Muhimman Kalmomi

Taƙaita Kalmomi/Kalma  Cikakkiyar Kamla 
AAR  Nazarin Bayan Aiki (After-Action Review)  
CAF 2.0 Tsarin Aikin Auna Rikici (Conflict Assessment Framework)
CBO Ƙungiyar Al'umma (Community-Based Organization)
CDA Shirye-Shiyen Koyon Haɗaka na CDA (CDA Collaborative Learning Projects)
CGCC Cibiyar Haɗin Kan Yaƙar Ta'addanci (Center on Global Counterterrorism Cooperation) 
CSOs Ƙungiyoyin Al'umma (Civil Society Organizations)
DFID Sashen Cigaban Ƙasa-daƘasa na Ingila (United Kingdom Department for International Development)
FBO Ƙungiyoyin Addinai (Faith-Based Organization)
FTFs Mayaƙan 'Yan Ta'adda na Ƙasashen Ƙetare (Foreign Terrorist Fighters)
GCCS Cibiyar Duniya game da Tsaron Haɗin Guiwa (Global Center on Cooperative Security ) 
GCERF Asusun Hidimomi da Kaucewar Al'umma daga Bin Tafarkin Tsattsauran Ra'ayi na Duniya (Global Community Engagement and Resilience Fund) 
GCTF Dandalin Yaƙi da Ta'addanci na Duniya (Global Counterterrorism Forum) 
GESI Daidaiton Jinsi da Damawa da Kowa (Gender Equality and Social Inclusion)
GLAM Ƙungiyar Ƙirƙirar Tsarin Gdanarwa ta Ƙasa-da-Ƙasa (Global Learning for Adaptive Management Initiative)
ISO Ƙungiyar Samar da Inganci ta Ƙasa-da-Ƙasa (International Organization for Standardization)
LGBTI Yar Maɗigo, Ɗan Luwaɗi, Mata-Maza, Masauyin Jinsi, Marar Jinsi (Lesbian, Gay, Bisexual, Transgender, Intersex)
Tsarin-Aiki Shiryayyen Tsarin Aiki
M&E Sa Ido Sannan a Aunawa
NGO Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu (Non-Governmental Organization)
OTI Ofishin Ƙirƙire-Ƙirƙire na USAID (USAID Office of Transition Initiatives)
P/CVE Karewa da Yaƙar Tsattsauran Ra'ayin Rikici (Preventing and Countering Violent Extremism)
PIRS Takardar Kundace Bayanin Ƙoƙari (Performance Indicator Reference Sheet)
PQA Auna Ingancin Shiri (Program Quality Assessment)
RAN Hulɗayyar Wayar da Kai game da Tsattsauran Ra'ayi (Radicalization Awareness Network) 
RESOLVE Binciken Mafita Game da Tsattsauran Ra'ayin Rikici (Researching Solutions to Violent Extremism Network) 
RUSI Royal United Services Institute
SMS Saƙon Kar-Ta-Kwana (Short Message Service)
ToTs Horas da Masu Horaswa (Training of Trainers)
UN Majalisar Ɗinkin Duniya (United Nations)
UNDP Shirin Ci Gaban Majalisar Dinkin Duniya (United Nations Development Program)
USAID Ma'aikatar Raya Ƙasa ta Ƙasar Amurka (United States Agency for International Development)
USIP Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (United States Institute of Peace)

 

 

Taƙaita Kalmomi/Kalma Cikakkiyar Kamla Bayani
Mai fuskantar haɗari  

Cikin haɗari na nufin ɗaiɗaikun mutane, ƙungiyoyi, ko al'ummu da barazanar VE zai iya yin tasiri a kansu sakamakon raunin da suke da shi ko kasancewar sauye-sauyen VE da abubuwan da ke janyo shi na iya yin tasiri a kansu.

(ƙarfafawa daga ɓangarori daban-daban)

C-AM Sa Ido don Fahimtar Ƙalubale (Complexity-Aware Monitoring)

C-AM nau'in sa ido ne domin tabbatar da inganci wanda ke da muhimmanci yayin da sakamako ke da wahalar fahimta biyo bayan sauye-sauye ga abin da ake magana a kai ko dangantakar da ke tsakanin sababi da tasiri. Yayin da aka samu ƙarancin damar iya hasashen musabbabin faruwar abubuwa, bayanan sa ido don fahimtar ƙalubale na samar da nau'ukan sakamako, musabbabi, da abubuwan da suka janyo.

(Tushe: Bayanin Tattaunawa: Sa Ido don Fahimtar Ƙalubale, USAID, 2018)

CLA Haɗin Guiwa, Koyo, Daidaitawa (Collaborating, Learning, and Adapting)

CLA tsarin aikin USAID ne na gudanar da shirye-shirye. CLA ya ƙunshi salon haɗin guiwa da ci gaba da koyo domin naƙaltar dabarun gudanarwa tare da naƙaltar yanaye-yanayen da ke ba da damar bin matakan.

(Tushe: Bayanin Tattaunawa: Tsarin Gudanarwa, USAID, 2018)

 

Haɗin Kan Al'umma (Haɗin Kai a Zamantakewa)  

Al'umma mai haɗin kai a inda mutum "ke aiki domin samar da walwala ga dukkannin al'ummar, tare da yaƙar rabuwar kai da wariya, tare da jin ana tare, da ƙarfafa amincewa, tare da ba wa mambobinta damar samun ci gaba a zamantakewa.”

(Tushe: OECD)

Haɗin kai a zamantakewa ya shafi haƙuri da girmama bambance-bambance (da suka shafi addini, ƙabila, tattalin arziki, ra'ayin siyasa, ra'ayin saduwa, jinsi, da shekaru) - wanda ya haɗa da matakin gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane. Duk da cewa akwai muhawara game da ma'anar haɗin kan zamantakewa, akwai manyan ɓangarorin da ya shafa: (1) Rage samuwar saɓani, bambanci, da nuna wariya. (1) Ƙarfafa hulɗayyar zamantakewa, cuɗanya, da kusantaka.

(Tushe: UNDP)

Ilimin Fahimtar Rikici  

Ilimin fahimtar rikici na nufin bin matakan fahimtar yadda taimako ke cuɗanya da rikici a wani muhalli, tare da manufar rage matsalolin da ba a so, da kuma yin tasiri wajen rage rikici ta hanyar ayyukan al'umma, cigaba, da/ko harƙalloli da suka shafi ƙarfafa zaman lafiya.

(Tushe: CDA)

Masu haɗawa  

Masu haɗawa su ne muhimman ɓangarorin tsarin aikin Guje wa Cutarwa Masu haɗawa sun kasance masu samar da haɗin kai a cikin al'umma. Masu haɗawa na fito da fikirar da mutane ke da shi na samar da zaman lafiya domin gina zamantakewa mai cike da lumana tsakanin mutane mabambanta.

(Tushe: an kwaikwaya daga Bayanan Jagorancin Mahalartar Taron Ƙara wa Juna Sani na Guje wa Cutarwa’, CDA, 2016)

CT Taƙar Ayyukan Ta'addanci (Counterterrorism)

Huɓɓasa domin taƙaitawa, dannewa, da bibiyar al'amarin 'yan ta'adda da ayyukan ta'addanci.

(ƙarfafawa daga ɓangarori daban-daban)

CVE Ƙoƙarin Shawo Kan Tsattsauran Ra'ayi (Countering Violent Extremism)

Shawo Kan Tsattsauran Ra'ayi na nufin yunƙurin tagaza wani abu domin daƙilewa ko wargaza ƙoƙarin masu tsattsauran ra'ayin rikici na cusa ra'ayin, ɗaukar mambobi, da jawo mabiya domin shiga rikici, tare kuma da shawo kan waɗansu al'amura da ke taimaka wa wajen samun sababbin masu tsattsauran ra'ayi da kuma cusa ra'ayin rikici. CVE ya ƙunshi doka da ayyukan da suka shafi inganta zaman lafiya a fannin siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa a ɓangaren ƙananan al'ummu da ƙananan hukumomi da kuma damar da suke da ita ta yin aiki game da su.

(Tushe: An sabunta daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da Dabarun Haɗin Guiwa Kan Yaƙar Ta'addanci na USAID, 2016)

Masu Rabawa  

Masu rabawa su ne muhimman ɓangarorin tsarin aikin Guje wa Cutarwa Masu rabawa su ke janyo watsaniya, rashin amincewa da juna, ko zargi a cikin al'umma wanda a baya ya haifar da ko a gaba zai haifar da rikici a tsakanin rukunonin al'umma. Sukan hana samuwar zamantakewar lumana.

(Madogara: an kwaikwaya daga Bayanan Jagorancin Mahalartar Taron Ƙara wa Juna Sani na Guje wa Cutarwa’, CDA, 2016)

DNH Ba Shi Da Illa (Do No Harm)

DNH ya shafi ilimin fahimtar rikici da ya dace da shirye-shiryen da ake gudanarwa a wuraren da ke fuskantar rikici. Za a iya sanya DNH a mafi yawan matakan aiwatar da shiri. Manufar ba ta taƙaita ga ƙoƙarin tabbatar da cewa shirinku ya ruruta wutar abubuwan da ke jawo rikici ba ko kuma ya jefa ku, ma'aikatanku, da masu cin gajiyar shirinku a cikin haɗari, a maimakon haka, manufar ta haɗa da tabbatar da cewa shirinku na taimakawa wajen hana samuwar tsattsauran ra'ayin rikici. Babbar manufar DNH shi ne ƙwanƙwance masu rabawa da masu haɗawa da ke lalatawa ko ƙarfafa dangantaka tsakanin rukunonin al'umma.

(Madogara: an kwaikwaya daga Bayanan Jagorancin Mahalartar Taron Ƙara wa Juna Sani na Guje wa Cutarwa’, CDA, 2016)

Abubuwan da ke Janyo Tsattsauran Ra'ayin Rikici  

Abubuwan da za su iya janyo ta'azzarar rikici ko fitina da kuma waɗanda ke iya tasiri a kan cusa wa mutane tsattsauran ra'ayi. Sau da dama akan raba abubuwan da ke haddasa faruwar wani abu zuwa rukunin abubuwan da ke janyowa da abubuwan da ke turawa.

(Tushe: Bayanin Halin da Ake Ciki Game da Tsattsauran Ra'ayin Rikici da Fitina, USAID, 2011) 

Daidaiton Jinsi  

Daidaiton jinsi ya ƙunshi aiki tare da maza manya da yara, mata manya da yara domin samar da sauye-sauye ga halaye, ɗabi'u, matsayi, da nauye-nauye da suka rataya kan mutane a gida, a wurin aiki, da kuma a cikin al'umma. Daidaiton jinsi ya wuce batun jerin dokoki a cikin littattafai kawai; ya shafi ba da 'yanci da inganta rayuwa baki ɗaya domin samun daidaito ba tare da tauye maza ko mata ba. 

(Tushe: Daidaiton Jinsi da Dokokin Ƙarfafa Mata, USAID, 2012)

Matakan Aiwatar da Shiri  

Matakan  Aiwatar da Shiri tsarawa ce da fasahar USAID domin yin bayani game da jeranton matakai da ake bi da manufar samun ƙarin shirye-shiryen samar da ci gaba tare da samun tasiri sosai. Ya ƙunshi waɗannan ɓangarori: Ci gaban CDCS, tsarawa da aiwatar da shiri, kula da cigaba, aunawa, koyo da ɗaukar sawu, da kuma kasafi da kayan aiki. Mun ɗauki hannu yayin tsara matakan aikwatar da shirin wannan Bayanan Jagorancin CVE, domin a duba matakan aiwatar da shirin guda biyar: (1) Samu, (2) Tsarawa, (3) Aiwatarwa; (4) Sa Ido da Aunawa; da (5) Koyo.  

Dalilan da ke Janyowa  

Abubuwa masu janyowa suna da tasiri kai tsaye a kan cusa tsattsauran ra'ayi a matakin ɗaiɗaikun mutane sannan sun kasance abubuwan da ke jayo mutane zuwa cikin rukunin VE ko tafiyarsu - kamar ɗaukaka ƙara game da wani shugaba, zaɓan kai a matsayin shugaba ko rani jagora, ko kuma cin moriyar wata ƙungiya ta fuskar kayayyaki ko ra'ayoyi.

(Tushe: Bayanin Halin da Ake Ciki Game da Tsattsauran Ra'ayin Rikici da Fitina, USAID, 2011)  

Dalilan da ke Turawa  

Abubuwa masu haddasawa sun kasance suna tasowa ne daga muhallin da ake zamantakewa waɗanda kume ke shafar mutanen da ke da rauni wajen tura su zuwa cikin sahun masu rikici. Waɗannan matakan rarraba matsayin al'umma sun haɗa da ƙasƙantarwa da rarrabawa; ɓangarorin da ba su da shugabanci na gari ko ɓangarori marasa shugabanci; danniyar gwamnati da tauyi 'yancin ɗan'ada; rashin tuhumar waɗansu game da cin hanci da rashin hukunta masu hannu da shuni; da ra'ayoyin al'ada masu illa.

(Tushe: Bayanin Halin da Ake Ciki Game da Tsattsauran Ra'ayin Rikici da Fitina, USAID, 2011)

PVE MaganceTsattsauran Ra'ayin Rikici (Preventing Violent Extremism)

Ya dace matakan magance tsattsauran ra'ayin rikici su mayar da hankali ba wai a kan matsalolin tsaro ba kawai, har ma da duba musabbabin hakan da kuma hanyoyin shawo kan al'amarin. Saboda haka, hanya mai ɗorewa ta magance matsalar tsattsauran ra'ayin rikici na buƙatar bin matakan damawa da al'umma tare da haƙuri, da ƙarfafawa da ya shafi siyasa da tattalin arziki, da kuma rage rashin daidaito.

(Tushe: Magance Tsattsauran Ra'ayin Rikici ta Hanayar Ƙarfafa Jawo Mutane a Jiki, Fahimtar Juna, da Girmama Ra'ayin Kowa, UNDP, 2016)

PYD Cigaba Mai Kyau na Matasa (Positive Youth Development)

PPYD mataki ne na bunƙasa matasa ta hanyar mayar da hankali kan ƙaruwar arzikin matasa da ƙarfafa abubuwan da ke ba su kariya. PYD na janyo matasa da iyalansu a jiki, da al'umma da gwamnatoci domin ƙarfafa musu guiwa wajen yin amfani da fasahohinsu. Matakin PYD na inganta ƙarewa, arziki, da ƙarfin guiwa; yana samar da hulɗayya mai kyau; yana ƙarfafa muhalli; sannan yana samar da sauyi ga tsare-tsare da ake da su.

(Tushe: An ɗauki hannu daga Hukumar Cigaba Mai Kyau na Matasa, YouthPower)

Cusa Tsattsauran Ra'ayi  

Cusa Tsattsauran Ra'ayi hanya ce da mutum ko ƙungiya ke rikon tsauraran ra'ayoyi ko fahimta sannan su ɗauki rikici a matsayin hanyar samar musu da cigaba. Yayin da ya kasance mafi yawan mutanen da suka riƙe tsattsauran ra'ayi ba za su taɓa janyo rikici ba, waɗanda suke yi sukan yi riƙo da ra'ayoyin da ke nuna cewa suna kan daidai.

(Tushe: Bibiyar Cusa Tsattsauran Ra'ayi: Jihad 4.0 da Shirin CVE, USAID, 2016)

Janyowa   

Janyowa hanya ce da mutanen da suke da haɗaka da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin rikici ke janyo waɗansu mutane zuwa cikinsu. Ana janyo mutane ne cikin salo da tsari tare da bin mataki-mataki; a ɓangare guda, ɗaiɗaikun mutane ("masu janyowa") su ke da alhakin gudanar da hakan cikin tsarin daga sama zuwa ƙasa, waɗanda su aka hannunta wa wannan aikin, waɗanda kuma suke aiki a ƙarƙashin rukuni na musamman da ke da wannan alhaki. [...] "Shigar da kai," a ɗaya ɓangaren, yanayi ne da ake samu inda mutane ke saka kansu cikin [VEOs], kai tsaye ko a kaikaice; sukan yi haka ta hanyar, mafi tsanani, aikata abubuwa kaɗan ko kuma abin da waɗansu suka gudanar bisa tsari.

(Tushe: Bayanin Halin da Ake Ciki Game da Tsattsauran Ra'ayin Rikici da Fitina, USAID, 2011)

Juriya   

Akan samu juriya a matakai daban-daban sannan cikin sigogi mabambanta. Saboda haka, ma'anar juriya zai danganta ne da kan abubuwan da suka haɗa da nau'in shiri da kuka mayar da hankali a kansa (ɗaiɗaikun mutane, rukuni, ko al'umma) sannan wane mataki kuke son kaiwa game da juriya (annoba, al'amarin abinci, fitina/rikici, tsattsauran ra'ayin rikici, cuta, da sauransu). A duka-duka, USAID ta ba da ma'anar juriya a matsayin “damar da mutane, iyalai, al'ummu, ƙasashe, da gwamnatoci suke da shi na ragewa, sabawa da, da farfaɗowa daga matsalolin da suka auku da suka shafi janyo raunin bin wani ra'ayi tare da samar da cigaba.”

Magance Haɗari  

Matakan kula da haɗurra tsari ne na lura da abubuwan da ka iya faruwa domin rage matsalar da za a iya samu ko asara tare da ƙara bin matakan samun damarmaki da nasarori. Manufar bin matakan kula da haɗurra shi ne "domin samar da hanya mafi dacewa ta gudanar da aiki bisa tabbacin cin nasara ta hanyar samu, fahimta, yanke hukunci, da ba da rahoto game da haɗurra. Matakan kula da haɗari ya kasance hanyar da ke ba da dama: komabayan samun matsala game da hukuncin da aka yanke wanda ka iya haifar da dakatarwar shiri. Ingantaccen matakin kula da haɗari na samar da yanayin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da shirin, sannan da nasarar shirin.

(Tushe: Shirye-Shiryen Kauce wa Haɗari da ya Shafi Magance Matsalar Tsattsauran Ra'ayi: Bayanan Jagoranci ga Masu Aiwatarwa, UNDP, 2018)

Damawa da Kowa  

Damawa da kowa na nufin inganta matsayin ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi domin su sanya hannu a cikin al'amuran al'umma da kuma matakin inganta ƙarfi, dama, da mutuncin waɗanda suke baya a ɓangaren tushensu domin ba su damar a shiga a dama da su a cikin al'umm.

(Tushe: Bankin Duniya)

Mai ruwa da tsaki  

Mahukunci na nufin dun wani mutum ko rukunin mutane ko ƙungiya waɗanda kai tsaye ko a kaikaice suka yi tasiri a kan ayyuka ko shiri da za a aiwatar. Sannan masu ruwa da tsaki na iya kasancewa sun yi tasiri a kan sakamakon aiki/shirin ta hanyar da ake so ko wadda ba a so. Misalan masu ruwa da tsaki sun haɗa da: al'ummu ko ɗaiɗaikun mutane; gwamnatocin ƙasa da na ƙananan hukumomi; jiga-jigai a cikin fararen hula; ƙungiyoyi masu zaman kansu a matakin ƙaramar hukuma, yanki, ƙasa, ko ƙasa da ƙasa; da mutane 'yan ƙasa, shuwagabannin addinai, malamai, hukumomi masu zaman kansu, hukumomin UN, 'yan ƙasashen waje da ke ba da tallafi, da rukunonin al'umma da ke da ra'ayi na musamman.

(ƙarfafawa daga ɓangarori daban-daban)

Damar Ci Gaba da Ɗorewa  

A bagiren aikin ci gaba, ana samun ɗorewa ne a matakai uku: (1) ɗorewar sakamako da tasirin ayyuka; (2) ɗorewar ayykan shiri ta hanyar ci gaba bayan an dakatar da kuɗin tallafi, maimaita shirin da aka aiwatar a waɗansu wurare na daban, da/ko gudanar da bibiya; da (3) ɗorewar masu aiwatarwa - wanda hakan na nufin, damar da ƙungiya take da shi a karan kanta na ci gaba da gudanarwa da aiwatar da sauran ayyuka a nan gaba.

(Tushe: An ɗauki hannu daga Shirin Sauya Tsare-Tsaren Ɗorewa Zuwa Shirye-Shiryen da za a Ɗauki Nauyi, Shawarwari ga NGO, Shirin Capable Partners, USAID da FHI 360, 2011)

ToC Ra'in Sauyi (Theory of Change)

ToC bayani ne na hanya da dalilin da ya sa wani shiri zai harfar da wani sauyi na musamman. Yana bin tsarin bai ɗaya na "idan/to": misali, idan shirin ya gudana cikin nasara, to za a samu sakamako da ake buƙata.    

Tushe: Ɗakin Koyo na USAID

VE Tsattsauran Ra'ayin Rikici (Violent Extremism)

Tsattsauran ra'ayin rikici na nufin yin kira, shiga cikin, shiryawa, ko kuma tallafa wa rikicin da aka yi amfani da ra'ayoyi wajen ba ƙarfin guiwar aiwatar da su tare da nuna dacewarsu a bisa manufofi da suka shafi zamantakewa, tattalin arziki, siyasa, ko addini.

(Tushe: An sabunta daga Bayanin Halin da Ake Ciki Game da Tsattsauran Ra'ayin Rikici da Fitina, USAID, 2011)

Sauye-Sauyen VE  

Fahimtar sauye-sauyen VE na buƙtar ƙwanƙance alaƙar da ke tsakanin rashin fahimtar juna da ake samu a matakin al'umma, muhimman masu yin tasiri, abubuwan da ke shiryawa, abubuwan waje da ke tasiri, mizanin rikici, da kuma abubuwan da ke tayarwa domin fahimtar yadda VEO ke mamaye muhallan da suke tare da gauraya da sauye-sauyen rikici a matakin al'umma. Gano raunin faɗawa cikin VEO na taimakawa wajen ware haɗurra tare da fahimtar nau'in yanaye-yanaye, hukumomi, [ƙara waƙafi] ko masu shiga tsakani ke iya yin tasiri a kan sauye-sauyen VE.

(Tushe: An sabunta daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da Dabarun Haɗin Guiwa Kan Yaƙar Ta'addanci na USAID, 2016)

VEO Ƙungiyar Masu Tsattsauran Ra'ayin Rikici (Violent Extremist Organization)

Rukunin mutane ko ƙungiya da ke ƙoƙarin yaɗa ajandar tsattsauran ra'ayin rikici.

(ƙarfafawa daga ɓangarori daban-daban)