A wannan mataki a shirinku, kun:
- Fahimci muhimman abubuwa da suke haifar da tsattsauran ra'ayin rikici a muhallinku. A duba Modul Ɗin Bincike domin samun bayanai da jagoranci game da wannan gaɓa ta shirin.
- Ayyana tsarin shirinku, ciki har da matakan da za ku bi da kuma ayyukanku. A duba Modul Ɗin Tsarawa domin samun bayanai da jagoranci game da wannan gaɓa ta shirin.
- Fara gudanar da ayyuka. A duba Modul Ɗin Aiwatarwa domin samun bayanai da jagoranci game da wannan gaɓa ta shirin.
Ya kamata a yi la'akari da kayan aiki da shawarwarin da ke cikin wannan modul ɗin a cikin dukkannin moduloli uku da suka gabata domin ganin yadda za ku iya auna mizanin tasirin shirinku. A lokacin aiwatar da shiri, yana da kyau a sanya ido don ganin ko ayyukanku na taimakawa wajen cimma maƙasudanku da manufofinku. Tattara bayanan da suka dace domin nuna ko kuna samun cigaba. Ƙari a kan kasancewar sau da dama masu ba da tallafi na buƙatar ku ba da rahoton waɗannan bayanai, ilimin da kuka samu a lokacin aiwatarwa zai taimaka wa tawagarku domin yanke hukunci da ya dace tare da iya aiki bayan samuwar sababbin sauye-sauye.
WANNAN MODUL ƊIN ZAI TAIMAKA MUKU WAJEN:
- Zayyana sakamakon aikin da aka tsara (adadin abubuwan da aka samar, kayayyaki da ayyuka) da sakamako (kyakkyawan sakamakon shirinku)
- Fahimtar kayan aiki daban-daban da za su taimaka wajen tattara bayanai da tantancewa, ciki har da waɗanda suka fi amfani a muhallin P/CVE
- A sarrafa bayanai cikin taka-tsantsan ɗin fahimtar rikici
- Gano dabarun aunawa domin taimaka muku wajen samun sakamako da ake buƙata
Yayin aiwatar da shiri da ayyukan P/CVE, ya kamata ƙungiyoyi su yi amfani da matakan sanya ido da aunawa wanda zai samar da abubuwan da ke ƙasa:
- Tsattsauran ra'ayin rikici na aukuwa sosai sannan yana buƙatar sauyin matakai domin magance shi
- Tsattsauran ra'yin rikici abu ne da aka tsara sosai domin ya dace da kowane muhallin da abin ya shafa, saboda haka, abu ne mai wahala a samu ilimi da zai wadatar ga dukkannin sauye-sauyen da suka shafi ayyukan shiri
- Dole ne a gudanar da sanya ido da auna ayyuka (kamar su tattara bayanai) cikin tsarin kula da rikici
Yayin da kuka fara tsarawa da aiwatar da shirinku, ku yi tunani game da yadda za ku auna nasararku. Yayin shiryawa da aiwatar da tsarinku na sanya ido da aunawa, ku yi la'akari da waɗannan tambayoyi:
FASALI
- Me ya sa kuka zaɓi waɗannan ayyuka taƙamaimai?
- Waɗanne manufofi ne kuke son ayyukanku su cimma?
AIWATAR
- Shin shirinku na amfani da kuɗi da kayan aiki yadda ya kamata?
- Shin kun fuskanci wata matsala?
- Shin kun ga alamu nasara?
- Shin shirinku ya cimma abin da aka tsara shi domin ya cimma?
- Shin kuna yawaita sa ido kan ayyukan da ake ƙaddamarwa domin tabbatar da muhimmancinsu a wuraren da ake aiwatar da su?
- Shin ko Magadan ayyukan na cikin haɗari idan wasu sun sami sunayensu da amsoshin da suka bayar yayin tattara bayanai?
- Ta yaya kuke sarrafa sadar da mahimman bayanai?
KOYO
- Shin wani abu da ba ku tsara ba ya auku?
- Shin kun koyi wani darasin da ba ku tsammanta ba?
- Bisa ga abin da kuka koya, waɗanne gyare-gyare kuke bukatar yi ga ayyukanku?
Sanya ido da aunawa kalmomi ne da ake yawan ambato a tare amma ya kamata a fahimce su a matsayin batutuwa masu zaman kansu:
Sanya ido: Tattara bayanai a duk tsawon wa'adin aiwatar da shirin domin bincikawa ko shirin na kaiwa ga waɗanda aka yi shi dominsu, sannan ana amfani da kuɗi da kayan aiki yadda ya kamata, sannan ana ɗaukar hannu daga waɗansu shirye-shirye idan akwai buƙatar hakan.
Aunawa: Auna shiri domin gano tasirinsa da ingancinsa.
Ya kamata sanya ido da aunawa su taimaka wa ƙungiya wajen gano ko akwai buƙatar sauye-sauye ga shirin da ake gudanarwa, ko abubuwan da suka shafi shirin da za su nan gaba. Modul Ɗin Koyo zai samar da ƙarin bayani game da yadda za a yi amfani da bayanan da aka tattara domin inganta shirinku.
Yaya mizanin yawan wanzuwarsa? | Waɗanne nau'ukan tambayoyi yake suke amsawa? | Wane nau'in bayani ne ake amfani da shi? | Wa ke aiwatarwa? | |
---|---|---|---|---|
SANYA IDO | Sau da dama, rana-rana, mako-mako, da/ko wata-wata |
|
Bayanai game da ayyuka, amfani da kuɗaɗe, da sakamako na gajeren zango | Kowane mamba na tawagar da ke cikin shirin |
AUNAWA |
A lokuta na musamman A misali: a tsakiyar shirin, a ƙarshen shirin, ko a ƙarshen shekara |
|
Bayanai game da sakamako da manufofi | Tawagar aunawa: ko dai na cikin gida ko na waje |
Sanya ido ga ƙoƙarin da shiri ke yi na taimaka wa ƙungiya domin bibiyar cigaba da ake samu a ƙoƙarin cimma manufofi da maƙasudanta. Yayin da ya kasance masu tallafawa na amfani da samfura daban-daban domin tsara bayanan, muhamman ɓangarori na iya haɗawa da: