Damawa da Matasa Yayin Aiwatar da Shiri

Sau da dama matasa ne ke kasancewa rukunin mutanen da shirye-shiryen P/CVE ke mayar da hankali kansu. Tun da haka ne kuwa, to damawa da matasa wajen aiwatar da ayyukan na da matuƙar amfani.

Kafin ku yi tunani kan jawo matasa cikin sha'anin aiwatar da shirinku, to ku duba Sashen Haɗi Game da Janyo Aiki da Matasa. Wannan ɓangare zai taimaka muku wajen samar da ma'anar "matasa" domin shirinku, tare da gabatar da matakin Cigaba Mai Kyau na Matasa (PYD) domin samun damar damawa da matasa, sannan a zayyano dalilin da ya sa damawa da matasa da kuma PYD na da amfani musamman ga shirye-shiryen P/CVE.

Title
Ta yaya ya kamata ku yi aiki tare da matasa a yayin aiwatar da shiri?

A matakin Tsarawa, kun zayyana rukunin al'ummar da za ku mayar da hankali kansu sannan kun ƙayyade rukunonin matasa da za ku yi ayyuka da su, idan akwai. A matakin aiwatarwa, ku yi la'akari da tambayoyin da ke ƙasa domin tabbatar da cewa kuna aiki da matasa yadda ya kamata, sannan ku tabbatar da cewa ba ku haifar da wata matsala da gangan ba: 

WAƊANNE MATAKAI NE DABAN-DABAN NA AIKI TARE DA MATASA YAYIN AIWATAR DA SHIRI?

Bincike da ilimin aiwatar da shiri sun nuna cewa muhimmancin aiki tare da matasa bai taƙaita ga zamar da su waɗanda za su ci gajiyar shirinku ba kawai, ya haɗa har da aiki da su a matakin aiwatar da shirin kansa. Yayin da kuke tunanin ta wace hanya ya fi dacewa ku ƙulla haɗin kai da matasa, ku yi la'akari da waɗannan matakai da ke ƙasa: 

  • Tuntuɓar matasa game da maƙasudai, ƙunshiya, da tsarin ayyuka a yayin aiwatarwa, ko aunawa da zai bunƙasa tsari da aiwatarku (auna haɗari ko tsaro, auna GESI, da sauransu)
  • A fi mayar da hankali kan fasahar matasa ta hanyar janyo su cikin tawagar da ke aiwatar da ayyuka - a matsayin ma'aikata masu cikakken matsayi, mataimaka na taƙaitaccen lokaci, ko masu aikin sa-kai.
  • Ku haɗa kai da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin jagorancin matasa, ku bincika sannan ku zaɓi matasan da za su halarta, domin saka hannu wajen gudanar da ayyuka da tarurruka, ko su jagoranci wani al'amari na shirin.

Yayin da kuke nazarin yadda za ku yi aiki tare da matasa a matakin aiwatar da shirin, ku duba wannan bayanin jagoranci game da matakai mabambanta na aiki tare da matasa.

MUHIMMIN DARASI

Domin shirin ya kasance ya samu halartar matasa, sannan domin a tabbatar da ba a harfar da wata matsala ba, dole ne shirinku ya tabbatar da cewa an gudanar da al'amarin halartar matasa yadda ya kamata.

Tattaunawa tare da matasa da kuma ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin jagorancin matasa ya nuna cewa: "Dole ne halartar da za a yi ta haifar da ingancin shirin tare da yin tasiri ga sakamakon, koma-bayan a ce ya kasance na je-ka-na-yi-ka. [...] Za a iya mora tare da samun ɗorewar ƙarfin guiwa da aiki tuƙuru na matasa game da da shirye-shiryen ci gaba da na PVE ne kawai idan akwai tabbacin cewa halartar tasu za ta samar da tasiri. Wannan al'amari ya kasance mai tasiri wajen nasarar shirye-shiryen rage rikice-rikice baki ɗaya. [...] Rashin aminci tsakanin matasa da sauran mahukunta na matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubale da ke tauye halartar matasa cikin shirye-shiryen magance tsattsauran ra'ayin rikici. Dole ne ɗaiɗaikun mutane da al'ummomi su aminta cewa an ɗauki halartar da suke yi da muhimmanci sannan zai haifar da tasiri sosai.” 

Tushe

WAƊANNE MATASA NE SHIRINKU ZAI ƘUNSA?

Bayan kun ƙayyade rukunonin al'ummar da shirin zai shafa a matakin Tsarawa, za ku iya mayar da hankali kan ire-iren matasan da kuke son gudanar da shirinku tare da su. Ku yi la'akari da abubuwa masu zuwa a yayin da kuke tsara matakan zaɓen naku:

  • Ta yaya za ku zaɓi mizanin shekarun matasan da za ku yi aiki tare da su? Idan za ku yi aiki ne tare da mizanin shekaru mai tazara sosai (a misali, shekaru 14-30), to ku yi tunani game da yadda hulɗayyarku za ta taƙaita ga matasan da ke tsakankanun waɗannan shekaru. Bai dace ba ku yi nau'in hulɗayya da 'yan shekara 14 irin wacce za ku yi da 'yan shekara 30. Domin samun ƙarin bayani game da matakan cigaban matasa da kuma tsara shiri domin kowane mataki, to ku duba Sashen Haɗi Game da Aiki da Matasa.
  • Shin za ku yi aiki tare da matasa daga jinsi mabambanta? Ta yaya za ku iya inganta daidaiton jinsi tare da la'akari da sauye-sauyen jinsi yayin aiwatar da shirinku?
  • Shin za ku yi aiki tare da matasan da ke da nakasa? Idan haka ne, me kuke buƙatar aiwatarwa domin tabbatar da cewa an yi aiki tare da su sannan sun halarci shirin yadda ya kamata?

TA YAYA ZA KU SAMAR DA TSARIN KAIWA GA MATASA TARE DA ZAƁEN SU?

Yayin da kuke shiri tare da zaɓen matasa domin gudanar da aikinku, ku tabbatar da cewa kun fahimci ƙalubalen da ke tattare da zaɓen waɗansu matasa tare da rashin zaɓar waɗansu. Ku yi la'akari da abubuwan da aka zayyano a ƙasa cikin nitsuwa yayin da kuke Tsara Matakan Tuntuɓa da Zaɓe da Tsarinku na Magance Haɗari:

MATSALOLIN DA IYA SHAFAR MATASAN DA BA A ZAƁA BA

Tsarinku na iya ware matasan da ba a zaɓa ba

MATSALOLIN DA KA IYA TASOWA

A duka-duka, yayin ɗaukar matasa domin gudanar da wani aiki, za ku bayyana alfanun abin tare da yin bakin ƙoƙari domin samun matasan da ke da ra'ayin halarta. Sai dai kuma sau da dama, ba dukkannin matasa da ke da ra'ayi ba ne ake iya zaɓa. A ire-iren waɗannan lokuta, matasan da ba a zaɓa ba na iya shiga cikin ƙunci da rashin jin daɗin yayin da ya kasance ba za su iya amfana da dama ko aikin da shirin ke aiwatarwa ba. Wannan na iya kasancewa matsala musamman yayin da matasan da ba a zaɓa ba suka ji cewar tsarin babu adalci a cikin tsarin zaɓen ko suka ji cewar an yi son kai.

ABUBUWAN DA KA IYA BIYO BAYA

  • Ku tabbatar da cewa an yi adalci a yayin zaɓen sannan ya kasance kun sanar a bayyane kuma dalla-dalla game da ƙa'idoji, matakai, da sakamakon zaɓen.
  • Ku yi shiri na aiki a wani shirin da za ku gudanar a nan gaba tare da matasan da ba a zaɓa ba a yanzu, sannan ku tabbatar da cewa kun sanar da waɗannan matasa game da damarmakin. Bayan haka, ku yi ƙoƙarin sanya matasan da ba a zaɓa ba a cikin waɗansu damarmaki ko shirye-shirye da waɗansu ƙungiyoyin da kuke da haɗin guiwa da su ke aiwatarwa.
  • Ku sanar da yadda shirin zai amfanar da matasa ko da kuwa ba a zaɓe su ba domin su taka wata rawa a cikinsa. A misali, shin shirin zai iya samar da wani bayani ko ya ƙirƙiri waɗansu gurabu da za a iya matasa a cikin al'ummar za su iya amfana da su?
Tsarin ku na iya ƙara mayar da matasan da ba a kusance su ko zaɓa ba

MATSALOLIN DA KA IYA TASOWA

Idan matakan zaɓenku ya mayar da hankali kan wani rukunin matasa taƙamaimai (ta la'akari da jinsi, wuri, matakin karatu, ƙabila ko addini, da sauransu) a matsayin rukunin al'ummar da shirin zai shafa, to shirin naku zai ware sauran rukunoni da ba su dace da wannan matakai ba. Sau da dama, ba a iya tsallake wannan al'amari sakamakon manufar shirin ko kuma ƙarancin kayan aiki, sai dai zai kuma ana iya raba gurabun halartar tsakanin mutanen da suka kasance sun fi fuskantar raunin faɗawa VE da kuma waɗanda ba su da wannan raunin. Koma yaya abin ya kasance, to ya kamata ƙungiyarku ta fahimci haɗurran da ke ƙunshe da lamarin sannan ta samar da matakan kauce wa aukuwar matsala yayin da waɗansu matasa suka ji cewa an ware su, sannan ku tabbatar da cewa matakan da kuka bi na zaɓe bai goyi bayan wanzuwar rarrabuwar kai da wariya a cikin al'umma ba.

ABUBUWAN DA KA IYA BIYO BAYA

  • Ku yi amfani da matakar da kayan aikin da suka shafi magance rikici domin zayyana sauye-sauyen rikici da nau'ukan wariya da ake samu a cikin al'ummarku sannan ku tabbatar da kun baza hannu sannan matakan zaɓen da kuka yi amfani da su suna rage samuwar matsala.
  • Ku yi tunani game da hanyoyin da zai iya ba da dama ga matasan da aka zaɓa su yi aiki tare da waɗanda ba a zaɓa ba ta hanyar bin matakin ilimantar da abokai. A misali, matasan da aka zaɓa na iya kaiwa ga waɗansu matasan na daban ta hanyar bayyana sakamakon aikin ga sauran matasa.
  • Ku yi tunani game da ko akwai alfanu dangane da yin aiki tare da rukunonin matasa mabambanta yayin aiwatar da wani abu da ya shafi shirinku. Misali, shin yin aiki tare da matasa daga ɓangarori daban-daban ko rukunonin ƙabilu daban-daban zai taimaka wajen samar da haɗin kan da zai taimaka wa shirin da kuma al'ummar?

MATSALOLIN DA IYA SHAFAR MATASAN DA AKA ZAƁA

Tsarinku na iya ware kunyatar matasan da aka zaɓa

MATSALOLIN DA KA IYA TASOWA

Za a iya tsara shirinku ta yadda zai mayar da hankali kan waɗansu al'ummu taƙamaimai na matasa, musamman al'ummu, rukunonin mutane, ko ɗaiɗaikun mutane da kuka gano cewar suna da raunin faɗawa cikin VE. Idan ya kasance shirinku na aiki ne tare da matasa na musamman, za ku iya yin kasadar haɗa waɗannan ɗaiɗaikun mutane ko rukunoni da ke da VE, wanda hakan zai samar da sakamako marar kyau tare da ƙara sanya su fuskantar wariya. Shi ma kansa aiki da matasan da "ke cikin haɗari" na iya kasancewa kunyatarwa, musamman da yake al'ummarsu, waɗansu al'ummu daban, da/ko matakan tsaro na iya yi wa waɗannan matasa da "ke cikin haɗari" kallon zargi, wanda zai sai su kasance abin hari game da fafutukar daƙile taaddanci. Bayan haka, bayyana matasa a matsayin waɗanda "ke cikin haɗari" na iya yin tasiri ga matasan da ke kallon kansu a matsayin masu rauni da rashin madafa, a maimakon waɗanda aka ƙarfafa.

ABUBUWAN DA KA IYA BIYO BAYA

  • Yi nazari sosai game da yadda ya dace ku riƙa yin magana da matasa. Shin za ku iya kauce wa amfani da inkia kamar su "waɗanda ke cikin haɗari" ko "masu rauni”?
  • Idan bai riga ya kasance a cikin tsarin shirinku ba, to ku yi tunanin sanyawa a matsayin matakin ƙarfafawa a shirinku (a duba "Sashen Haɗi Game da Aiki da Matasa" domin samun ƙarin bayani game da bin matakan la'akari da kadara).
  • Ku yi tunani game da hanyar da za ta ƙarfafa aminci da haɗin kai tsakanin matasa.
Matakanku na iya jefa matasa cikin haɗurra da suka haɗa da na har da sha'anin tsaronsu

MATSALOLIN DA KA IYA TASOWA

Matasan da ke halartar shirye-shiryen P/CVE na iya faɗawa cikin haɗarin da ya shafi tsaro:

  • Yayin da matasa ke halartar shirye-shiryen P/CVE, hakan zai jawo hankalin ƙungiyoyin ta ke ta da rikici da masu tsattsauran ra'ayi da ke kallon cewa shirin ƙalubale ne a gare su.
  • Kamar yadda aka bayyana, yayin da shirin P/CVE ya mayar da hankali kan waɗansu mutane ko rukunonin mutane da aka bayyana a matsayin "waɗanda ke cikin haɗari," waɗannan rukunonin al'umma na iya kasancewa gwamnati da matakan tsaro sun sanya musu ido yayin yaƙi da ta'addanci. Haɗurra na iya ƙasanta a ƙasashen da gwamnati ta taɓa yin amfani da P/CVE ko CT a matsayin hanyar shawo kan al'amura da suka shafi hamayyar siyasa, haƙƙoƙin mutane da kuma 'yancin 'yan Adam.

ABUBUWAN DA KA IYA BIYO BAYA

  • Bayan haka, ku yi nazari sosai game da yadda ya dace ku riƙa tattaunawa da matasa da kuma yadda za ku tsara shirinku. Shin za ku iya kauce wa amfani da inkia kamar su "waɗanda ke cikin haɗari" ko "masu rauni"? Shin idan aka riƙa kiran shirin da suna "P/CVE" hakan na iya jefa mahalarta shirin cikin haɗari? Idan haka ne, to ku sauya tsarin shirinku.
  • Ku sanya bayanan haɗurra da za a iya fuskanta da kuma bayanai kan matakan ba da tsaro da kariya ga lafiyar matasa mahalarta a tsare-tsarenku na Rage Haɗari da Samar da Tsaro. Shin akwai buƙatar ku ɗauki matakai na musamman domin tabbatar da cewa an sirranta bayanan matasa da ke halartar shirin? Ku tattauna da matasan da ke halartar shirn game da haɗurra da ƙa'idojin da matakan da suka shafi tsaro.

 

Wannan teburin da ke sama ya samo tushe daga rahotani da dama, har ma da na “Gwarzaye: Matasan da ke kan gaban wajen daƙile tashin hankali” da kuma na “Matasa da Yaƙi da Ta'addanci,” har ma da na kwarewar FHI 360 wajen cuɗanya da ƙungiyoyin da ke aiwatar da aikin kan Yaƙi da Tsattsauran Ra'ayi P/CVE.

DABARAR AIWATARWA

TA YAYA ZA KU IYA SHIRYA ƘUNGIYARKU DOMIN GUDANAR DA SHIRYE-SHIRYEN P/CVE TARE DA MATASA?

An tsakuro daga: Matasa da Ta'addanci: Kundin Bayanai Domin Matasa Masu Aiki da Matasa a Fagen Yaƙar Tsattsauran Ra'ayin Rikici

1

KU SAMAR DA MUHALLIN DA YA DACE SANNAN MAI AMINCI DOMIN AIKI TARE DA MATASA.

Yana da muhimmanci ƙungiyoyi su mallaki kayan aikin da suka dace da kuma muhallin haɗuwa da matasa - wannan na iya kasance a gaba-da-gaba ko kuma ta kan intanet, sannan ayyukan matasan na iya kasancewa a waɗansu wurare na musamman ko kuma a kan titi, ta hanyar "tsararren" shirin da za a gudanar a kan titi. Saɓanin aikin matasa da ya keɓanta a wuri guda, tsararren aikin matasa na gudana ne a wuraren da matasa ke taruwa - a misali, a wurin shaƙatawa, dandali, ke a keɓantattun wurare na musamman. Muhimmancin wannan salo, da ya shafi hulɗayya da matasa ta sigar da ta dace da ƙa'idojinsu, shi ne zai samar da damarmakin hulɗayya da matasa da ba su saba cin gajiyar ayyukan matasa ba. Duk da haka, tsararren aikin matasa a wani wuri na buƙatar samun cikakken bayani game da ƙa'idoji da matakan da ake da su domin tabbatar da cewa ayyukan da za a gudanar tare da matasa sun tafi yadda ya kamata sannan cikin aminci.

2

A SAMAR DA TSARIN TAIMAKO DOMIN MA'AIKATAN DA KE AIKI KAI TSAYE DA MATASAN DA KE AIKI GAME DA BATUTUWA MASU TSAURI KAMAR TSATTSAURAN RA'AYI.

Tomakon ma'aikata da masu aikin sa-kai, musamman waɗanda suke cuɗanya kai tsaye da matasa, na da matuƙar amfani domin tabbatar da cewa ayyukan da ake samarwa suna tafiya bai-ɗaya. Wannan taimako na iya kasancewa dubawa na gaba-da-gaba ko kuma tawagar matasa na iya haɗuewa wuri guda domin tattauna matsaloli da ƙalubale da ake da fuskanta sannan su bayyana bubuwan da suka koya. Tsara irin wannan lokacin dubawa na da amfani ga matasa masu aiki, ƙungiyoyi, da kuma matasan da ƙungiyoyin ke gudanar da ayyuka tare da su. Hakan zai iya samar da wani nau'in 'yanayi mai kyau' - wata dama ta yin nazari tare da guje wa bin tafarki guda kawai na tsarawa, shiryawa, gudanarwa, da aiwatar da shirye-shirye da ayyuka. Bayan haka, dubawa na iya taimakon ma'aikata domin bunƙasa fikirarsu ta zurfafa tunani, a yayin da suke yin nazari game da tattaunawa tsakanin matasa da kuma auna shirye-shirye. Lura da yadda tsattsauran ra'ayi ya kasance lamari mai sarƙaƙiya da muhimmanci (musamman tsattsauran ra'ayin rikici), yana da matuƙar amfani matasa su samu taimakon da suke buƙata domin ci gaba da halartar wannan aikin.

3

A TSARA ƘA'IDOJI DA MATAKAN DA ZA SU TAIMAKA WAJEN MAGANCE MATSALOLIN DA KA IYA TASOWA.

Ƙungiyoyin da suke hulɗayya kai tsaye da matasa na da buƙatar tabbatar da cewa suna da ingantaccen tsari na cikin gida da ƙa'idoji da matakan fuskantar duk waɗansu matsaloli da za su iya tasowa waɗanda suka shafi matasa da tsattsauran ra'ayi. Dole ne duukkannin ma'aikata da 'yan sa-kai da ke da alaƙa da ƙungiyar su kasance suna da masaniya game da waɗannan ƙa'idoji da matakai. Yayin da ya kasance abu ne mai wahala a iya hasashen dukkannin abubuwan da ka iya faruwa, yana da muhimmanci a tabbatar da samuwar matakai ingantattu na ba da rahoto da sadarwa.

4

KU TABBATAR DA CEWA KUNA SANE DA ƘA'IDOJI DA MATAKAN DA KE TASIRI KAN MATASA A CIKIN AL'UMMARKU.

Ya kamata ya kasance ƙungiyoyi na da masaniya game da ƙa'idojin ƙaramar hukumarsu, da na matakin yanki, da kuma na matakin ƙasa, musamman waɗanda ke da alaƙa da ƙa'idojin da ke yin tasiri a kan matasa kai tsaye - waɗanda suka shafi ɓangarorin ilimi, kasuwanci, aiki, lafiya, shari'a, da cigaban rayuwa. Yayin da ya kasance ba kowane matashi da ke aiki ba ne zai iya samun wani nau'i taƙamaimai da ya rataya a kansa, da yawa z asu samu damarmakin zayyano buƙatun matasa tare da bayyana hanyoyin da gwamnatocin ƙananan hukumomi da na ƙasa za su iya bi domin dacewa da muradu da buƙatun matasa.

5

KU RIƘA LA'AKARI DA MUHIMMANCIN INTANET DA MUSANYEN BAYANAI TARE DA KOYO.

Haɗuwa da matasa ma'aikata daga ma'aikatu daban-daban bai taƙaita ga samar da tallafi ba kawai ya haɗa har da musanyen ilimummuka da ra'ayoyi domin gudanarwa. Haɗuwa da ma'aikatan da ke waɗansu ɓangarori da ke da alaƙa da matasa na iya samar da ƙarin cigaba – misali, domin samun damar aiki tare da ma'aikatan kiwon lafiya, malamai da masana, shuwagabbin addinai, ma'aikatan gwamnati, 'yan siyasa, shuwagabannin al'umma, da 'yan sanda. Samar da dangantaka da alaƙa tsakanin waɗannan muhallan ƙwarewa mabambanta na ba ku damar neman taimako ko shawara a lokacin da kuke da buƙatar hakan - sannan domin samun damar aiki tuƙuru domin samar da sakamako mai kyau ga matasa. Sannan waɗannan alaƙa na iya kaiwa ga haɗin guiwa - a misali, a ɓangaren goyon bayan shiri na haɗin guiwa.

6

KU LURA DA MATSAYIN MAMBOBIN TAWAGAR DA KUKA ZAƁA DOMIN AIKI TARE DA MATASA.

Ɗaukar fitattu cikin al'umma tare da haɗa su da mutanen da ke fuskantar wariya domin aiki tare na samar da ruɗani sannan ya kamata a guji yin hakan. Abu ne mai wahala ga waɗanda suka fito daga gidan wadata da su fahimta sannan su cire wayewa da rayuwar wadata da suka saba da ita na tsawon lokaci. Fikirar gayyato waɗanda ba fitattu ba da kuma ilimin tasirin da rukunin mutane da ke fuskantar wariya ke da shi da kuma al'adu da suka shafi jinsi, na da muhimmanci ga ma'aikata da kuma shirye-shiryen da suka shafi yin aiki tare da matasa.

TA YAYA ZA KU SHIGAR DA CIGABA MAI KYAU NA MATASA A CIKIN TSARIN AIWATAR DA P/CVE?

A wannan gaɓa, kun riga da kun fara aiki tare da matasa, sannan/ko kuma kun sanya ƙa'idojin PYD a matakin Samu da Tsarawa na shirinku. Ko da ba ku riga kun yi ba, ba ku makara ba wajen sanya matasa cikin shaanin aiwatar da shirinku ta hanyar sanya PYD. Gwada wannan motsa jiki a ƙasa:

Title
doc
PYD JAGORAR AYYUKAN MATASA
photo
Details

Takardar Ƙayyade ayyukan Matasa

Wannan Takardar Ƙayyade ayyukan Matasa da aka gabatar a yayin da ake tsara ayyuka, ana iya amfani da shi a yayin aiwatar da ayyuka, ta haka za a iya danganta ayyukan da matasa ke yi/ko ke gudanarwa, kuma za a iya yin bita ko a shigo da sabobin ayyuka domin haɓaka ayyukan Matasa.