Nazarin Bincike

Title
Tsara Ayyukan P/CVE da suka kasance Bisa Dalili, Masu Damawa da Kowa, Masu Ɗore, Kuma Masu Bunƙasawa

An ƙirƙiri ƙungiyar Association Tétouani de Iniciativas Laborales (ATIL) a shekarar 1993 sannan tun lokacin sun aiwatar da ayyuka sama da 50 da ke bunƙasa lamarin ba da kariya ga yara, ilimi, horaswa, da kuma sanya ilimin zamantakewa da na sana'a domin kauce wa ware matasa. Asalin wurin da ATIL ke gudanar da ayyukanta shi ne Tétouan, Morocco, sannan takan yi haɗin guiwa da ƙungiyoyin fararen hula (CSOs) daban-daban da ƙungiyoyin ƙasashen waje da hukumomin gwamnati.

Kasancewar sau da dama CSOs da ke Morocco ba su da kayan aikin gudanar da ayyukan da suka shafi P/CVE, ATIL ta yanke shawarar samar wa ƙananan ƙungiyoyi kayan aikin da zai taimaka musu wajen shiryawa da sanya ayyukan P/CVE a cikin aikinsu da ke gudana. A ƙarƙashin shirin USAID na Fuskantar Tsattsauran Ra'ayin Rikici a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka (CoVE-MENA), ATIL ta samu taimako daga FHI 360 domin gyarawa da gwada kayan aiki da ake da shi domin taimaka wa sauran CSOs wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan P/CVE ko waɗanda suka shafi zamantakewa da al'adu.

Ilimin da ATIL ta samu na aiki da matasa masu rauni ko masu fuskantar wariya ya nuna muhimmancin gayyatar amintattun mahukunta - kamar makarantu da ƙananan ƙungiyoyi - domin taimakawa wajen tabbatar da cewa al'ummu suna da ra'ayin yin aiki tare, da kuma inganta tasirin ayyukansa. Bayan haka, ATIL na son tabbatar da cewa an gyara kayan kayan aikin domin amfanar al'ummu da suke da al'adun gargajiya game da bambance-bambancen jinsi da kuma wurin da har yanzu VE ya kasance batu mai jan hankali sosai. Haka kuma, ATIL ta ɗauki hayar masani domin gyaran kayan aikin. Waɗannan matakai sun haɗa da:

1
Details

Tattaunawar bincike tare da da wakilan CSO guda shida domin taimakawa wajen samun bayani game da ƙoƙari gano buƙatun CSO da ya suka shafi taimako da bunƙasa P/CVE

2
Details

Taron ƙara wa juna sani na Horas da Masu Horaswa wanda aka gabatar wa ma'aikatan ATIL tara ƙarƙashin jagorancin masani a ɓangaren tsarawa da fadakarwa game da ayyukan da suka shafi al'ada da zamantakewa masu manufar magance tsattsauran ra'ayin rikici

3
Details

Samar da kayan aiki ga CSO game da yadda za su tsara da aiwatar da shirye-shirye da suka shafi al'ada da zamantakewa da ya haɗa da matakan P/CVE, wanda aka gwada ta hanyar horaswar ƙara wa juna sani na ƙarshe ƙarƙashin kulawar ATIL wanda aka yi wa ƙwararru guda 22 daga CSO ɗin da ke ƙaramin mataki da kuma sauran masu faɗa a ji a fannin karatu da kuma abokan haɗin guiwa

Sannan ATIL na ƙoƙarin aiki tare da masu ruwa da tsaki mabambanta a kowace gaɓa na shirin ta hanyar:

  • Samarwa da aiwatar da dabaru ta la'akari da kayan aiki domin ba da horaswa ga masu ruwa da tsaki a matakin ƙaramar hukuma domin ɗaukar hannu da sanyo al'amuran P/CVE a cikin shirye-shiryensu na zamantakewa waɗanda aka sanya a cikin gine-ginen ilimi (ɗakunan karantun al'umma, cibiyoyin al'adu, da makarantu)
  • Dabarun damawa da masu ruwa da tsaki domin mangance duk waɗansu ƙalubale da suka shafi damawa da dukkannin jinsi da nau'ukan mutane; tare da tsara hanyar watsawa da yaɗa ilimi domin gwadawa ko dabarar za ta yi aiki a waɗansu bagire na daban

ATIL sun tsara ayyukansu domin tabbatar da komai ya tafi daidai har bayan lokacin gudanar da shirin, ta hanyar:

  • Ƙoƙarin auna ƙwarewa da mayar da hankali wajen gina ƙwarewa a fannin fasahar CSO domin tabbatar da cewa za a iya ci gaba da gudanar da aiki bayan tallafin farko ya ƙare
  • Inganta ƙwarewar ma'aikatan ATIL domin su horas da waɗansu jami'ai da ma'aikatan CSO game da yadda za su yi amfani da kayan aiki wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan da suka shafi zamantakea da al'ada waɗanda ke inganta P/CVE
  • "Ginawa da jeranta" shirinsu ta hanyar tsara ayyukan bibiya ta hanyar (CoVE-MENA da sauran mahukunta) ɗorawa a kan abinda ya gabata tare da ci gaba domin bunƙasa tasirorin aikin gajeren zango da ya gabata

Ta amfani da tsarin aikin da ya mayar da hankali a kan inganta kayan aikin CSO, ATIL sun tsara tare da aiwatar da a ƙalla ayyuka uku da suka shafi bibiya:

  • Tare da haɗin guiwar gwamnatin Tétouan, ATIL sun ƙaddamar da shiri domin CSOs a yankin Tétouan domin inganta ƙwarewarsu a ɓangaren tsara abubuwan da suka shafi zamantakewa da al'ada. ATIL sun yi amfani da kayan aikin a matsayin takardar jagoranci domin ba da horaswa ga mahalarta game da yadda za su yi amfani da ita, wanda hakan na ba su damar koyon tsarawa da aiwatar da ayyuka a gine-ginen al'umma inda suke gudanar da ayyukansu.
  • Ta hanyar haɗin guiwa da shirin da Hukumar Haɗin Kan Mutanen Espanya (AECID) ta ɗauki nauyi, ATIL, da Ma'aikatar Ilimi da Koyar da Sana'o'i a Tétouan sun ƙaddamar da shirin P/CVE domin masana ilimi a makarantu da sauran makarantun al'umma. Sun samar da aikin da ya shafi shiryawa domin tsarawa da aiwatar da faɗakarwa da ayyukan P/CVE da suka shafi zamantakewa da al'ada waɗanda ke taimaka wa P/CVE a makarantu.
  • ATIL ta aiwatar da shirin watanni biyar a ƙarƙashin shirin CoVE-MENA domin magance cusa wa matasa tsattsauran ra'ayi. Shirin ya haɗa da ranar koyo game da VE ta haɗakar mahukunta a yankin Tangier-Tétouan-Al Hoceima da kuma shirin Horas da Masu Horaswa (ToTs) na CoVE-MENA tare da haɗa kai da CSOs a Algeria da Tunisia domin gabatarwa da gwada yanayin karɓuwar salon P/CVE ɗin ATIL.