Game Da

Title
Tushen Bayanen Jagorancin

Fasahar ƙirƙirar Bayanan Jagoranci Game da CVE Domin Ƙananan Ƙungiyoyi a kan intanet ya zo ne kai tsaye daga ƙungiyoyin fararen hula waɗanda ke aiwatar da shiraruwa domin daƙilewa da yaƙar tsattsauran ra'ayin rikici (P/CVE). Da yawa daga cikin waɗannan ƙungiyoyi da ke ƙasashen da tsattsauran ra'ayin rikici ya shafa na fafutukan neman bayanai da za su kasance masu gamsarwa, taƙaitattu, sannan waɗanda ke da amfani kai tsaye, sannan sukan sha wahala wajen neman kayan aikin da aka samar kai tsaye domin amfaninsu kuma a cikin harshensu na gida. A taƙaice, da yawa daga cikin kayan aikin an samar da so ne domin amfanin mahukunta, masu ba da tallafi, ko ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa kamar su NGOs. Kayan aiki kaɗan ne ke samar da bayanai da jagoranci ga masu wannan fafutuka a ƙaramin mataki domin su kwaikwaya sannan su yi amfani da shi a cikin al'umominsu - a matakin al'umma. Bayan haka, kasancewar duniya na ƙara mayar da hankali wajen yaƙar tsattsauran ra'ayin rikici, to kullum akan samu ƙarin bincike da kayan aiki da kuma bayanai game da P/CVE. Wannan yawaitar bayanai ya sa ya zamo abu mai wahala ga ƙananan ƙungiyoyi da su samu, su fahimta, sannan su iya amfani da bayanan cikin salon da ya kamata.

Saboda haka, Hukumar Raya Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID) ta goyi bayan FHI 360 domin tsara kayan aiki da zai samar wa masu amfani damar kaiwa ga bayanen da suke buƙata cikin sauƙi ta hanyar tsara rukunonin ƙunshiyar ta yadda za su tattauna kan matakai daban-daban na gudanar da shirin (Samu da Tsarawa da Aiwatarwa da M&E da Ɗaukar Darasi). Kundin jagorancin ya taɓo muhimman tsare-tsare waɗanda ƙananan ƙungiyoyi za su iya amfani da su domin gudanar da shirin P/CVE sannan ya samar da liƙau ɗin da za a iya samun ƙarin kayan aiki a kowace gaɓa. Domin rage maimaici tare da gabatar da mashahurin ƙoƙari da masu P/CVE suka yi, mun zaɓi da mu ba da haske game da kayan aikin da ake da su, sannan ba za mu ƙirƙiri sabon ƙunshiya ba har sai idan mun ci karo da wani giɓi da ke buƙatar bayanai.

Title
Don me Aka Samar da Wannan Kayan Aiki

Wannan ba gama-garin jagoranci ba ne da ya dace da kowane shirin P/CVE. Samfuran bayanai ne da kayan aiki domin amfanin ƙananan ƙungiyoyin P/CVE. Za a iya samun waɗansu tsare-tsare, salailai, da kayan aki da za su kasance masu amfani a gare ku, ko waɗansu shawarwari da ba a faɗa ba. Kamar haka kuma, mun fahimci cewa ƙananan ƙungiyoyi sukan bayyana ilimi da fahimtar da suka yi wa batutuwa, sannan su samar da mafita. Muna so mu tabbatar da cewa wannan bayanan jagoranci sun dace sannan sun yi daidai da buƙatar mutane da ƙungiyoyi daban-daban, saboda haka, ku daure ku tuntuɓe mu domin sanar da mu abin da ya fi dacewa da ku. Za mu sabunta bayanan jagoranci yadda ya kamata.