari

Ga duk wani haɗari da aka gano, a amsa manyan tambayoyi guda biyu:

  • Yaya mizanin yiwuwa/tsammani da ake yi cewa haɗarin zai auku?
  • Wane tasiri wannan haɗari zai yi a kan shirinku?

Ta hanyar amfani da wannan bayani, tawagarku na iya sanya maki ko matsayi ta amfani da lambobi (kaɗan, tsaka-tsaki, mai yawa) game da yiwuwa/tsammani da tasirin haɗarin da ake zaton aukuwarsa. Yawanci akan gabatar da sakamakon wannan aunawa ne a cikin sigar bayanan haɗari wanda ke ɗauke da bayanan abubuwan da ake tsammanta da kuma na tasiri a ɓangarori daban-daban, domin nuna haɗurran da suka fi dacewa a mayar da hankali a kansu.

MATAKI NA 3

Tsara hanyar magancewa

Samar da tsari game da yadda za ku magance waɗannan haɗurra. A lokuta da dama, ba za a iya kawar da haɗurra kwata-kwata ba, sannan ya kamata matakan magancewa su gano yadda za a magance waɗannan haɗurra. Amsoshi da za a iya samu yawanci sun haɗa da waɗannan matakai:

  1. Rage haɗurra ta hanyar ɗaukar matakan rage yiwuwa/tsammani da ake yi na aukuwar haɗari ko tasirinsa ga shirinku
  2. Tura haɗarin zuwa waɗansu mutane ko ƙungiya ta daban, misali turawa zuwa mai samar da inshora
  3. Yin haƙuri da haɗarin ta hanyar yanke hukuncin cewa da wuya haɗarin ya auku ko kuma tasirin da yake da shi ba shi da yawa wanda hakan ya sa ba dole ne a yi wani abu game da shi ba
  4. Guje wa haɗarin ta hanyar ƙin aikata aikin da zai harfar da shi tun farko

An samo wannan jadawali ne daga bayanan kula da haɗari wanda aka samar a Ƙa'idojin Gudanarwa da suka shafi shiryawa da aiwatar da ayyukan EU da aka ɗauki nauyinsu waɗanda suka keɓanta ga magance ta'addanci da tsattsauran ra'ayin rikici a waɗansu ƙasashe.

Akwai tsarin aiki da bayanai da dama da za ku iya samu waɗanda za su taimaka muku wajen gudanar da shirinku. Shirye-Shiryen UNDP na Kauce wa Haɗari da ya Shafi Magance Matsalar Tsattsauran Ra'ayi (PVE) Kundin Bayanan Jagoranci ga Masu Gudanarwa ya yi bayani game da muhimman matakai guda biyar (duba jadawalin da ke ƙasa) da suka shafi amfani da matakan kula da haɗari domin shirinku na P/CVE. Ku danna kan wannan fayil ɗin samun bayanan gaggawa wanda ya taƙaita matakan kula da haɗari guda biyar na UNDP.

 

riskmanagement

Duba wannan misalign daga Rajistar Haɗari wanda aka aro daga Jagorar da UNDP ta ruwaito. Wannan Rajistar Haɗarin zai taimaka muku tsara shirye-shiryen ku ta fuskatar haɗarorin da aka gano. 

Title
doc
Ƙarin Albarkatu
photo
Details

Sarrafa Matsalar Tsaro: Taƙaitaccen Jagora domin Ƙananan Ƙungiyoyin Sa-kai

Kuna bukatar ƙarin ilimi game da sarrafa haɗarin tsaro? Wannan jagorar ta zayyana takaitaccen bayanai tsarin kula da haɗarin tsaro wanda zai iya taimaka wa ƙananan ƙungiyoyin sa-kai don haɓaka mahimman matakai da ayyuka waɗanda za su inganta tsarin ma'aikatansu da haɓaka suna da amincin ƙungiyar su. Littafin ya ƙunshi jagora, ƙarin bayanai, da samfura waɗanda ƙungiyar ku za ta iya amfani su. 

photo
Details

Shawarwari don Amfani da kundin Bayanai na USAID

Kuna bukatar sanin haɗarin da ke tattare d a bayanai da kuma yadda zaku sarrafa bayanan da ayyukan ku ke tattarawa da samarwa? Wannan kundin na gabatar da tsarin da za a iya ganowa da fahimtar haɗaorin da ke tare da tattara tabayanai. Kundin na nuna mahimman abubuwan da za ayi la’akari da su kuma yana ba da shawarwari don taimakawa waɗanda ke amfani da bayanai don haɓbaka aiki a yayin da kuma suke sarrafa haɗari.  

KULA DA HAƊARI KO ILIMIN FAHIMTAR RIKICI WANNE ZA MU RIƘA AIWATARWA?

Amsar a taƙaice ita ce: duka biyu! Sau da dama Kula da haɗari da kuma ilimin fahimtar rikici suna aiki ne a tare, sannan za ta iya yiwuwa waɗansu daga cikin tsare-tsaren aikin su kasance sun haɗa su duka biyun. A misali, tsarin UNDP na Kula da Haɗari da aka bayyana a sama ya haɗa da ilimin fahimtar rikici a matsayin wani muhimmin jigo. Ana buƙatar ilimin fahimtar rikici domin gudanar da al'amarin da ya shafi kula da rikici yadda ya kamata kasancewar yin illa, wanda sau da dama ake yi bisa rashin sani, na iya haifar da haɗari ga ƙungiyar, shirin, ko ma'aikatan kansu.

CDA sun samar da jerin tambayoyi da za su taimaka muku wajen sanya tsarin Kauce Wa Haɗari a cikin matakin nazarin haɗarinku da tsarin magance haɗari.

YAYA KAMANNIN HAƊURRAN P/CVE SUKE?

Haɗurra za su kasance suna da bambanci game da kowane shiri ta la'akari da bagire da kuma ƙungiyar da ke aiwatar da shirin. Ƙungiyoyi na iya gano rukunoni da/ko nau'ukan haɗari da za su yi jagorancin matakanta na lura da haɗari. Tsarin Lura da Haɗari na UNDP ya gano rukunoni uku na haɗurra da damarmaki - na bagire, na hukuma, da na gudanarwa.

contextualinteractions

Hukumar Tarayyar Turai ta gano rukunoni ko nau'ukan haɗari da aka zayyano a ƙasa: Na Kuɗi, Na Gudanarwa, Na Tsaro, Na Shari'a, Na Siyasa, Na Ƙima, da Na Shugabanci.

Wannan jerin ya kawo haɗurran da sauran shirye-shiryen P/CVE ko masu gudanar da shiri suka gano. Jerin abubuwan da aka kawo bai cika ba, amma zai iya taimaka wa ƙungiyarku domin nazartar rukunoni da nau'ukan haɗurra da za su iya shafar shirinku.