Ƙungiyoyi da dama da ke aiwatar da shirye-shiryen P/CVE sun ɗauki matasa a matsayin waɗanda ayyukansu suka mayar da hankali kansu Mayar da hankali kan matasa abu ne mai muhimmanci a bayyane kasancewar ƙasashe da dama - musamman a ƙasashe masu tasowa a inda za a iya samun ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi (VEOs) - matattara ne na matasa da yawa da za su iya faɗawa cikin raunin bin tafarkin tsattsauran ra'ayi. Yawanci matasa ne aka fi kallo a cikin ƙungiyoyin rikici ko na tsattsauran ra'ayi. A lokaci guda kuma, ilimin da aka samu daga bincike da aiwatarwa sun nuna cewa wani ɓangare ne kawai na matasa da ke da raunin faɗawa cikin VE ke kasancewa masu haddasa rikici. Matasa da dama bayan sun kasance masu kauce wa waɗannan tarko, sukan taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya cikin al'ummominsu.
Kalmar "matasa" ba tana nufin wani matakin shekaru ba ne, sannan gwamnatoci, ƙungiyoyi, makarantu na iya bayyana mabamancin ra'ayi game da adadin shekarun da suka kasance na matasantaka, ta la'akari da muhallinsu, buƙatu, da abubuwan da ake buƙata. Saboda haka, ya fi kyau a fahimci matasantaka a matsayin matakin rayuwa, a lokacin da rayuwar mutum ke sauyawa daga zangon yarunta zuwa na manyanta. Kamar haka kuma, akwai aubuwa guda biyu da ya kamata a yi la'akari da su yayin aiwatar da shirin da ya haɗa da matasa:
Ya kamata a tsara shirye-shirye da ayyukan P/CVE wanda ya haɗa da matasa ta la'akari da kowane matakin cigaba sannan a tsara shi ta yadda zai tallafa wa matasa ta fuskar ra'ayoyinsu da ƙwarewarsu. Matakan girma guda huɗu na matasa wanda aka kawo a cikin shirin USAID na Matasa a Cikin Harkar Samar da Doka su ne: (1) Farkon Samartaka: Shekaru 10–14; (2) Samartaka: Shekaru 15–19; (3) Tashen Balaga: Shekaru 20–24; da (4) Shiga Matakin Balaga: Shekaru 25-29. Rataye na A & B na wannan doka sun samar da bayani game da manyan siffofin cigaba na kowane mataki da kuma nau'in shiri da dabarun aiwatarwa da za su iya kasancewa mafiya inganci a kowane mataki.
Cigaba mai kyau na matasa (PYD) mataki ne na bunƙasa matasa ta hanyar mayar da hankali kan ƙaruwar arzikin matasa da ƙarfafa abubuwan da ke ba su kariya. PYD ya ɗoru ne kan fahimtar da aka samo daga bincike da ilimin shiri, wanda ke nuna cewa "gina basira, jiki, zamantakewa, da tunanin matasa shi ne matakin da ya fi inganci sama da mayar da hankali kan gyara matsaloli.”
Yayin da ya kasance akwai tsaruka daban-daban na PYD, mun mayar da hankali ne kan tsarin da Shirin Koyo Don ZarrarMatasa (Youth Power Learning) ya samar wa USAID. ZarrarMatasa ya nazarci bincike da tsaruka da suka gabata tare da tuntuɓar USAID da sauran ƙungiyoyi. Domin samun ƙarin bayani game da tsarin ZarrarMatasa na PYD, a daure a duba YouthPower.org.
Hanyar Aiki Tare da Matasa Mai Fuskoki Uku na DFID: Wannan yanya da ta mayar da hankali kan fikira na kallon halarta ta fuskoki guda uku: (1) aiki tare da matasa a matsayin masu cin gajiya, (2) aiki da matasa a matsayin abokan haɗin guiwa, da (3) tallafa wa matasa a matsayi jagorori.
Tsarin Bunƙasar Cigaba na Cibiyar Bincike (Search Institute’s Developmental Assets Framework: Tsarin ya bayyana nau'ukan tallafi da ƙwarin guiwa (cigaba) 40 da matasa ke buƙatar cimmawa. Rabin cigaban ya mayar da hankali ne kan alaƙa da damarmakin da suke da buƙata a cikin iyalinsu, makantu, da al'ummomi (cigaba na waje)/ Sauran cigaban su mayar da hankali kan ƙwarin guiwa ta fuskar zamantakewa-tunani, ɗabi'u, da ɗawainiyoyi da ake bunƙasawa a jikin matasa (cigaban ciki).
TA WACE FUSKA PYD YA BAMBANTA DA SAURAN HANYOYIN BUNƘASA MATASA NA GARGAJIYA?
Al'amarin PYD ya fara bunƙasa ne a shekarun 1990. A wannan lokaci, manazarta sun fara karkata tambayoyinsu game da cigaban matasa daga "Me ya sa wannan matsalar ta matasa ke wanzuwa?" zuwa tambayar "Me zai sa matasa su cigaba ko su bunƙasa?" Wannan sauyi ya samo asali ne yayin da aka fahimci matasa na da damarmaki yayin da su ma suka kasance suna maraba da ra'ayoyi kyawawa, ɗabi'u, halayya, da haɗurra, sannan za su iya taimakawa tare da halartar ayyukan da suka shafi cigaban kansu ko na al'ummominsu.
Hanyar Al'ada Ga Ci gaban Matasa | Hanyoyin ciniki na PYD | |
---|---|---|
Mayar da hankali kan yanki guda don hana munanan halaye | Mayar da hankali kan matakan haɓakawa da buƙatu | |
Mai da hankali ga mutum ɗaya | Mayar da hankali ga mutum da iyali, takwarorina, al'umma, muhalli | |
An yi watsi da buƙatun ci gaba da ƙwarewa | Ya haɗa da haɓakawa da rigakafi | |
Mai da hankali kan matsalolin matasa da rigakafin matsalolin | Mayar da hankali kan gina kadarori da ƙwarewa da haɓaka kyakkyawan sakamako | |
Matasa a matsayin masu amfana/masu karɓa | Shigar da matasa a matsayin ƴan wasan kwaikwayo da kuma ƙwaƙƙwaran mahalarta | |
Matasa (ko babban haɗari ko shugabanni) ƙwararru ne suka yi niyya | Matasa masu aiki tare da al'umma, a matsayin wani ɓangare na al'umma; samar da damammaki ga dukkan matasa. | |
Matasa sune masu karɓar ayyuka da shirye-shirye | Matasa a matsayin albarkatu da abokan haɗin gwiwa waɗanda za su iya ba da gudummawa mai mahimmanci wajen tsarawa da aiwatar da ayyuka | |
Reactive, shirye-shirye na kashe daya | Amsa na tushen al'umma, mai dorewa kuma mai fa'ida | |
Ci gaban matasa aiki ne na kwararru | Ci gaban matasa aiki ne na dukkan al'umma |
A duka-duka, tsarin PYD ya kasance mai inganci yayin gudanar da shirye-shirye tare da matasa musamman da yake shirye-shiryen PYD ya cimma ko ya taimaka wajen samun sakamako masu nagarta a ɓangarori da dama da suka haɗa da:
- Yaƙar laifuka da rikice-rikice
- Jinkirin saduwar sha'awa
- Bunƙasar ƙwarewa ta fuskar ilimi/ayyuka
- Bunƙasa halartar al'umma
- Hana shaye-shaye
- Inganta dangantaka
Yayin da matakin PYD ke amfani wajen cimma muhimman maƙasudai ko sakamako (kamar hana faruwar laifi), sannan yana iya samar da waɗansu muhimman sakamako ga matasa waɗanda daga farko ba a sanya shi cikin ƙuduri ba ko kuma an ɗauke su a matsayin 'ba mafiya muhimmanci ba.' A misali, shirye-shiryen hana aukuwar laifi ta amfani da matakin PYD na iya samar da tasiri mai kyau ga ƙarewar ilimi da kuma jinkirin saduwar sha'awa. Wannan tasiri na shafar jinsi da rukunonin ƙabila.
Bayan haka, bincike da shiri game da P/CVE sun nuna muhimmancin yin aiki tare da matasa a matsayin "wakilan sauyi," tare da ƙarfafawa kan cigaban matasa, da ƙarfafa jin cewa ana tare da su da samar da damarmaki na taimakawa ga al'umma, da goyon bayan jagorancin matasa da damawa da su ga al'amura, da kuma bunƙasa ƙwarewar matasa. Dukkannin waɗannan al'amura ne masu muhimmanci a matakin PYD.
Tsarin ZarrarMatasa na PYD na USAID an gina shi ne a kan jerin abubuwa (muhimman abubuwa) da kuma sifofi da ke da alaƙa da shi (ɓangarorin da shiri ko aiki zai mayar da hankali kansu). Domin samun misalan ayyukan shirin PYD da ke da dangantaka da siffofin PYD da kuma dangantaka da Tsarin da ya Shafi Zamantakewa da Muhalli, to ku duba wannan kundi.
DABARAR AIWATARWA: JAGORA AKAN HADA MATASA A CIKIN ZAGIN AIKIN P/CVE
Yayin da kuke tunanin yadda kuka kasance ko kuma zaku iya fara haɗawa da matasa a cikin matakai daban-daban na aikinku - Kima, Tsara, Aiwatar da, Kulawa da Aunawa, da Koyi - kalli wannan bayanin jagora akan matakan shiga daban-daban da tasirinsu. da wasu tambayoyi masu jagora da za a yi la'akari da su lokacin shigar da matasa a cikin zagayowar aikin P/CVE.