Domin tabbatar da cewa an tsara shirye-shiryen P/CVE ta sigar da zai samar da muhimmin tasiri, a yi tunani game da samar da Ra'in Sauyi (ToC) domin zayyana dalilin da ya sa shiri zai cimma manufofinku da kuma ta yadda hakan zai faru. Sashen da ke ƙasa na gabatar da muhimman bayanai da jagoranci game da samar da ToC wanda zai taimaka muku wajen tsara ayyukanku tare da dangantawa da sauyin da kuke ƙoƙarin kawowa. Zai iya kasance kun riga da kun fara gudanar da ayyuka domin karewa ko daƙile VE. A wannan bagire, ToC na iya taimaka muku wajen zayyana dalilin gudanar da shirinku da kuma alaƙarsa da manufofin P/CVE. Sannan dama ce ta gano ko ya dace ku sauya salonku sannan ku tsara shirinku. Sannan wannan mataki zai taimaka wa tsarin sa ido da gwadawa (M&E), wanda aka tattauna a cikin modul ɗin Sa'ido da Gwadawa.
A cewar USAID, Ra'in Sauyi (ToC) "na bayani game da hanya da dalilin da ya sa ake tsammanin a samu sauyi da kuma yadda ƙungiyarku ke da niyyar yin aiki kai tsaye da/ko a kaikaice domin yin tasiri wajen samar da sauyin da ake buƙata da kuma Dalilin Aiwatar da Shirin.”
- Ra'o'in sauyi gajerun jawabai ne da ke bayanin dabara da hikimar da ke tattare da dalilin aiwatar da shirin. Suna bayani game da "me ya sa, ta yaya, da kuma dalilin" da ya sa ake tsammanin sauyin.
ToC ɗin da aka tsara shi yadda ya kamata, ya kamata ya taimaka muku wajen:
- a fayyace sauye-sauye da abubuwan da ke jawowa ne ke haifar da cusa tsattsauran ra'ayi da cusa ra'ayi a matakin cikin gida waɗanda kuke ƙoƙarin magancewa, da kuma abin da ya shafi tsaronku a cikin tsarin;
- bayyana manufofin shirin ƙarara, wanda ke da dangantaka da karewa da/ko daƙile tsattsauran ra'ayin rikici; da
- a yi cikakken bayani game da hanya da dalilin da ya sa aikin zai magance sauye-sauye da abubuwan da ke janyo tsattsauran ra'ayin rikici domin cimma manufofinsa.
Sau da dama akan bayyana ra'o'in sauyi a matsayin zantuttukan "idan/sai"; "Idan muka yi X (aiki), sai mu samar da Y (sauyi/garambawul zuwa ga zaman lafiya, kwanciyar hankali, tsaro)." Domin tabbatar da amfani da ilimin fahimtar rikici, ana kuma ba da shawarar sanya hasashe da hikima game da dalilind a ya sa muke tunanin X zai samar da Y, ta hanyar sanya Z - "saboda." Wannan jawabi na "saboda" na ƙarin bayani a kan hasashenmu - da haɗurran da suka dangance su - da kuma yadda za mu ji da amarinsu ta hanyar shiri.
DABARUN AIWATARWA
Kafin ku gina Ra'in Sauyinku, ga nan aikin da za ku gudanar a cikin rukuni domin taimaka muku wajen yin tunani game da manufofi da maƙasudan shirinku:
- An zo ƙarshen shirin sannan mai rahoton labarai na rubuta insha'i game da manyan sauye-sauye da shirinku ya taimaka wajen samarwa. Waɗanne sauye-sauye ne mai rahoton zai yi rubutu game da su? Waɗanne siffofi uku ne za su iya yin bayanin wannan tasirin?
- Ku rubuta manyan manufofi ko nasarori guda uku da aka samu sakamakon shirin. A sanya amsoshi da ke kama da juna ta fuskar jigo. Daga nan ku yi bitar su sannan ku ƙarfafa a kan manufofin a cikin babban rukuni. Daga nan, ku yi nazari tare game da hasashen da dole su kasance gaskiya kafin a samu damar cimma waɗannan manyan manufofi.
Ra'o'i da Manunan Sauyi na USAID (THINC) ya taƙaita muhimman ra'o'in sauyi da ake amfani da su a bagiren kwantar da rikici, mangance rikici, da samar da mafita. Tsarin THINC zai taimaka muku wajen samar da Ra'in Sauyinku.