Shiryayyen tsarin aiki

Shiryayyen Yanayin Aiki (Tsarin-Aiki) ya kasance kayan aiki da ke taimakawa wajen gabatar da Ra'in Sauyinku, manufa, maƙasudai, da ayyukan da ke ƙarƙashin Modul Ɗin Tsarin Gudanarwaku. Tsarin-Aiki na samar da jagoranci ga aiki tare da tabbatar da cewa ma'aikatan da ke gudanar da shiri, masu ba da tallafi, masu jin gajiyar shirin na da fahimta iri guda game da manufa da maƙasudan shirin. Tsarin-Aikin da tsarin M&E duk ya kamata su kasance masu sauƙi sannan waɗanda ake bita a-ka-a-kai. Ta hanyar bibiyar waɗannan takardu a duk tsawon wa'adin aiwatar da shirin, za ku tabbatar da cewa sun dace da manufofi da muhalli. 

Shiryayyen Tsarin Aiki (Tsarin Aiki) na bayani game da:

  • Ayyukan shirin​
  • Manufofin shirin na gajeren zango da na dogon zango​
  • Yadda za a auna cigaba da aka samu wajen cimma manufofi​
  • Haɗurra da hasashe da ka iya kawo muku tangarɗa wajen cimma manufofinku 
Title
doc
ƘIRƘIRAR TSARIN-AIKI

Yadda ake amfani da Tsarin-Aiki 

logframe1

LogFrame

Ku karanta shafin taƙaitawar shiri (bayani) na Tsarin-Aiki daga ƙasa zuwa sam:

  • Tsararrun taƙaitawa waɗanda shirya daga ƙasa zuwa sama
  • Kowanne matakin Tsarin-Aiki na haifar da na sama da shi
  • Bayanan "idan" da "to"

Ayyuka su ne abubuwan da aka gudanar ko tarurruka waɗanda shirin ke aiwatarwa domin cimma manufarsa.

  • Misali: samar da horaswar rayuwa ga matasan da ke cikin haɗari

Sakamako sun kasance kayayyaki ko ayyukan zahiri waɗanda shirinku ke samarwa. Sau da dama sakamako na da sauƙin ƙirgawa.

  • Misali: adadin matasan da ke cikin haɗari da aka ba wa horaswa

Sakamako su ne tasiri masu kyau da aka samu daga shirinku. Waɗannan na iya kasancewa waɗanda ake cimmawa cikin tsawon lokaci, kamar su tsari na gaba ɗaya - ko waɗanda suka kasance na matakin al'umma, ko waɗanda ake cimmawa cikin gajeren lokaci, kamar tasirin nan take na shirin a kan dabarun koyo ko sauyin hali.

  • Misali: pahalarta sun nuna cigaba a ɓangaren halaye da ɗabi'u nagartattu

Manufa babbar sauyi mai kyau ne da kuke muradin shirinku ya samar a duniya.

  • Misali: rage faruwar VE