Aunawa

Aunawa na nufin auna shiri domin gano tasirinsa da ingancinsa. Akwai manyan rabe-raben aunawa guda biyu: na aiwatarwa da na taƙaitawa. Aunawar aiwatarwa shi ne nau'in aunawa da ake gudanarwa a lokacin aiwatar da shirinku waɗanda ka iya haifar da sauye-sauye a lokacin gudanar da shi. Aunawar taƙaitawa na aukuwa ne bayan an kammala shiri sannan aikinsa shi ne auna nasarar shirin.

Kafin fara aunawa, ku ayyana nau'in sauyi guda da shirinku ke son samarwa. Auna tasirin shirinku na iya komawa kan sauye-sauyen da su ma sun kasance ana sanya ido a kansu a duk tsawon lokacin gduanar da shirin, kamar sauyi a ɓangaren halayya, ɗabi'u da dangantaka.

Domin tsara aunawar shirinku na P/CVE, Cibiyar Haɗin Kan Yaƙar Ta'addanci (CGCC) ta ba da shawarar bin waɗansu matakai:

1
Details
Zayyana dalili
2
Details
Zattaba farfajiya
3
Details
Ayyana mai aunawa
4
Details
Zaɓen ƙunshiya
5
Details
Samar da manunan da za a iya aunawa

A gaba an yi bayanin waɗannan matakai a ƙarƙashin shirin P/CVE a cikin wannan kudin bayanai.

Hidayah ta yi bayanin nau'ukan aunawa da za a iya amfani da su a cikin shirin P/CVE, kamar yadda aka nuna a jadawalin da ke ƙasa.

Hanyoyin aunawa ba dole ne su mayar da hakali a kan ko dai an cimma manufa ko ba a cimma ba kawai, a bayan haka ma sukan lura da abubuwa da dama. Hanyoyin aunawa daban-daban ba su kasance keɓance da juna ba sannan ana iya samun sakamako iri guda (abin da aka samar/sakamako/abin da aka sanya) daga hanyoyi daban-daban.

AUNAWAR TANTANCEWA domin tantancewa ko shirye-shirye sun dace da sakamakon shirin CVE da tasirinsa. A irin wannan nau'in aunawa, manufar ita ce a gwada sannan a auna tsari da ƙoƙarin shirin a karan kansa. Waɗansu muhimman manunai na iya kasancewa:
  • Samuwar Ra'in Sauyi domin shirin
  • Ayyukan da ke taimaka wa sakamako da abubuwan da aka samar
  • Sakamako da abubuwan da aka samar da suka dace da manufa ko maƙasudi
  • Isassun kayan aiki domin gudanar da shiri ko ayyuka
  • Adadin kwasa-kwasai da aka koyar, adadin awanni da aka ɓata, ko adadin masu koyo da aka koyar
AUNA INGANCIN SHIRI donmin yadda ayyukan suka cika manufofinsu. A wannan yanayin, ma'auni da kimantawa shine aikin shirin ko aikin. Wasu maɓalli masu mahimmanci na iya zama:
  • Kammala shiri
  • Waɗanda aka kai gare su da farfajiyar da aka karaɗe sun yi daidai da abin da ake buri
  • An yi amfani da kasafin kuɗi yadda ya kamata
  • An bi da kayan aiki (lokaci da ma'aikata) yadda ya kamata
AUNA AMFANIN SHIRI domin a auna a gani ko sakamakon shiri sun samar da amfanin da ake so. Waɗansu muhimman manunai na iya kasancewa:
  • Ƙarin daraja ga mahalarta da/ko mutanen da abin ya shafa
  • Ƙarin daraja ga tsarin shugabanci da/ko mutanen da abin ya shafa
AUNA SAKAMAKO domin aunawa a gani idan shirye-shirye sun taimaka wa sakamakon shirin, tare da auna tasirin shirin a kan masu amfana da shi. Waɗansu muhimman manunai na iya kasancewa:
  • Sauyi a hali ko ra'ayoyi da/ko mutanen da abin ya shafa
  • Sauyi ga ɗabi'ar masu cin gajiyar shirin da/ko waɗanda abin ya shafa
AUNA TASIRIN SHIRI domin aunawa a gano idan amfanin shiri ya taimaka wajen cimma manufa. Waɗansu muhimman manunai na iya kasancewa:
  • Raguwar adadin rikici da ake samu a Wurin X a Lokacin Y
  • Raguwar kason mutanen da ke goyon bayan tsattsauran ra'ayin rikici a Wurin X a Lokacin Y