Damar Ci Gaba da Ɗorewa

Sau da dama ƙananan ƙungiyoyi suna yin aiki ne da kuɗaɗen shiga da ba wadatattu ba da/ko na gajeren zango. Shirye-shiryen P/CVE sun fi dacewa idan suna da tsarin da za a kammalasu cikin ƙanƙanin lokaci ko idan suna buƙatar kuɗaɗe kaɗan domin gudanar da su tun da waɗannan shirye-shiryen na buƙatar ɗorewa da shirin da zai ɗauki tsawon lokaci domin shawo kan abubuwan da ke kawo VE da ke da ruɗani. Saboda haka, ku yi tunani game da hanyoyi daban-daban na ɗorewar aikinku yayin da kuke tsara shirinku na P/CVE a matakin Samu da kuma duk tsawon lokacin aiwatarwa.

ME ƊOREWA KE NUFI?

A bagiren aikinnmu, ana samun ɗorewa ne a matakai uku:

Sakamako

Results - What does it mean graphic

ME YAKE NUFI?

Ko da a ce ayyukan shiri sun tsara, sau da dama ayyukan na haifar da tasiri. A misali, ƙungiyar da ke ƙoƙarin kammala shirin da ya shafi ba da horaswa na iya kasancewa ta kasa ba da horaswa a sababbin mutane, amma dukkannin mahalarta da aka a wa horaswa a lokacin shirin na iya ci gaba da amfani da ƙwarewarsu da iliminsu.

Results - How can you advance it graphic

TA YAYA ZA KU IYA BUNƘASA SHI?

Tsarin shirin na iya taimakawa wajen ganin sakamakonsa ya ci gaba da yin tasiri:

  1. Samu kuɗaɗen da ake buƙata domin maye gurbin waɗanda za su ƙare. Ya kamata a fara tsara matakan ɗorewar aiki a lokacin da ake tsara aikin domin tabbatar da cewar ƙungiyar na iya ganowa tare da neman kuɗin shiga ta waɗansu hanyoyi. A lokacin aiwatarwa, ƙungiya na iya neman haɗin guiwar waɗansu ƙungiyoyi waɗanda za su iya tallafawa ta fuskar kuɗaɗen shiga ko a aikace. A misali, idan aka ɗauki ƙungiyar ɗaukar hoto a matsayin misali, ƙungiyar na iya neman haɗin guiwar shirin da ya shafi sauraro da kallo domin samun damar kaiwa ga kayan aiki tare da neman ɗalibai 'yan sa kai domin su yi jagoranci sannan su ba da horaswa ga matasa da suka shiga ƙungiyar.
  2. Bunƙasa shiri domin tabbatar da cewa an inganta ƙwarewar da ake da ita a ɓangaren gudanarwa da abubuwan da za su sa ayyukan su ɗore. Ta hanyar amfani da wannan misali, ƙungiyar na iya ba da horaswa ga masu gudanarwa a matattarar matasa domin ci gaba da jagoranci da ba da horaswa ga matasa da ke cikin kulab ɗin.

AYYUKA

Activities - What does it mean graphic

ME YAKE NUFI?

Ɗorewar ayyukan shiri na nufin ci gaba da gudanar da ayyukan da aka samu kuɗin gudanar da su a ƙarƙashin shiri, maye gurbin ayyuka ta fuskar muhallai da/ko aiwatar da ayyukan bibiya da suka dace. A misali, idan shiri na samar da tallafi ga matattarar matasa domin gudanar da ƙungiyar ɗaukar hoto, to ɗorewar ayyukan shiri na iya ɗaukar ma'anar cewa kulab ɗin zai ci gaba da wanzuwa tare da janyo ƙarin matasa cikin sha'anin ɗaukar hoto.

Activities - How can you advance it graphic

TA YAYA ZA KU IYA BUNƘASA SHI?

Ayyukan shiri za su iya ɗorewa ta hanyar:

  1. Samar da ƙuɗi da ake buƙata domin maye gurbin wanda zai ƙare, wanda za a iya yin hakan ta hanyar bincikowa da kaiwa ga waɗansu waɗansu hanyoyin samun kuɗi. Ya kamata a fara tsara matakan ɗorewar aiki a lokacin da ake tsara aikin domin tabbatar da cewar tsarawa da aiwatarwa sun ba da dama ga ƙungiyar domin ganowa tare da neman kuɗin shiga ta waɗansu hanyoyi. A lokacin aiwatarwa, ƙungiya na iya neman haɗin guiwar waɗansu ƙungiyoyi waɗanda za su iya tallafawa ta fuskar kuɗaɗen shiga ko a aikace. A misali, idan aka ɗauki ƙungiyar ɗaukar hoto a matsayin misali, ƙungiyar na iya neman haɗin guiwar shirin da ya shafi sauraro da kallo domin samun damar kaiwa ga kayan aiki tare da neman ɗalibai 'yan sa kai domin su yi jagoranci sannan su ba da horaswa ga matasa da suka shiga ƙungiyar.
  2. Bunƙasa shiri domin tabbatar da cewa an inganta ƙwarewar da ake da ita a ɓangaren gudanarwa da abubuwan da za su taimaka wajen samar da ayyukan da suka kamata. Ta hanyar amfani da wannan misali, ƙungiyar na iya ba da horaswa ga masu gudanarwa a matattarar matasa domin ci gaba da jagoranci da ba da horaswa ga matasa da ke cikin kulab ɗin.

MASU GUDANARWA

Implementers - What does it mean graphic

ME YAKE NUFI?

Na magana game da damar da ƙungiyar karan kanta take da shi na cigaba da gudanarwa da aiwatar da sauran ayyuka a nan gaba. A misali, ƙungiyar tana da kuɗaɗen shiga da ko ƙarfin guiwar gudanarwa da ake buƙata domin ɗorewar ayyukanta.

Implementers - How can you advance it graphic

TA YAYA ZA KU IYA BUNƘASA SHI?

Ɗorewar ayyukan ƙungiya na iay ƙunsar yin huɓɓasa ta fuskar:

  1. Ɗorewar samun kuɗaɗen shiga da damar samun kuɗaɗen shiga a nan gaba, wanda ya haɗa da damar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi
  2. Bunƙasa ƙungiya domin ta ta samu cigaba ta fuskar ƙwarewarta domin samun damar gudanar da ayyukan cigaba, sannan domin ba wa manajojin shirye-shirye damar tabbatar da cewa a su iya aiwatar da abubuwan da ake buƙata game da ayyukansu, su fahimta sannan su fuskanci sauye-sauyen yanayi, sannan su samar da haɗin guiwa mai kyau

Auna lamuran ƙungiya na iya kasancewa abu mai matuƙar amfani wajen taimaka wa ƙungiya domin ta gano abubuwan da ake buƙata tare da shirya tsarin da zai samar da waɗannan buƙatu. Ku daure ku duba Bayanai Game da Aiwatarwa da ke ƙasa.

MATAKAN AUNA IYA AIKI

Kayan aiki don Tantance Ƙarfi

Shin kuna da ra'ayin auna mizanin iya aiki na ƙungiyarku a muhimman ɓangarorin gudanarwa guda bakwai - ciki har da shugabanci, tafiyar da harkokin mutane, da kuma tafiyar da harkokin kuɗi? Ku duba matakan Auna Iya Aikin Ƙungiya.

Shin kuna da ra'ayin inganta mizanin iya aikin ƙungiyarku a fannin fasaha game da shiye-shiryen da suka shafi matasa? Ku duba Matakan Auna Shirye-Shiryen Matasa waɗanda ke ba wa ƙungiyoyi damar yin nazari game da shirye-shiryensu na cikin gida da tsarin gudanarwarsu domin Cigaba Mai Kyau na Matasa (PYD) tare da manufar bunƙasa shiri domin al'amuran matasa.

TA YAYA ZA KU IYA BUNƘASA MATAKAN ƊOREWAR SHIRI A DUKKANNIN ZANGUNAN SHIRIN?

DAMA

Ku gano ayyukan da ke gudana waɗanda shirinku zai iya ɗorawa daga kansu ko abokan harƙallar da za ku iya aiki tare da su.

FASALI

Ku sanya dabarun ƙara ƙwarewa da haɗin kan al'umma wajen tsara matakan ɗorewar shiri a lokacin tsara shirinku.

AIWATAR

Ku yi aiki tare da mahukunta a cikin al'umma domin aiwatar da ayyuka domin bunƙasa mallaki a matakin ƙaramar hukuma.

KOYO

Ku gano darrusa daga shirin waɗanda za ku iya sanar da waɗansu domin ɗorewa da bunƙasar sakamakon P/CVE.

SANYA IDO DA AUNAWA

Ku kundace sakamakon P/CVE domin nuna sakamako masu kyau na ayyukanku sannan ku yi huɓɓasa domin cigaba da samun kuɗin shiga na cigaba da gudanar da ayyukanku na P/CVE.

Me yasa dorewa yake da mahimmanci ga Ayyukan P/CVE?

Tsattsauran ra'ayin rikici al'amari ne mai matuƙar sarƙaƙiya, sannan sau da dama ba za a iya magance abubuwan da ke haifar da VE ba ta hanyar nau'in aiki guda kawai. Sau da dama akan buƙaci ɗorewar aiki da shiri na tsawon lokaci domin samun sauye-sauye masu amfani ta fuskar tunani, halayya, ko ɗabi'u a matakin ɗaiɗaikun mutane ko domin magance lamuran da suka shafi shugabanci waɗanda ke jefa al'umma cikin haɗarin fuskantar VE. Bugu da ƙari, shirye-shiryen gajerun zango waɗanda aka tsara sannan aka aiwatar cikin sigar da ba ta ba da tabbacin samun ɗorewa na iya ruruta saɓani da matsaloli. A misali, shirin da ya samar da kulab ɗin matasa amma bai tsara yadda ayyuka za su ci gaba ba bayan kuɗin shigar da ake da su sun ƙare, na iya haifar da matsala yayin da ya kasance matasan da ke buƙatar a ƙarfafa musu guiwa suka sake karaya sannan suka ji cewa ba su da amfani yayin da tsarin da ke taimaka musu ya dakatar da aiki.

Haka kuma, yayin da ake tattaunawa game da shirye-shiryen P/CVE, za mu iya mayar da hankali kan matakan ɗorewa guda biyu na farko:

  • Ɗorewar sakamako domin shirinku, ciki har da ayyukan gajeren zango, ya kasance an tsara shi ne sannan an gudanar da shi cikin sigar da zai taimaka wa tasirin shirin na tsawon lokaci wanda ke da tasiri a kan abubuwan da ke janyowa
  • Ɗorewar aiki domin ya kasance duk waɗansu ayyuka da kuka fara wanda ke da muhimmancin da za a ci gaba da su har zuwa ƙarshen shirin yadda zai inganta ɗorewar shirin

TA YAYA ZA MU IYA SAMUN ƊOREWAR SAKAMAKON SHIRI DA/KO AYYUKA?

Babu hanya ko mataki guda na inganta ɗorewa. Dole ne kowane shiri ya gano matakan da ya kamata ya bi domin gano ayyuka mabambanta da ya kamata ya aiwatar domin ya samu ɗorewar sakamakon ayyukansa.

YIN AIKI TARE DA MAHUKUNTA A CIKIN AL'UMMA DA KUMA SAMAR DA HAƊIN GUIWA NA IYA BA DA DAMAR A SAMU ƊOREWA

Al'ummomi za su fi ɗorar da ayyukan da aka dama da su wajen tsarawa da/ko aiwatarwa, wanda suke ganin na da alaƙa da buƙatun da suka bayyana, sannan suka ji cewa mallakinsune. Bugu da ƙari, yayin da kuke tsarawa da aiwatar da shirye-shiryenku, za ku iya haɗawa da mahukunta da abokan harƙalla domin tsara yadda za ku ci gaba da gudanar da ayyukan yayin da ƙudin shigar da kuke da su suka ƙare. A misali, shin za su iya samar da wuri, ƙwararru, kayan aiki, ko kuɗi domin taimakawa wajen ciyar da aikin gaba?

SHIRYE-SHIRYE DA MUSANYEN BAYANAI DA DARRUSA DOMIN SAKAMAKO YA ƊORE

Abu ne mai muhimmanci ga ƙungiyarku da ta samar da darrusa a yayin da take aiwatar da ayyukan P/CVE (duba Modul Ɗin Koyo domin samun ƙarin bayani game da matsayin koyo ga aiwatar da shiri). Daga nan za ku iya gabatar da waɗannan darrusa da bayanan da suka dace ga mahukunta da abokan haɗin guiwa da ke cikin al'ummarku. Wannan musanyen bayanai na iya taimakawa wajen ɗorewar shiri ta ɓangarori da dama, ciki har da:

  • Taimaka muku wajen gano waɗanda ya dace su kasance abokan haɗin guiwa waɗanda ke da ra'ayi game da aikinku
  • Ba wa waɗansu damar koyo daga aikinku har ma wataƙila su yi amfani da waɗannan bayanai yayin aiwatar da aikinsu na P/CVE, wanda hakan zai taimaka wajen ɗorewar sakamakon aikinku
  • Ba ku damar gabatar da ƙwarewar da kuke da ita a ɓangaren P/CVE ga sauran ƙungiyoyi, ciki har da masu ba da tallafi, domin su kallo ku a matsayin waɗanda ke iya zamantowa abokan haɗin guiwarsu a ɓangaren ayyukan P/CVE

KU SANYA MATAKAN INGANTA ƘWAREWA A CIKIN SHIRIN DOMIN SAMAR DA DAMAR ƊOREWA

Inganta ƙwarewa abu ne mai muhimmanci ta fuskar tabbatar da mallaki tare da tabbatar da ilimi da ƙwarewar da ake buƙata domin ayyukan P/CVE su ci gaba da gudana a cikin al'ummar. Inganta ƙwarewa na iya mayar da hankali kai:

  • Inganta fahimtar VE da P/CVE a tsakanin mahukunta a cikin al'umma domin ba wa mahukuntar damar ba da gudummuwa a fannin tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen P/CVE da suka dace
  • Samar da ƙwarewar da ake buƙata domin ɗorewar aikin da shirin ya faro: Yin amfani da misalin kulab ɗin ɗaukar hoto domin janyo matasan da ke fuskantar wariya. Shirin zai inganta ƙwarewar masu gudanar da cibiyoyin matasa game da aiki da matasa yadda ya kamata, tsara ayyukan da za a halarta da ilimin ɗaukar hoto, da amfani da dabarun da za su taimaka wajen tabbatar da cewa cibiyar matasan na iya ci gaba da aiki da matasa da taimakon kulab ɗin
  • Bunƙasa ilimi da ƙwarrewa game da babutuwa da za su iya taimakawa wajen ɗorewar shiri: Wannan ya haɗa da tuntuɓan 'yan ƙasa da ke waɗansu wurare na daban, roƙon hukumomi, gayyato ɓangarori masu zaman kansu, faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi, tsarawa, da sauransu.

TSARAWA, GINAWA, DA JERA AYYUKA DOMIN SAMAR DA ƊOREWAR SAKAMAKO

Ofishin Ƙaddamar da Sauyi (OTI) na USAID sun ɗauki sababbin matakai na gudanar da shirye-shirye da suka shafi CVE. Ta hanyar bin wannan mataki, shirin OTI na iya aiwatar da ayyuka na gajerun zanguna, ta amfani da kowane aiki ko jerin ayyuka domin ɗaukar hannu da kuma tsara wanda zai biyo bayansa. Yayin da ya kasance wannan mataki na ba da damar koyo da ɗaukar hannu yayin gudanarwa, yana ƙunshi da ƙalubalen da ya shafi ɗorwa: ta yaya sakamakon da aka samu daga sanya kuɗaɗe kaɗan (ayyuka) za su iya ci gaba yayin da kuɗaɗen gudanar da ayyukan suka ƙare? Ilimin da OTI ke da shi ya bayyana cewa "rashin ɗorewa da za a iya samu na shiri da manyan ƙalubale duk za a iya rage su idan masu gudanarwa sun yi tunani tun farko tare da tsara yadda za a gudanar a shirin gajeren zango, inda za a riƙa ci gaba da samun kuɗaɗen shiga bi-da-bi wanda hakan zai kai da a cimma abin da ake so na CVE." Wannan mataki na iya kasancewa mai nagarta ga ƙungiyoyi idan har za su aiwatar da shirye-shiryen gajeren zangu sakamakon ƙarancin kuɗaɗen shiga amma kuma suna son tabbatar da cewa sakamakon kowane shiri zai taimaka wajen samar da sakamakon CVE mai ɗorewa na tsawon lokaci. Domin samun ƙarin bayani game da amfani da tsarin ayyukan P/CVE na tsarawa, ginawa, da jerewa, to ku duba Kundin aikin OTI CVE da kuma Tsarin Fuskantar Shirin CVE.

SAMUN KUƊAƊEN SHIGA DA HANYOYIN SAMUN KUƊAƊE DABAN-DABAN DOMIN ƊOREWAR AIKIN P/CVE

Ko da kun ɗauki dukkannin matakai na tsara ɗorewar aikin P/CVE ɗinku da ke gudana, har ila yau za ku so ku samu ƙarin kuɗi domin ci gaba ko bunƙasa aikinku. Ku yi nazari game da bayanan jagoranci da ke ƙasa da suka shafi samun kuɗaɗen shiga:

  • Ku haɗa kai da waɗanda ke aiki game da P/CVE. Waɗannan na iya haɗawa da masu ba da tallafi daga ƙasashen ƙetare, ƙungiyoyin ba da tallafi na ƙasa-da-ƙasa, hukumomin yankuna, ko ƙungiyoyin fararen hula na matakin ƙasa ko ƙananan hukumomi. Yayin da ya kasance babu cikakken jerin sunayen masu ruwa da tsaki, wannan jerin sunaye ya ƙunshi ƙungiyoyi da suka taimaka wajen samar da haɗin guiwa da musanye tsakankin masu ruwa da tsari a ɓangaren P/CVE a ɓangarori ko yankuna na musamman. 
  • Haɗa kai da al'ummarku domin cigaba da P/CVE. Ƙungiyarku na iya samun kayan aiki daga cikin al'ummarku domin gudanar da ayyukan P/CVE da za su inganta sakamakon P/CVE. Abubuwan da za a iya amfana da su daga al'umma sun haɗa da ra'ayoyi, lokaci, ƙwarewa, talalfin kuɗi, ko gudummuwa ba a aikace ba. A misali, Gidauniya na mayar da hankali kan ƙaruwar amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da kafafen intanet daban-daban domin sadar da sababbin ra'ayoyi, shirye-shirye, da kiraye-kiyare zuwa ga waɗanda ka ita tallafawa. Waɗannan ma su bada gudummawa na iya kasancewa a cikin al'umma, ko kuma kawai waɗanda suka kasance suna da ra'ayin ba da gudummuwa ga gidauniyar da ake yi. Domin samun ƙarin bayani, ku duba Mafita ta Fuskar Tattalin Arziki Domin Cigaba Mai Ɗorewa na UNDP - Gidauniya